Sashe 1
Wata Kissar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
✨✨✨✨
    *WATA KISSAR*
          ✨✨✨✨✨
           ( *Sai Mata* )
    Â
*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞
( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P.W.Aâœï¸
*_A SHORT LOVE STORY_*
*Story and written by*
'''AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)
The experience writer of ABDUL JALAL'''
______Bismillahir rahmanirrahim
Ban rubuta wannan littafi dancin zarafin wani ko wata ba, nayi shine dan ɗebewa masoya na kewa sakamakon hutun da zan tafi da se Allah ya kaimu September zan cigaba da kawo muku littafin AƘIDA TA, Se dai kash farincikin ku shine nawa, zan baku wannan gajeren labari dan ɗebe muku kewa, ina fatan mu amfana da darusan dake ciki
Amma zamu tafi in random direction ne, babu specific lokacin posting, zan Bismillahir rahmanirrahim

Amma zamu tafi in random direction ne, babu specific lokacin posting, zan iyayi a kowane lokaci, bazan samu kawo posting akai akai ba saboda uzurrurikan da suka shamin kai, dan Allah include me in your prayers.
           Â
* a kowane lokaci, bazan samu kawo posting akai akai ba saboda uzurrurikan da suka shamin kai, dan Allah include me in your prayers.
           Â
              Page 1
Tuƙin Babur ɗin a daidaita sahun sa yake cikin nutsuwa da ƙwarewa, yana yi yana duba agogon hannun sa, ga dukkan alamu yana hanzari ne yaje wani guri, kiraye kirayen sallar la'asar da'ake ne yasa shi yin parking ɗin baburin nasa domin bin jam'in salla.
Koda'aka idar da salla, komawa yayi cikin baburin sa ya cigaba da tuƙi.
Wata ƙaramar Unguwa ya nufa, me ɗauke da gidajen talakawa, wani matsakaicin gida ya nufa yaje yayi parking ɗin baburin sa.
Da Sallama ya shiga gidan, amma yanayin sallamar tasa kaman anyi masa dole ya furta.
Wata babbar mace ce da wasu mata guda biyu kewaye da ita suna hira, da gani kasan 'ya' yan tane, saboda kamar da take da su.
Amsa masa Sallamar suka yi gaba É—aya, tare da yi masa Sannu da zuwa.
Ba wadda ya kula a cikin su ya shiga É—akin sa, ya É—au kusan mintuna Ashirin sannan ya fito ya nufi matsakaicin kitchen É—in dake tsakar gidan.
Yana shiga ya fara buÉ—e tukwane, wani uban tsaki yayi ya fito tsakar gida ya kalli inda Mahaifiyarsa da yayyen sa suke yace
"Umma wai ba wani abu se tuwon nan, dan Allah ki dafa min wani abun, ni bana son tuwon nan"
Kallon sa ɗaya daga cikin matan tayi tace "iyeee wai har yanzu Ammar baka dena wannan taɓarar ba? Ayi Abinci amma kai se wanda kake so?"
HaÉ—e rai yayi yace "ina ruwan ki? Gidan ki ne?"
Ɗayar tace "Taɓɗijan nikam Zanga abunda za'a dinga girkawa a gidan ka, ka fiye ƙaƙale Ammar"
Tsaki yayi yace "Umma dan Allah akwai wani Abincin ne?"
Umma tace "Dan Allah kar kuyi min faÉ—a, ba yadda zaku haÉ—u se kunyi rigima, nasan dama ba cin tuwon zakayi ba, duba na dafa maka shinkafa da miya yana É—akina"
Bece komai ba ya nufi É—akin mahaifiyarsu domin ya É—akko Abinci.
"Hmm gaskiya Umma kina sangarta Ammar, Abinci se wanda yaga dama? Har yanzu be dena wannan iyayin ba? Wallahi matar Ammar ta shiga uku, ga masifa da zafin rai, ga jin kai da isa"
"Taɓ lallai Yaya Maryam akace miki zeyi wa matarsa ne? Taɓɗijan ai irin sa in suka shiga hannun mata se yadda akai da shi, baze mata wannan muzuran ba, musamman ya haɗu da yaran zamanin nan masu wankaken ido"
Ammar yana jinsu ya fito ya kalle su yace
"har yanzu ba'a haifi yarinyar da zata juyani ba, ƙare wa ni bazan auri yarinya ba, sena samu wadda aƙa llata kai shekara talatin, dan bazan ɗauki hauka da rawar kai daga kowace yarinya ba, Munafukai kunzo se zigamin uwa kuke, baku da aiki se zarya a gida, wallahi nine mijin ku baku isa ba, bazan yadda da wannan gantalin naku ba"
Yaya Maryam tace
"'yar shekara talatin fa sa' arka kenan? Kana shekara talatin da biyar ka auri 'yar talatin da biyar?"
"eh' yar shekara talatin É—in, wadda tasan meye zaman Aure, ba wannan banzayen yaran masu rawar kai da fitsara ba"
Amina tace "mhmm wai Mune munafukan, Allah ya bamu rai da lafiya, zamu ga matar Ammar, zamu ga irin zaman da za'ayi, 'yar shekara talatin din tayi maganin ka yarinya ba tayi ba"
"Ba' a haife ta ba, macen da zata juya Ammar babu ita"
Yaya Maryam tace "to ina batun Amirar gidan Baffa salmanu, ai kaga ita da girman ta dan zata kai shekara ashirin da biyar, da ko ita seka aura"
"Nine zan auri wannan yarinyar? Banda hauka da yarin ta babu komai akan ta, ko ciwon kanta bata gama sani ba"
"shekara Ashirin da biyar É—in ce bata san ciwon kanta ba?
Umma tace "dan Allah ya isa haka, ku idan kun haÉ—u baku da aiki se faÉ—a, jeka kaci Abincin ka, ni É—azu gidan Malam Lawan sunzo, sunce dan Allah ranar Lahadi zaka kai musu 'yan É—aukar Amarya, ka faÉ—i nawa zasu baka"
Yamutsa fuska yayi "É—aukar Amarya kuma?"
Umma tace "Eh mana, ko ba kaji me nace ba?"
"Bazani ba" ya bata Amsa
"me yasa?"
"Ni bazan É—auki wannan mahaukatan yaran ba, in tafi titi suna hauka da ihu a cikin babur É—ina ba, dan sam hankali be ishi matan unguwar nan ba, daga su har iyayen su, basu da kintsi, duk gayyar ballagazai, bana san shirme ko nawa zasu bani ba zani ba"
Maryam tace "hada mu kenan? Tunda muma 'yan unguwar ne"
Wani mugun kallo yayi mata yai gaba abun sa ba tare da ya bata amsa ba
**********
Tafiya take a sannu uniform ɗin ta na makaranta sun ɗau guga, dukda lokaci ya ƙure kusan tara da rabi na safe, ta makara sosai amma tafiyar ta take cikin nutsuwa.
Tana isa makaranta ta shiga kanta tsaye ba tare da fargabar komai ba ta nufi hanyar Ajin su.
Ji tayi an ƙwala mata kira daga bakin staff room "Mufeeda" tsayawa tayi ta dai daita nutsuwar ta sannan ta juyo ta nufi inda ake kiran ta, yanayin tafiyar ta zaka kalla kasan bata da lafiya.
Discipline Master ne tsaye shida megadi tana zuwa ta zube har ƙasa ta gaishe shi, ya amsa ransa a haɗe ya kalle ta
"ke se yanzu ake zuwa makaranta?"
Cikin sanyin murya tace "Sir am sick that's why I come late"
Ta faɗa tana ɗan yamutsa fuska tareda ƙwalla a idon ta alamar tana jin jiki.
"Meyasa kika zo bayan kin san baki da lafiya"?
"Naji na ɗan samu sauƙi ne shiyasa"
"Shikenan jeki Allah ya sawwake"
"Ameen thank you sir"
Ta miƙe tana juya masa Baya ta kama dariya tareda gwali ta tafi Aji.
Bayan an fita break an dawo, class ya kaure da surutu da hayaniya, prefect ne suka zo sukayi magana a class ɗin akan principal yace ayi shiru yana da baƙi, sannan a rubuta masa noise makers duk wanda sunan sa ya fito a 'yan surutu akwai horo me tsanani .
Hakan yasa ajin yin tsit, dan ko kwakwaran motsi kika fiye yi se a rubuta sunan ki, saboda punishment ɗin principal ba sauƙi.
Mufeeda ta kalli ƙawar ta Fati tace "Kin san meyasa na makara yau?"
Fati ta girgiza kai, Mufeeda tace "Anguwar su Anty murja na biya, naje na samu Yaya Usman me mana ɗinki nan ƙanin mijin ta na sauke masa kwandon bala'i, na gaya masa an jima da yamma zan koma ya bani dinki na kona masa rashin mutunci, dan wulaƙanci biki saura sati ɗaya amma be gama min ɗinki na ba, Anty murja ta hanani kuɗin mota wai tunda nayi wa ƙanin mijinta rashin mutunci ba zata bani kuɗin mota ba, ni ko nai amfani da kuɗin makaranta na, nai taho wata"
"Mufeeda wallahi zan rubuta sunan ki, tun É—azu kike surutu fa" cewar class captain É—in su
Cikin tsiwa mufeeda tace "eh da yake nika É—ai kika raina ba, karki fasa saka sunan nawa"
Aikuwa aka rubuta sunan Mufeeda cikin masu surutu.
"Fati dan Allah bayan la'asar zanzo gidan ku ki raka ni, idan be gama ba koda me yake yawo seya bani kayana"
Seda Mufeeda tayi surutun ta me isar ta sannan ta fara tunanin me zata yi wanda zesa ta ɓata sunayen 'yan surutu da' aka rubuta.
Miƙewa tayi ta tafi gurin zaman class captain ɗin su, tana zuwa ta fizge takardar sunayen,
"Kai lallai wannan sunayen hada san kai a ciki, ku saurara kuji sunayen wanda aka tsana, aka rubuta sunan su"
Nan Mufeeda ta shiga karanto sunayen wanda babu su a cikin takardar, nan da nan aka É—au hayaniya, wanda suka san ba su yi surutu ba suna son jin ba'asin dalilin rubuta sunayen su.
Nan da nan Class ya kaure da hayaniya, class rep na ƙoƙarin kare kanta akan bata rubuta sunan wasu ba, yayin da Mufeeda ta hana ta magana, aka yaga takaddar sunaye, se zage zage da hayaniya sosai.
Ana cikin hayaniyar ne head girl ta leƙo ajin tace "SS2 on your knees under the sun inji PC"
Nan suka fara salallami, wanda basu jiba basu gani ba suna Allah ya isa.
Dama sun saba shan punishment, saboda tsabar rashin jin 'yan ajin.