← Book details Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 64

Sashe 45

Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kusan gaba sosai Ammar yake da Mufeeda ba tare da tasan laifin da tayi masa ba, ko haÉ—a hanya suka yi, idan yayi mata tsawa se tayi dana sanin haÉ—uwar da suka yi.
Gaba ɗaya ya zame mata tamkar wani dodo, duk da jin kansa amma yanayin yadda suke kasancewa tare, suci Abinci tare yanayi ne da yake matuƙar sata nishaɗi, Amma ƙirƙiri yanzu fargabar ganin sa ma take yi balle su haɗa hanya, gashi ita bata san laifin da tayi masa ba.
Duk wani abu da ya kama na ciyar wa be fasa ba, Amma ba zata dafa yaci ba ko gaisuwa bata haÉ—a su.
Sosai zaman da suke yi yake damun ta ya kamata ace idan laifi tayi masa ya gaya mata, dan haka ta yanke shawarar zuwa ta same shi taji laifin da tayi take fuskantar wannan hukuncin me matuƙar tsauri.

ÆŠakin sa taje ta same shi yana shiri ze fita, É—agowa yayi ya kalleta ya É—auke kansa, jiki a sanyaye tace

"Yaya Ammar ka dubi zatin Allah ka gayamin laifin da nayi maka kake min wannan hukunci"

Banza yayi mata ya ɗau wayarsa ya saka a Aljihu yana ƙoƙarin kewaye ta ya wuce, tare shi ta kuma yi cikin kuka tace
"Yaya Ammar zuciya ta ba zata iya É—aukar wannan hukuncin ba, dan Allah ka gayamin me nayi maka haka?"

A fusace yace "get out from my sight bana son wannan salon yaudarar taki, 'yar ƙanƙanuwar yarinya dake amma kin iya yaudara"

Zubewa tayi akan gwiwoyin ta tace "Naji na yadda amma dan Allah kayi haƙuri dukda ban san laifin da nayi maka ba, Amma kayi haƙuri"

Ture ta yayi daga gaban sa yasa kai ya fice, da gudu ta kuma binsa falon tana riƙe rigar sa tana kuka.

Fizge rigar sa yayi yace
"Karki ƙara riƙe min riga munafuka mayaudariya, seda na yadda dake zaki tozartani ki bani kunya"

"Yaya Ammar me yayi zafi kake kirana da wannan miyagun maganganun? Wani laifi ne haka na aikata? A zaman mu da kai bana tunanin na aikata wani kuskure dana cancanci wannan kalmomin daga bakin ka"

"Tambaya ta ma kike yi? Da Aurena a kanki kike Soyayya da wani a waje, kin san zaki yi soyayya da wani dan me kika dage sekin Aureni kike yaudara ta da cewar kina sona, kinsan me kuɗi kike burin Aure meyasa kika Aureni kikemin daɗin bakin cewar ni kike so ba abun hannu na ba? An kiraki a waya na ɗaga wani ɗan iska yana faɗin yayi missing ɗinki, na fita sallar Asuba an tareni ance an ganki ƙiri ƙiri da wani me mota kina zance, akan me zakimin haka? Har yanzu zuciya ta ta kasa Amincewa zaki min hakan, sakamakon kalaman yaudara da kike Amfani dasu akaina, nasan da mace na Aura me hankali da inaga duk hakan bata faru ba, nayi nadamar Auren ki da nayi "

Shiru tayi seda yayi ya gama ta É—ago idanun ta da suka koma Jawur ta kalli Ammar tace
"Ba dan sharrin Soyayya ba Ammar babu abunda zesa in soka in zauna da kai da wannan halin naka, Yaya Ammar ko a kotu Alƙali yana bawa mai laifi damar kare kansa koda kuwa a gaban Alƙalin me laifi ya aikata laifin, ba kai ya kamata ka yi dana sani ba, ni ya kamata inyi dana sanin yin Aure, A iya zamana da kai na gane abubuwan da mahaifiya ta da 'yan uwana suke jiye min, Yaya Ammar ko dan Darajar Soyayyar da nake maka ya kamata kayi min Adalci ban cancanci jin wannan kalaman daga bakin ka ba, a zaman mu da kai a Alkhairaina guda nawa ka yaba? Amma yau akan kuskuren da baka da tabbas na Aikata ka hukunta ni da kalamai masu muni, kalaman da bazan manta ba har in koma ga Allah, Shikenan Nagode sosai, sannan bazan gajiya ba Allah ya baka haƙuri, idan ka sakko daga Fushin nayi maka bayanin abunda ya faru, Adawo lafiya Allah ya kiyaye hanya "

Tana gama maganar ta tafi ɗakin ta tana shehssheƙar kuka me tsuma zuciya, seda Mufeeda tai wannan maganganun sannan Ammar ya dawo hayyacin sa ya fara tunanin Anya kalaman da yayi Amfani da su sun dace? Take kuma yaji kamar be kyauta ba gaba ɗaya jikin sa yayi sanyi, tabbas ya kamata ya bincika kafin yayi mata hukunci, haka nan ya ɗau key ɗin babur ɗin sa ya fice.

Bayan fitar sa Mufeeda gaba ɗaya ji tayi ta tsani zaman gidan, gaba ɗaya ta rasa abunda yake mata daɗi ga zuciyar ta da take ta faman bugawa da ƙarfi, miƙewa tayi tasa hijjabin ta ta ɗau wayar ta ta fice, tafiya kawai take dan wani matsanancin ciwon kai ne ke damun ta ga Jiri da take ji dan haka kawai jefa ƙafar ta take, tana fita bakin titi ta tare me Napep ta gaya masa unguwar daze kaita ta faɗa ciki tana goge Hawaye.

Akan idon Sa'idu me kayan miya hakan ta faru, dan haka ya jinjina kai yace "Yau akwai zazzafar Jarida"

Me Napep ɗin daya ɗauki Mufeeda kuwa tsoro ya fara ji karta mace masa a Babur, dan wata irin shaƙuwa take tana sauke numfashi da ƙyar, seda ya kaita har ƙofar gidan Yaya Amina, Mufeeda ta fito daga A daidaita sahu abu ya faskara dan harta fara fita daga hayyacin ta da ƙyar take numfashi.

Ƙwanƙwasa gate ɗin Yaya Amina me Napep ɗin yayi, akayi sa'a Yaya Amina ce ta buɗe, suka gaisa dame Napep sannan yace mata

"dama waccan baiwar Allah na É—akko tace nan zan kawo ta, kuma gashi munzo ta kasa fitowa kamar bata da lafiya"

Aikuwa Yaya Amina na leƙawa ta hango Mufeeda a cikin Napep ɗin ta riƙe ƙirji, da Sauri Yaya Amina ta koma cikin gida ta ɗakko mayafi suka fito tare da mijin ta, Mufeeda na ganin Yaya Amina ta sake fashewa da kuka, suka ɗakko ta daga A daidaita sahu zuwa cikin gidan, mijin Yaya Amina ya sallami me Napep.

A tayani Share ba dan halina ba 😍😍😜

NAGA NAFARA ƁATAWA 'YAN TEAM ƊIN MUFEEDA RAI, ANA CEWA HAƘURIN MUFEEDA YAYI YAWA, GA WATA TAMBAYA, DA MUFEEDA BATA KASANCE ME HAƘURI BA WANI IRIN ZAMA KUKE TUNANIN ZATA YI DA WANNAN MIJI NATA ME BAUƊAƊƊEN HALI? IDAN BA TAYI HAƘURI BA TAZAMA ME YAWAN ƘORAFI YANA HAƊA SHI FAƊA SA 'YAN UWAN SA A SANNU WATARAN SE IYAYEN MIJIN TA SUN FARA JIN HAUSHIN TA.
AYIMIN HAƘURI LABARIN NE YAZO A HAKA DAN HAKA KU BIYONI SANNU A HANKALI DAN JIN YADDA ZATA KAYA
KISSA BATA NUFIN KWALLIYA DA KWARKWASA BANE, AKWAI HAƘURI DA JURIYA.

Taku har Kullum Aisha Humaira, Daddy's girl ko ince Ayshercool, ina godiya sosai da ƙauna da kuma bibiyar littafin da kuke

Domin sharhi gyara ko shawara
07063065680
✨✨✨✨
*WATA KISSAR...... *
✨✨✨✨✨

( *Sai Mata* )

*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*_A SHORT LOVE STORY_*

*Story and written by*

'''AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)
The experience writer of ABDUL JALAL'''

Na sadaukar da wannan littafin ga ÆŠaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba

Watpad @ Ayshercool7724

What's app 07063065680

Gmail [email protected]

Please follow me on Wattpad, vote and Comment

https://www.wattpad.com/1096499534?utm_source=android&utm_medium=com.fmwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Ayshercool7724&wp_originator=NWkhlySuZ8Eug%2BopXFfcycv2JGS3axjaccC5%2FbUYT6YzeXAYV4ybw7FnTr8fHQDwo5ncF8TNfQfelSdeR5t0OZi0%2FKAiAcvwuLa561y0j%2BMpxBPI15z3EyzU4ZruY9KP

__Happy marriage life to my lovely friend_, __MARYAM MUSA ƁAIDU_I WISH YOU A VERY HAPPY MARRIAGE LIFE DEAR_

ELEGANT ONLINE WRITER'S

                 
             
                          Page 22

Har Ammar ze share wayar ya tafi É—akin sa se kuma ya É—au wayar ya nufi É—akin Mufeeda.

Yana zuwa ya tarar har tayi bacci ta dunƙule a guri ɗaya ko kayan jikin ta bata canza ba da alama dai baccin ba shiri ya ɗauke ta, fuskarta duk hawaye se ajiyar zuciya take.
Ɗan girgiza kai Ammar yayi ya zauna gefen gadon ya ɗagota ya cire mata hijjabin jikin ta, a wasu lokutan Mufeeda na da  nauyin bacci sosai dan haka ya rage mata kayan jikin ta data kwanta da su, ya ƙura mata ido ta ɗan rame sosai, Amma tubarkallah tana da kyau dai dai gwargwado, musamman idan tana bacci se yaga ƙuruciyar ta ta ƙara fitowa,  iya goshin ta ya ɗau zafi sosai yayin da sauran jikin ta yayi sanyi saboda kuka.

Ammar ya daɗe yana kallon ta yana jin wani abu na masa yawo a jikin sa ba tare da ya tabattar dame hakan ke nufi ba, a hankali ya janyo pillow ya kwantar da ita a kai yana cigaba da kallon fuskarta, sosai yake jin tausayinta be kamata ya cigaba da yi mata faɗa any how ba, hakan yana sata a cikin damuwa sosai, gefe guda wayar Mufeeda na ci gaba da vibrating, har ya miƙe ze bar ɗakin yaga vibration ɗin wayar ze iya tashin ta dan haka ya dawo ya sunkuya ya ɗau wayar, baƙuwar lamba ce babu suna ya danna alamar amsawa ya kai kunnen sa zeyi magana, shiru yayi yana sauraren abunda me wayar yake faɗa, kunnuwan Ammar ba zasu iya jure jin abunda wannan la'anannen dabe san darajar Aure yake faɗa ba, Idan kunnuwan sa ba ƙarya suka jiye masa ba to tabbas kalaman soyayya ne wanda ya kiratan yake faɗa

"tun ɗazu nake kiran ki saboda inji daddaɗar muryar ki ko da zagina kiyi in samu inyi bacci cikin kwanciyar hankali, Amma kinƙi ɗaga waya ta, kice wani abu mana mufeeda, Shikenan tunda ba zaki magana ba ɗaga wayar da kika yi ma ya tabbatar min kina lafiya, Ina son ki fiye da yadda wannan mijin naki me girman kai da baki da tabbacin yana sonki"

A hankali Ammar ya ajiye wayar, zuciyar sa tana wani irin bugu da ƙarfin gaske tamkar zata tsaga ƙirjin sa ta fito, gashin jikin sa duk ya mimmiƙe saboda ɓacin rai, ya kalli inda Mufeeda take kwance tana bacci, se faman sauke ajiyar zuciya take she's looking so innocent.

Da ƙyar Ammar yaja ƙafar sa ya bar ɗakin yana ci gaba da jin Yadda zuciyar sa take bugawa.
Chapter 45 · 0% Book details