Sashe 51
Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
****************
Ammar har baya so ya tunkari komawa gida, musamman idan ya tuna Mufeeda bata gidan. Yanzu ma ba yadda zeyi ne, haka nan ya tunkari gidan yana komawa ya shiga da Napep ɗinsa harabar gidan yayi parking, Amma se yaji kaman ƙamshin turaren wuta, da sauri ya ƙarasa cikin falon ya tararar da komai tsaf se tashin ƙamshi falon yake, Ajiyar zuciya yayi ya lumshe ido yace
"ta dawo kenan" ya nufi ɗakin Mufeeda da Sauri, yana zuwa ya tura ƙofar ɗakin Amma yaga bata nan.
"Mufeeda" ya kira sunan ta da ɗan ƙarfi.
Gyaran murya tayi masa alamar tana banÉ—aki.
Guri ya samu ya zauna a gefen gadon ta yana jiran fitowar ta.
A ƙalla ya kai mintuna goma sha biyar a zaune sannan Mufeeda ta buɗe ƙofar toilet ɗin ta fito.
Ba tasan yana ɗakin ba dan haka daga ita se towel ta fito, tana fitowa suka haɗa ido, ɗauke idon ta tayi tai gaba abun ta, shikam Ammar binta yayi da ido, tun daga sama bayan ta ƙugunta zuwa ƙafafunta, se sheƙi fatar ta take kamar wata tarwaɗa, kasa Magana Ammar yayi, Mufeeda ta tafi gaba wardrobe ɗinta ta ɗakko zumbulelen Hijjabi ta zura ta nemi guri tayi zaman ta.
Mamaki Ammar yake, Yarinyar da wata shigar idan tayi wataran sedai yabar mata falo, shine yau ta wani basar tasa Hijjabi, sharewa Yayi yace
"Ashe kin dawo?" maimakon ta amsa masa seta kalle shi kawai.
"Dakin min Waya nazo na taho dake, tunda baki da lafiya"
"Hmm to koma dai mene ne, ai gani na dawo"
"Ki tashi kisa kayanki mana, kinsa Hijjabi kin duƙunƙune ko har yanzu jikin ne?"
"toni kazo kana ta kallona, a haka zansa kayan?"
Ammar yace "Hmm shikenan bari in baki guri, ko akwai abunda kike buƙata in siyo miki?"
Girgiza masa kai tayi alamar A'a, ya tashi ya fice.
Yana zuwa É—akin sa ya tarar da Abinci, wani murmushi yayi yai salla, sannan ya zauna yaci Abincin, rabon da yaci Abinci haka har ya manta, yayi missing É—in Abincin ta sosai.
Har yanzu Mufeeda basar da Ammar take, taƙi sakin jiki dashi kamar da, yana rage mata ayyukan gida sosai saboda tana fama da laulayi sosai, Amma a hakan kafin ya dawo take masa girki ta gyara ko'ina.
Sam Mufeeda bata iya cin Abinci se 'yan kame kame yana matuƙar tausayin ta yadda take fama da laulayi amma ko inda take bata so yaje.
Yau Ammar be dawo da wuri ba dan se dare ya koma gida, yana komawa ya tarar bata falo ya bita ɗakin ta, yana zuwa ya tarar ta kwanta dan harta fara bacci, gaban gadon ta ya ƙarasa ya durƙusa yana kallon fuskarta data faɗa sedai fatar ta data ƙara haske, Zuba mata idanuwan sa yayi yana kuma ƙare mata kallo, Sosai Ammar yake jin Mufeeda a ransa, ƙamshin turaren Ammar ne yasa ta farka, A hankali ta buɗe nata idanuwan da suka yi mata nauyi saboda bacci kallon sa ta ɗanyi ta mayar da idon ta ta lumshe.
"Sannu ya jiki?"
"Da sauƙi" ta faɗa ba tare da ta buɗe idon ta ba.
"Ki tashi ga Maltina da fruit na kawo miki ko zaki iya ci, tunda ba kya iya cin Abinci" girgiza masa kai tayi tace
"Na ƙoshi"
Gaba É—aya Ammar baya jin daÉ—in wannan Mood É—in nata, ya kuma Æ™asa da murya yaceÂ
"har yanzu baki huce ba fushi kike dani ko?"
Girgiza masa kai tayi.
"to dan Allah ki tashi kici Abinci, bana jin daɗin yanayin da nake ganin ki, nayi nadamar maganganun dana gaya miki, Amma kiyi haƙuri bazan sake ba Insha Allah"
"Ai nima ya wuce a gurina"
"Banga alamar hakan ba tunda har yanzu bakya kulani kamar da, kin dena Yimin Addu'a, kin dena sakin jiki dani, ko sena bada cin hanci ne? Biscuit ko chocolate, gayamin wanne kike so?" Yai maganar yana sake langaɓar da kai cikin sigar rarrashi
Murmushi tayi taceÂ
"Ai am still under punishment, ko kaman ta ne?"
"Baki haƙuran ba kenan?"
Miƙewa zaune tayi ta kalle shi
"eh gaskiya ban haƙura ba"
"Meyasa?"
"Saboda baka sona"
ÆŠan zaro ido yayi yaceÂ
"Nine nace bana son ki?"
Cikin shagwaɓa tace "to ka taɓa cewa kana sona ne?"
Murmushi yayi yace "Hmm wayo zakimin ko? Ni dai kiyi hakuri kidena wannan fushin"
Faɗawa tayi jikin sa ta rungume shi tace "Nifa ya wuce"
Yasa hannayen sa ya ƙara rungume ta a jikin sa yace "I miss you ƙwailata"
Murmushi tayi tace
"bazaka dena cemin ƙwaila ba ko?"
"Eh mana har yanzu ke ƙwaila ce"
"Hmm zan rama ne"
Daga nan suka jone abunsu ya sata a gaba yana bata Fruit
(Note: kayan marmari mussaman ga mace me ciki yana da amfani da kuma ƙara mata lafiya, yana dawo da test ɗin baki da sukan rasa mussman a first trimester wato watannin ukun farko)
Ammar yace" Anty Maryam ta wahal dani, nasan da dagani seke ne zamu sasanta da wuri, please idan mun samu Saɓani ki bari mu dinga gyarawa a tsakanin mu base wani yaji ba"
"Yaya Ammar nima ba haka naso ba, naso ka saurareni a lokacin amma kaƙi, kuma bayan fitarka naji kamar zan mutu shine na tafi gidan Yaya Amina"
"Hakane raina ne ya ɓaci sosai, nasan kina haƙuri da ni amma ki ƙara kinji Jaririya ta, ban san ina sonki haka ba seda na zauna a 'yan kwanakin nan babu ke, kin mun wayo kin shiga raina ba tare da na sani ba"
Murmushi tayi masa tare da kwanciya a jikin sa tace "Yaya Ammar nima nasan kana haƙuri dani, duba ga yanayin ƙuruciya ta da kuma shirme na wani lokacin, Allah ya ƙara mana haƙuri da juna"
"Ameen, Amma ya aka yi haka ta faru baki sanar dani ba, hankali na ya tashi sosai akan abunda ya faru"
Nan ta zauna ta warware masa abunda ya faru tsaf tun daga ranar da aka fara kiran ta, Sannan ta É—ora da cewa
"Abunda yasa ban gaya maka ba, nasan halinka Yaya Ammar kallo É—aya kake wa abu kayi masa hukunci, baka fiye tsawaita bincike ba, kana Amfani ne da abunda zuciyar ka ta gaya maka ko abunda idonka ya gani"
Ammar yace
"shikenan abunda za'ayi zaki bani layin da kike Amfani da shi, zan canza miki wani Insha Allah, Sannan zan duba matakin da zan É—auka, Sannan gobe insha Allah zan maida ke Asibiti gaskiya, rashin cin Abincin nan yana damuna"
Haka suka shirya suka jone abunsu, dukda rashin lafiyar Mufeeda, be hana Ammar shan Shagalin sa ba, he show's her how much he miss her, Mufeeda kam taga ta kanta, yana ce mata Æ™waila Amma a hakan.... ðŸ¤ðŸ¤, seda ya nutsu ya dawo hankalin sa, sannan kuma yaga yadda ya tara mata gajiya, ya taimaka mata ta gyara jikin ta ta kwanta sannan ya tafi É—akin sa.
*****************
Saima se tayi Sati ba ta riƙe naira ɗari biyu ba, Jabir baze kaita Asibiti ba dan haka befi sau biyu taje awon ciki ba, yauma da ta tashi maimakon yadda take ji ana faɗa daga alamomin Naƙuda akwai zubar ruwa se ita taga Jini, bata ɗauka matsala bane dan haka ta ci gaba da harkokinta sama sama, Sosai Marar ta ta fara ciwo, ga baya ya riƙe se jiri da take ji idon ta yana mata duhu, Jabir ya fito falo yana gyara links ɗin rigarsa, kunnen sa ɗauke da wayar salula yana magana
"Haba my Fatiyya, kiyi haƙuri dan Allah, yanzu zaki ganni zanzo in kaiki da kaina, kina dani meye sekin jira driver ɗinku, ki jira gani nan yanzun nan zaki ganni"
Saima tace "Jabir dan girman Allah ka kaini Asibiti, wallahi ina ga haihuwa zanyi, bayana kamar ya ɓalle"
"to uwar ciwo, baki ma tabattar da naƙudar bace, ina EDD ɗinki se ƙarshen wata za kice wani naƙuda kike, ga ɗari biyu kije Asibitin in haihuwar ce se kimin waya"
Shiru tayi tana binsa da ido ya É—au mukullin motar sa ya fice, duhu ta ci gaba da gani a idon ta dan haka ta nemi guri ta kwanta akan kujera
******************
Mufeeda taƙi yadda Ammar ya maida ita Asibiti tace ita likita yace se cikin ta yayi wata huɗu sannan zata fara zuwa Awo haka ya haƙura ya ƙyale ta.
Bayan fitar Ammar sega su Maman Amir sun shigo mata.
Fuska ba yabo ba fallasa Mufeeda ta karɓe su,
Maman Amir tace "Mufeeda ashe baki da lafiya kina gida? Hankalin mu ya tashi kwana biyu bama ganin ki, shine muka tambayi mijin ki yace mana kina gida babu lafiya"
Mufeeda tace "Eh banji daɗi bane ba"
Maman Sadiq tace "Allah sarki sannu, munso muje gidan naku duba ki ai, to kin san halin Mijin naki bashi da fuska shiyasa bamu tambaye shi ba"
Mufeeda tace "Ai na warware ma Alhamdilillah"
Maman Amir tace "Aikam dai mijin ki bashi da fuska, ai Sa'idu me kayan miya ne ya gaya mana a gaban sa kika wuce kika hau A daidaita sahu kaman ba kya hayyacin ki, kina ta kuka bayan fitar shi mijin naki, shine hankalin mu ya tashi muka ce bari mu biyo muga ko lafiya, shine ya gaya mana ai baki da lafiya kina gida "
Mufeeda tace " Sa'idu me kayan miya kuma? "
Maman Amir tace " Eh wallahi munje cefane yake ga yamana "
Jinjina kai Mufeeda tayi ba tace komai ba, suka ƙaraci soki burutsun su, ciki hadda yi da Maman Nur wadda ta kasance a cikin su, Mufeeda ba tace musu komai ba, ganin Mufeeda bata da niyyar kulasu yasa su kayi mata sallama suka fita.