← Book details Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 64

Sashe 28

Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ammar shiru Yayi yana tunani, ya tuna Yadda Jabir yake Soyayya da Saima kaman babu wata mace da tai Saura a duniya sama da ita.
Ammar yace
"tabbas Jabir kana da laifi, ba kowane ze iya jure ka zagi iyayen sa yai maka shiru ba duk mutuncin ka da yake gani, karka manta da haƙoran ta bayan iyayen ta sun gama ɗawainiya da ita ka ganta ka aura, babu yadda zata iya jure cin zarafin su gaskiya, kaman yadda bamu da juriya da jarumta irin na iyayen mu haka suma matan basu da haƙuri da biyayya kaman na iyayen mu duk sedai muyi haƙuri da juna, amma batun chatting da 'yan mata lokacin da matarka ke buƙatar lokacin ka, to tabbas idan me raunin Imani ce hakan zesa itama ta fara tunanin fara chatting da wasu mazan"

Suka dinga yiwa Jabir Nasiha, zasu tafi ne Saima ta fito idon ta jawur saboda kuka ta miƙawa Ammar turaren wuta, da humra tace
"Ammar gashi ka kaiwa Amarya a bata haƙuri, Insha Allah ina nan tafe mu gaisa, Kaikuma Aminu se Fiddausi ta haihu ma haɗu"

Ammar yace "to mungode zan gaya mata Insha Allah, sannan Adinga haƙuri ana kai zuciya nesa saima, a unguwar mu babu wanda be san Soyayyar ku da Jabir ba, be kamata ace daga yin Auren ku hakan tana faruwa ba"

Murmushi me ciwo Saima tayi tace "Ammar kenan, Soyayyar nan duk a baki ce ya nunamin, kudai ina muku fatan Alkhairi ku gaida gida" ta juya É—akin ta tana sharce hawaye.

Ammar yake tunanin ita kuwa wani irin pain take ji a zuciyar ta har take wannan kukan haka. Su kayi wa Jabir sallama suka tafi, seda Ammar da Aminu suka ƙara tattaunawa akan batun, Ammar yace

"gaskiya Aminu lamarin rayuwar nan akwai ban tsoro, shiyasa naita gudun yin Aure a baya"

"Ammar kenan, ai abun dace ne, kaga ni babu wata babbar matsala da nake fuskanta tsakanina da fiddausi se tarkacen ƙawaye da yawon maƙota, sune babbar matsalar ta, nayi nayi ta dena taƙi, Amma ta wani ɓangaren idan na duba alkhairan ta se in share ta kawai inyi haƙuri tunda nima haƙuri take dani"

Suka gama taÉ—insu sannan Ammar ya nufi gida, ya É—an tsaya a hanya yaiwa Mufeeda siyayya, sannan ya tafi gida, tunani yake tayi ya gano me Mufeeda take yi wanda baya so, amma ya kasa ganowa se yai tunanin ko dan Yarinya ce, ko kuma tana jin tsoro nane yasa bata min wasu abubuwan? Ko dan bamu daÉ—e tare ba? A'a wannan Yarinyar da tana jin tsorona da bata tunkareni ta kalli tsabar idona tace tana sona ba wata zuciyar ta bashi amsa.

Da wannan tunane tunanen yaje gida, se daya duba agogonsa yaga sha É—aya na dare.
Aikuwa yana shiga tana falo a zaune tana rarraba ido, tana ganin sa ta miƙe
"Yaya Ammar ina ka tsaya haka? Har na fara tsorata ko wani abun ne ya same ka"
"Sarkin tsoro, ba abunda ya sameni gani na dawo"
"gaskiya ka daÉ—e sosai"
"Ai gani na dawo dai, ya jikin naki?"
"Naji sauƙi Alhamdilillah"
"Haka ake so, ungo gashi nan ki samu Kisha, tunda yau baki ci Abun kirki ba"
Ƙatuwar Jarkar yoghurt ce a ciki,
Murmushi tayi tace "Masha Allah, Nagode sosai mijina Allah ya baka Aljanna maÉ—aukakiya, Yasa ka gama da duniya lafiya"
"Ameen"
Ta É—akko kofi ta zubawa Ammar ta bashi yace shi baya sha, ita dai ta sha ya sata a gaba ta sha sosai sannan ta ajiye sauran.
Ta kalle shi tace "Mijina meke damunka ne? Naga kaman akwai damuwa tare da kai"
Kallon ta yayi da mamaki ya akai ta gane yana da damuwa.

Ya maze yace "gajiya ce ni babu wata damuwa dake raina"

"idan gajiya ce kawai take damun ka ina ganewa, yau yanayi ya nunamin bayan gajiya akwai damuwa"

Miƙewa yayi yace "jeki kwanta seda Safe"

Bayan sa tabi da kallo daga bisani ta miƙe ta tafi ɗakin ta, yau ta sha baccin rana, saboda rashin lafiyar ta, dan haka ta kasa bacci, tana ta tunanin meke damun Ammar? "dole inyi wani abu kar ya kwana da damuwa.

Ta ɗakko wayar ta tura masa saƙo
"My love, hau online kaga wani abu"

Ya tura mata "me kike baki Bacci ba?"

"Nakasa baccin ne, ka hau ka gani"

Ya buɗe data ɗinsa ya shiga what's App, hoton ta ta tura masa, tayi wa gashin kanta ado, ga wata body hook ce a jikin ta pink, leɓen ta raɗau da jambaki se shining yake, ta ɗan turo baki ta lanƙwasa wuya, a haka ta ɗau hoton ta ɗora waƙa me daɗi akan hoton.

Ammar na buÉ—e hoton besan lokacin da ga tura mata
"Wow Masha Allah"
Wani murmushi tayi tana daga kwance ta tashi zaune, ta tura masa
"Nayi kyau?"

"Ba laifi kin kusa yin kyau, dama kin girma ne da se yafi kyau"

Sosai Mufeeda tayi dariya, baze ce tayi kyau ba sedai ya kushe ta.

Ta tura masa
"Mijin baby wani jambaki yafi min kyau?"

"kowanne" ya bata Amsa.

"shikenan gobe idan na saka zaka ce nayi kyau?"

"ba tabbas dan ba wani kyau kike ba idan kin saka, seki koma kaman 'yar ƙauye" ya rubuta yana murmushi.

Emoji É—in haÉ—e rai ta tura masa tare da "nice mummuna ko? Sena gayawa Umma kana cemin mummuna"

"Ke ki kwanta dare yayi fa"

"to My love, you do your task very well today ka kula da Jaririyar ka, nagode sosai Allah ya ƙara Arziki, da naso inyi fushi saboda kasa anmin Allura, amma bazan iya ba nagode sosai da kulawar ka miji nagari, Allah ya barmin kai har ƙarshen rayuwa ta"

"Me a daidaita sahun kike so har ƙarshen rayuwar ki?"

"Ko sana'ar da kake bata kai ta a daidaita sahu ba, ai halal kake nema, kuma ni ba sana'arka ce a gabana ba, kai nake so Ammar É—ina"

Tayi mai voice message kaman me raÉ—a take cewa "I love you my Ammar have a nice dreams"

Shiru Ammar yayi yana jujjuya wayar a hannun sa yana kuma duba chatting É—in sa da Mufeeda.
Murmushi yayi ya kwanta wani daddaÉ—an bacci yayi awon gaba da shi.

(to su Yaya Ammar ko an faller ne🙄🙄🙄)

Ina godiya da ƙauna da kulawar ku.
Ƙofata a buɗe take, domin gyara sharhi, ko kuma shawara nagode sosai 😍 😍 😍
Ayshercool
07063065680
.✨✨✨✨
        *WATA KISSAR...... *
                  ✨✨✨✨✨

                      ( *Sai Mata* )

         

                        

*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*_A SHORT LOVE STORY_*

*Story and written by*

'''AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)
The experience writer of ABDUL JALAL'''

Na sadaukar da wannan littafin ga ÆŠaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba

Watpad @ Ayshercool7724

What's app 07063065680

Gmail [email protected]

     

ELEGANT ONLINE WRITER'S

             

           

                  

                        Page 15

Da Safe Ammar ya fito, se dai Mufeeda bata saka jambakin ba kaman yadda yayi tsammani, haushin kansa ne ya kama shi, komeya na son ganin ta da Jambakin ma oho, haka sama sama ya tambaye ta ya jiki, Sarai ta gane abunda yasa shi haÉ—e rai
Tace

"Jiki da sauƙi Alhamdilillah tunda Mijina yana tare dani"

Ƙin kula ta yayi ya karya abunsa yana wani basarwa.
Da ya gama ya kalle ta yace

"ya kamata ki shiga ku gaisa da maƙwabta, ɗazu mun haɗu da maigidan dake kallon namu, yace min baki shiga kun gaisa da matan su ba, kuma haka ake yi"

"to idan naje me zance musu?"

"nima ban sani ba" ya bata amsa.
"ce musu zanyi nice matar gidan nan, kokuma Jaririyar Yaya Ammar?" shiru ya mata tare da yi mata wata uwar harara.
Mufeeda tace "shikenan zan shiga Insha Allah"
"Sannan kuma ba cewa nayi kuma kidinga shige2 ba da tarkacen Maƙota ba, cewa nayi kawai ku gaisa bana son shige2"
"Shikenan insha Allah zan kiyaye, dama niba me shige shigen bace, saboda bana son takura da sa ido"

Ya gama karyawar sa ya shirya ya fita, yana ƙoƙarin tada babur ɗin sa ya fita da shi ne Mufeeda ta ƙaraso da sauri ta riƙe ƙarfen Babur ɗin, cikin shagwaɓar ta ta tace

"Wai fita zakayi?"

"A'a zama zanyi, in kinji yunwa ki dafani ki cinye"

"idan na dafa ka na cinye na zauna da wa? Wani abu nake son baka ne"
Juyowa yayi yana kallon ta, ba zato ba tsammani ta sumbace shi a kumatun sa na hagu tace

"take a good care of your self My love, Allah ya kiyaye hanya, ya wadata mu da halal" tsayawa yayi yana kallon ta, yayin da ita kuma ta koma gida.

Seda ta kammala aikace2 da zata yi a gidan sannan ta shiga maƙota suka gaisa kaman yadda Ammar ya urmace ta, wasu sun bayyana mamakin su kan cewar itace matar gidan, yayin da wasu kuma suka ɓoye hakan, ita kuwa ko a jikin ta, tai musu sallama ta koma gida.

Ta koma gidan ta babu daɗewa Yaya Usman ya kira ta a waya yace "ke buɗe mana ƙofa muna waje.

Aida gudu ta miƙe ta tafi gate ta buɗe, gurin Baba ta tafi da gudu ta rungume shi, Baba ya shafa kanta yace
"I really miss you Auta na"
Mama tace
"Baban ki kaÉ—ai kika gani ko? Ni baki ganni ba"

Ta É—an tura baki tace "Aini duk fushi nake, tunda aka kawo ni masoyyiya Amina ce kawai tazo gidan nan"

Yaya Usman yace "mu koma kenan?"
Tai murmushi tace "ni bance ba"
Mota biyu suka yi, duk Yayyen ta da yaran su, haka suka zo.

Mufeeda ta rasa inda zata saka ranta dan murna, nan suka shiga shigo da kayan Abinci na garar Mufeeda.

Yaya Fadeela tace "Auta naga kin ƙara haske ko dai an gamu ne?"
Chapter 28 · 0% Book details