Sashe 62
Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jidda tace "Wai Maryam baki san hakin da nake ciki bane?"
Maryam tace "koma na sani mezan iyayi akai? Tun farko ni dama wannan Zainab ɗin ba tayi min ba, na baki shawara shaƙuwarki da ita tayi yawa, Amma kika ƙi ji, Abunda haƙuri be baki ba rashinsa baze baki ba, kuma wallahi in baki nutsu ba Abba yaji labarin yadda kike ɗagawa mijin ki hankali kin san sauran"
Sallamar Ammar ce ta hana su ci gaba da Hirar, ya shigo É—akin ya zauna, ya kalli Yaya Maryam
yace
"Sarakan yawo, daga Yaya Jidda tazo shine kema kika taho ko?"
Anty Maryam tayi dariya tace
"A'a zuwan ta daban nawa daban, kawai mun haÉ—u ne, Ai bansan tare kuke da Mufeeda ba, banga babur É—inka a waje ba"
"Eh yana gurin gyara ne"
Ya kalli Umma yace "Umma me kika dafa ne, muna jin Yunwa fa, daga nan wani gurin zamu tafi"
Jidda tace "Ammar shine kazo ka kula kowa, Amma ni ka shareni kamar baka ganni ba, balle ka tambayi halin da nake ciki, koda yake ba abun mamaki bane, tunda ka fi ƙaunar matar ka a kanmu, damuwar ta itace damuwa 'yar gwal"
"Wallahi tafi gwal"
Ammar ya bata Amsa kai tsaye cike da basarwa.
"Ni kake gayawa Matar ka tafi gwal ko?"
Shiru yayi mata yaƙi bata Amsa, a fusace tace
"Ai dama nasani, ba yau kasaba wulaƙantani ba akan Yarinyar nan, ƙiri ƙiri naje gidanka da buƙata amma kaƙi saurara ta, ko Abinci ya gagara a bani a gidan ka, kuma kana kallo ba kace komai ba"
Shiru Ammar yayi yana mamakin wani irin hali ne haka da Jidda.
Yaya Maryam tace "Haba Yaya Jidda, kema fa ɗan wasu kike Aure, kuma Yayan wasu, sannan ƙanin wasu, shekaru Ashirin da biyu yana miki bauta ya wahalta miki kamar besan ciwon nema ba, shikenan ke kuma wata ba zata mori ɗan uwanmu ba? Mu yiwa kanmu Adalci mana, me Ammar yake dashi wanda yake wahaltawa Mufeeda da har kike iƙrarin ya tare a gurin ta? Ita kin san halaccin da take masa? Kin san ita ɗawainiyar da take da shi, ai macen ma da zata iya Zama da ɗan uwan mu da irin halinsa na Fushi da zuciya, Yabo ya kamata ta samu"
gaba É—aya Mufeeda ta takura taji babu daÉ—i abubuwan da suke faruwa duk a dalilin ta, Umma kuwa ta hau yiwa Jidda FaÉ—a, jiki a sanyaye Mufeeda ta bar É—akin dan bekamata ta cigaba da zama ana rigima a kanta ba.
Tana fita Ammar ma ya miƙe yabi bayan ta, Abinci ya zubo ya jata ɗakin sa suka zauna yana bata, sedai sam hankalin ta ba'a kan Abincin yake ba.
Yana bata yana mata hira, Amma sam taƙi sakin Jiki, ganin haka yasa Ammar yace
"Shirya muje kiyi musu sallama, mu tafi"
Ta jinjina masa kai, haka aka yi jiki ba ƙwari Mufeeda taje tayi wa su Umma Sallama, ta zaci Umma zata canza mata Fuska ko wani abun, Amma taga saɓanin hakan.
Mufeeda tasa hannu a Jakarta ta É—akko dubu uku tace "Umma ga wannan, ki É—au dubu É—aya a ajiyewa Abba dubu biyu"
Girgiza kai Umma tayi tace "A'a Mufeeda, Nagode Allah yayi Albarka, Amma ai sunyi yawa, ki riƙe Abun ki, ga hidima tana tunkarar ku Allah ya raba lafiya"
Kunya ce ta kama Mufeeda, dan ba tayi zaton Umma ta gane tana da ciki ba, saboda bata cire hijjabin jikin ta ba.
Ammar kam ba kunya caraf ya amsa da "Ameen ya Allah Umma"
Mufeeda a ɗan Shagwaɓe tace "Amma Umma meyasa idan Yaya Ammar ya baki kike karɓa? Nawane bakya so ko?"
Gaba É—aya Jidda ta tsani yarinyar nan, duk wani salon bariki ta iya.
Umma tai murmushi irin na manya tace "Aishi wannan ƙyale shi, suyi ta nemowa suna bamu muna cinyewa"
Ammar yace "yau dai na ganku a rana keda Umman"
Mufeeda tace "Dan Allah Umma karfa yayi mana dariya, Anty Maryam kisa baki mana"
Anty Maryam tace "Gaskiya Umma kar kisa Yayi mata dariya mana"
Da ƙyar Umma ta karɓa, tana ta mata Addu'a dasa Albarka kamar ta bata duniya, suka yi Sallama suka tafi.
Seda suka shiga Ammar ya nuna mata dabbobin ta, suna ta hayayyafa gwanin sha'awa, Sannan suka tafi.
Bayan fitar su Mufeeda Anty Maryam ta bawa Umma labarin abunda su Fa'iza suka yi wa Mufeeda, da yadda ta zauna a gurin ta bayan sun samu Saɓani, Abun ya daki zuciyar umma, tayi tayiwa Ammar faɗa idan Fa'iza tazo tace ya mata wulaƙanci.
Maryam tace "Wallahi Jidda ba kowace mace bace zata iya abunda Mufeeda tayi ba, na haƙuri da Ɗan uwan mu, Muddin kikayi dalilin kashe masa Aure wallahi kin cuce shi, kuma baze manta ba, nan ma Umma tai kan Jidda da faɗa, da taga alamun babu me goya mata baya, ta miƙe tai haramar tafiya, ranta a ɓace.
Ammar yaji daÉ—in Abunda Mufeeda tayi, dan be san zata basu ba, suna tafe a hanya yace
"Mufeeda Nagode sosai, Amma kuÉ—in da kika bawa su Umma yayi yawa, karki kwashe jarin naki fa"
Wata uwar harara tai masa wanda hakan ya shashi yin shiru, suka tari abun hawa zuwa unguwar su Mufeeda.
Suna yin Sallama ta tarar da Baba ze fita, ai da gudu ta tafi ta rungume shi, seda Ammar yaji tsoron karta jiwa kanta rauni, ko nauyin cikin bata jiba take wannan tsallen.
"Autar Baba naga kin zama ƙatuwa, Ammar me kake bata ne? Ta cinye maka tuwo ko?"
Murmushi Ammar yayi suka gaisa da Baba, Baba yace
"tunda 'ya' ya na sunzo bari in zauna muyi hira"
Ammar yabi Baba ɗakin sa, Mufeeda ta ƙarasa gurin Mama, Ta tarar da Yaya Fadeela, Yaya Fadeela ta hangame baki tana bin Mufeeda da kallo, Mufeeda ta rungume Mama tana Shagwaɓa.
"Mamana ina Missing É—inki sosai"
Fadeela tace "Auta wannan ƙiba haka? Ke kuwa me kike ci haka?"
"Abunda kike ci mana"
Hira suka shiga yi, Fadeela tace "Auta a cire hijjabin mana, kowani salon ne kuma haka?"
"bazan cire ba É—in"
"Autar Baba kodai kodai"
Hararta Mufeeda tayi tace "Kodai me?"
Ammar yai sallama a falon Mama suka gaisa, sannan yace ze tafi bayan la'asar zezo su tafi.
Mufeeda ta tashi ta tafi rakashi, suna fita Fadeela tace
"Mama kinga abunda nagani kuwa?"
Mama tace "A ina?"
"Kamar ciki ne da Yarinyar nan fa"
"Hmm Fadeela kenan, nagani mana se fatan Allah ya raba lafiya"
Mufeeda ta dawo falon suka cigaba da hira, tunda Mufeeda ta cire hijjabin ta Fadeela taga cikin Mufeeda har ya fito, ta dinga tsokanar ta.
"Mufeeda ni zan miki wankan Jego fa in kin haihu"
"Allah ya kiyaye, wallahi ba zaki minba"
"Ohh ni Fadeela, wai Mufeeda da ciki"
"Eh ya ranki? Shiyasa nake raina ki takuramin kike"
Haka Mufeeda suka wuni suna hira, Fadeela tana ta tsokanar ta, duk lokacin da Mufeeda tazo gida idan tana hira Mama tana fuskantar Mufeeda na cikin kwanciyar hankali, Ammar ya isa da gidan sa, ta dinga tuna lokacin da take ƙoƙarin hana Auren nan, yadda mazan yanzu suke se a hankali samun kamar Ammar se an tona.
**********************
Wata É—aya da sakin Saima Jabir yana ta shirin Aurensa, Saura Sati biyu a fara biki, Amma Ammar, da Aminu sam basa goyon bayan Auren Jabir, dan haka sam besa su shirgin Auren sa ba.
Saima kam tana murmurewa, ta siyo form ɗin makaranta ta cike zata koma, dama tayi N. C. E, ta sai D. E Form zata koma Jami'a, ta tura aka kwaso mata kayan ta tsaf daga gidan Jabir, dukda gwaggonta ba wata me ƙarfi bace, Amma sam bata tsangwamar Saima, Saima ta iya ɗinki dan haka ta cigaba da sana'ar ta, suna rufawa juna Asiri, nan da nan ta fara dawo da ƙibarta kamar ba ita ba.
Sa'idu me kayan miya aka yanke masa hukunci zaman shekara uku a gidan yari ƙarƙashin wata kotun Addinin musulunci, tunda Abun nan ya faru layin su Mufeeda suka zauna lafiya, ba gantali ba tashin hankali kowacce tana gidan ta, idan suka haɗu da Hajara a hanya har guduwa suke su ɓuya
Ammar ya dage sosai da zuwa kasuwar nan, da safe ya sauke kaya a biya shi, ya siyo wani abun ya fito bakin kasuwa ya siyar, ɓangaren Mufeeda ma likkafa ta cigaba, yanzu har manyan kuloli take cikawa da kayan sanyi, Almajirai suzo su ɗauka sukai mata kasuwa
Da yake Mufeeda tasu ta É—anzo É—aya da Hajara, ta bata shawarar ta dinga haÉ—awa da snacks za tayi ciniki, dan sune Abincin shaf shaf mussman ga ma tafiya, Aikuwa Mufeeda ta shawarci Ammar ya bata goyon baya, a hankali ta fara haÉ—awa da snacks É—in.
Wataran se Ammar ya dawo da daddare yake temaka mata ta haÉ—a kayan siyarwar, saboda cikin ta ya tsufa.
Duk abun nan Sam Ammar besa mata ido akan abunda take samu ba, ba ruwan sa sannan babu abunda ya fasa yi na hidimar gidan sa.
*********************
Satin bikin Jabir ya kama akai biki aka sha shagali, aka yi ɓarnar dukiya, kamar yadda akayiwa Jabir Alƙawari aka bashi gida da mota, aka sake masa Aiki a kamfanin Mahaifin Fatiyya.
Sedai tun a ranar farko da ta tare Jabir ya gane Fatiyya tasan Maza, Amma ba shi da ikon magana ko dan wannan daular da'aka sa shi a ciki, haka nan ya haƙura bece komai ba.
Ammar sun gama sauke kaya a kasuwa, yana shirin tafiya Wani hamshaƙin Alhaji da suka gama sauke masa kaya, yasa aka kira masa Ammar,Ammar yazo suka gaisa.
Ammar a nutse yake sam baya wannan rawar jikin da sauran suke idan sunga Alhajin, Alhajin yace
"Dan Allah in ba zaka damu ba kuÉ—i nake so ka kaimin banki"
ÆŠan zare ido Ammar yayi, shi dai yasan ba ma'aikacin Kamfanin Alhajin bane, kawai aikin sa idan ya shigo kasuwar za'a sauke kaya ya sauke a biya shi, Amma me yasa yace masa ya kai masa kuÉ—i banki?
Alhajin yace "Dan Allah ka temaka, in bazaka damu ba, na yaba da hankalin ka ne, depositing kawai zakayi min, ga kuɗin can a mota, me kaimin ne baya nan, million biyar ne"