← Book details Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 64

Sashe 41

Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ammar kallon tuhuma yakewa Fa'iza amma ya dake yace "Aikuwa ka kyauta bari in kira ta ku gaisa, dan harta kwanta"
Yaje ya taso Mufeeda suka taho tare, suka gaisa Fa'iza se wani mugun kallo take mata, hirar babu gaira babu dalili Faruk yake, gaba É—aya Mufeeda ta tsani Faruk É—in nan musamman irin kallon da yake mata.
Yarinyar da suka zo da itane Jawahir ta fara kuka, tausayin Yarinyar ya kama Mufeeda taje ta haÉ—o mata cornflakes tana bata.
Faruk yace
"Kai Amarya akwai san yara, ina fatan dai kun kusa kiran mu mu É—au Baby"
Yai maganar yana mata wani irin kallo.
Fa'iza tace
"Ai ka tausaya mata tayi ƙanƙanta ace tayi ciki ai"
Wani mugun kallo Ammar yayi wa Fa'iza, Fa'iza tace
"Kinga dan Allah idan da cornflakes É—in nan É—an haÉ—amin dan nima Yunwa nake ji"
"Cornflakes Abincin yara ne, kamar Yadda kika faɗa Mufeeda Yarinya ce saboda ita nake ajiye irin wannan Abincin ba dan baƙi ba, da kunzo da wuri ne da se ko wani abun ta girka muku, Amma tunda kuka kai kamar wannan lokacin nasan kunci Abinci, Sannan Faruk gaskiya banji daɗin yadda ka ɗakko 'yar uwa ta kana yawo da ita a gari a wannan daren ba, raina ya ɓaci gaskiya kuma zanje in samu Mama se naji dalilin da yasa kika fito kika biyo shi a wannan daren, maza ka tashi ka gaggauta maida ita gida na gaya maka"

Fa"iza tace "Yanzu Yaya Ammar bani da Alfarmar da zanci wani abu a gidan ka? Har inzo amma ka koreni"

"Gidanki ne ko gida na? Ko kuma ya dace kizo min gida a irin wannan lokacin"

Faruk yace "Amma Ammar gaskiya.....

"Shut up get out from here please, kekuma zamu gauraya dake"

Haka ta tashi sum suma suka fice

Amin Afuwa abubuwa ne sunmin yawa sosai
Domin gyara, sharhi, ko Shawara
Ayshercool
0706306568
[14/07, 8:19 AM] Ayshercool: ✨✨✨✨
        *WATA KISSAR...... *
                  ✨✨✨✨✨

                      ( *Sai Mata* )

         

                        

*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*_A SHORT LOVE STORY_*

*Story and written by*

'''AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)
The experience writer of ABDUL JALAL'''

Na sadaukar da wannan littafin ga ÆŠaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba

Watpad @ Ayshercool7724

What's app 07063065680

Gmail [email protected]

Please follow me on Wattpad, vote and Comment

https://www.wattpad.com/1096499534?utm_source=android&utm_medium=com.fmwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Ayshercool7724&wp_originator=NWkhlySuZ8Eug%2BopXFfcycv2JGS3axjaccC5%2FbUYT6YzeXAYV4ybw7FnTr8fHQDwo5ncF8TNfQfelSdeR5t0OZi0%2FKAiAcvwuLa561y0j%2BMpxBPI15z3EyzU4ZruY9KP

ELEGANT ONLINE WRITER'S

             

           

                  

                        Page 21

Bayan tafiyar su Faruk gaba É—aya jikin Mufeeda yayi sanyi, ta kalli Ammar zatayi magana, Amma yai sauri yace "kar inji wata magana daga bakin ki, tafi É—akin ki kije ki kwanta" haka tai shiru ta wuce É—akin ta cike da Fargabar kar Fa'iza taje ta kunno mata wata wutar a gurin 'yan uwan Ammar.

Ammar tunani ya dingayi wace irin Alaƙa ce tsakanin Faruk da Fa'iza, da har zesa su dinga yawo a wannan daren su biyu se ƙaramar Yarinya, iyayen Fa' iza suna da tsauri akan tarbiyya amma me zesa abar Fa'iza ta fita a wannan daren? Meye alaƙar ta da Faruk? Da wannan tunanin yai bacci.

Da safe Mufeeda na ta kallon Ammar, tana so ta gaya masa abunda ke faruwa game da halin da take ciki da wanda yake kiran ta, Amma sam Ammar baya walwala ransa a matukar ɓace yake tun zuwan su Faruk jiya da daddare, babu alamar ze tsaya ya saurare ta be kamata ma ta tunkare shi da zancen ba ganin yadda yake cikin ɓacin rai, dan haka bata gaya masa ba ta lallaɓa yai breakfast ya fice.

*****************
Maƙotan Mufeeda' yan layin su suka shirya zasu tafi duba Maman Nur, suka biyo wa Mufeeda wai in zata je.
Mufeeda tace
"dan Allah kuyi haƙuri idan kunje kuyi mata sannu, baya nan ban tambayeshi ba kunga be kamata in fita ba"

Wata maƙociyar su tace  "ke yanzu dan dai dubiya muje yanzu mu dawo shine sekin wani tambayi miji, yanzu fa zamu dawo"

Mufeeda tace "A'a bekamata in fita be sani ba"

Maman Amir ta kwaɓe baki tace "Aikin banza sannu daɗi miji, dama seda nace muku karmu biyo mata, Yarinya 'yar ƙarama se girman kan tsiya da nuna tafi kowa tsoron Allah, tsoron Allah a baki, zuciya baƙi ƙirin"

Mufeeda binsu tayi da kallo suka gama surutan su suka fita suna mita.

Har suka je Asibitin nan Maman Amir Mita take, suka je suka tarar Maman Nur an gama sama ta jini, Jaririn data haifa É—inma yana Nursery Unit saboda bashi da cikakkiyar lafiya.

Suka mata Sannu, Maman Nur tace "wai Maman Amir mitar me kike hakane?"
"Wannan banzar Yarinyar mana, muka biya mata tazo muzo duba ki amma taƙi wai bata tambayi mijin ta ba, 'ya se girman kai kamar wata matar gwamna, Da mijin nata wani shege me a ƙasar nan inaga da seta kore mu daga unguwar"

Wata Yayar Maman Nur me suna Hadiza tace "to ai da gaskiyar ta, ya zata fito bata tambayi mijin ta ba, ai tayi gaskiya"

Maman sadik tace "Anty hauwa bari kawai, ta fiye iyayi ne, ita fa ko ɗam shiga maƙotan nan a Saba da juna ba tayi ga rowar tsiya ta jaraba"

Anty Hauwa tace "Wallahi banga laifin ta ba hakane daidai, ta zauna inda mijin ta ya ajiye ta kuda kuga zaku iya yawo se kuyi tayi"

Maman Amir tace "wallahi Anty hauwa ba wani bin miji, to jiya Sa'idu me kayan miya ne ya gaya wa Baban Amir yace ganin idonsa ya ga tana zance da wannan Alhaji Idris É—in na bayan layin mu da ranar Allah"

Maman Nur tace "ke dan Allah dagaske?"

"Wallahi tallahi dagaske, dan har Baban Amir yace ze tari mijin nata Amma ya fasa"

Nan suka salallami suna ƙara jagwalgwala maganar, Anty hauwa tace  "ban taɓa sanin munafuncin maza ya kai haka ba, kinga ku kiyayi wannan me kayan miyan, kuma wallahi in sharri kukayi mata se Allah ya tambaye ku"

Maman Sadik tace "ba wani sharri, nifa rashin lafiyar Maman Nur ma ina zargin ta, don in baku manta ba ranar da muka kai mata anko se cewa tayi, Ai maman Nur tayi Addu'ar Allah ya sauke ta lafiya yafi wannan ankon da take rabawa, Jama'a kunga Yadda Maman Nur ta ƙare a Asibiti, ta haihu lafiya amma kalli "

Maman Nur ta zare ido tace
"Wallahi hakane maman sadik, na haihu lafiya, Amma naita zubar da jini, nikam kar dai ace mayya ce"

Maman Amir tace "ai cire kamar É—in, itace kawai se kowa ya kula da kansa, bayan bin maza hadda maita"

Nan suka haɗu suka saka gulmar Mufeeda suka dinga zagin ta gami da tsine mata bata san suna yi ba, laifin ta ɗaya taƙi yadda ta zama irin su, mata masu gantali da yawon kwararo kamar ba matan Aure ba, Matan da basu ɗauki sirrin mazajen su a komai ba duk inda suka zauna sesu tone shi.

****************

Mufeeda tana zaune tana karanta Al'qur'ani mai girma, cikin nutsuwa ji tayi ana mata wani irin mahaukacin bugu da seda yasa ta miƙe tsaye a tsorace, kasa matsawa tayi ta tsaya tana rarraba ido dan firgick, gashi dai Yamma ce amma bugun ya tsorata ta, kamar mara gaskiya haka ta fito tsakar gidan ta nufi gate cikin murya me cike da tsoro tace
"Waye?"
"Mune ko ba zaki buɗe ba?" babu ko tantama muryar Jidda ce, buɗe ƙofar tayi bata ko ƙarasa buɗe ƙofar ba Jidda ta danno ƙofar da ƙarfi ta shigo, ita da Fa'iza ne da wasu Yara, wanda 'ya' yan Anty Jidda ne.

Tun daga tsakar gidan ta fara faÉ—a tana masifa,
"Ke har kin isa wani daga dangin mu yazo gidan nan ki hanashi wani abu, ina ɗan uwan mune yake siya ya ajiye, 'yar ƙanƙanuwa dake se rashin mutunci"
Fa' iza tace

"wallahi Anty Jidda idan ba'a ɗau tsatstsauran mataki akan wannan yarinyar ba, wallahi se ta raba shi da kowa, baki ga zagin cin mutunci da yayi min saboda ita ba, akan shege cornflakes aka wulaƙanta ni, ta wani haɗe rai tace gaskiya ya sallameni za ta yi bacci "

" tunda da uban ta aka haÉ—a kuÉ—i aka gina gidan ai dole ta faÉ—i haka mana, ku shiga kowa ya É—au abunda yake so, Ammar ne ya siya"

Mufeeda ta koma gefe ta zubawa sarautar Allah ido, kayan garar Mufeeda da suke ci yasa Ammar yake samun rararar kuɗi, ya ɗanyo siyayyar kayan buƙatu, Amma Fa'iza ta shiga kitchen ta ɗakko ƙaton kwano da cokula, tazo suka dinga zazzage cornflakes ɗin nan suna antaya Madara cike da mugun ta suna ci suna zubarwa, suka gama Fa'iza ta shiga kitchen ta buɗe mata fridge ta ɗebi abunda ranta yake so, suka wulaƙanta mata falo Abinci har kan kujerun ta, Mufeeda tayi tagumi ta zuba musi ido.

Anty Jidda tace "Wallahi duk ranar da wani namu ya kuma zuwa gidan nan kika masa wulaƙanci, ko kika saka Ammar ya wulaƙanta shi sekin koma inda kika fito, Yarinyar banza data wofi kawai"

Tabbas Anty Jidda ta haifi Mufeeda, kuma taci darajar Ya yar mijin ta ce, banda haka ba abunda ze hana Mufeeda ta sawa falo key da mata duka da muciya, sedai Hausawa suka ce Ana barin halak dan kunya.

Tana nan zaune Fa'iza ta shiga kitchen ta dafa Abinci fiye da yadda zasu iya cinyewa, ta ci kowa yaran nan kwano suka ci suka jagwalgwala sauran, 'Yar Anty Jidda Haseena wadda zata shekaru É—aya da Mufeeda ita ce tace
"Amma Anty Fa' iza wannan almubazzaranci ne, Abincin nan yayi yawa, muma idan Abbnmu ya dawo yaga an wulaƙanta masa Abinci Faɗa yake mana"

Fa'iza tace "Rufemin baki ko in make ki, ji gulmamiya, wancan Abbanku ne yake siya wannan kuma uncle É—inki ne ya siya, kici iya cinki ki bar sauran"
Chapter 41 · 0% Book details