← Book details Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 134

Sashe 95

Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A gurin su ne ta kuma tabbatar da labarin mutuwar Hussain. Ita kuma tana kuka tana basu labarin mutuwar Fatima "tunda na tashi dama na fahimci cewa ta mutu, nayi nayi kokarin in fito da gawarsu daga cikin motar ita da driver amma na kasa, ga wuta kuma ta kama" sai ta rufe fuskarta tana rusa kuka Sumayya tana taya ta. Tace "wuta ta kone su kurmus. Ance ma ba za'a iya dauko gawawwakin su ba sai dai a binne su a can" Sumayya ta share hawayen ta tana tuno kyakykyawar fuskar Fatima, sai kuma ta kara karfin kukanta data tuno da tsohon cikin da Fatima take dauke dashi. Dai kuma Hussain, ta tuno ganinta dashi na karshe sanda taje gidan ta hadu dashi. Cikin barkwanci irin nasa yace "Sumayya kin kuwa san gimbiya ta tsohon ciki ne da ita?" Tayi dariya Tace "na sani mana, na shiga ai mun gaisa" yace "to ki je gida ki fasa bankin ki ki tattara kudaden ki ki sayi lace dan yayi ki kai wa tailor yayi miki dinkin zamani dan suna ne za'a yi shi irin wanda ba'a taba yin irinsa a garin kaduna" sukayi dariya gaba daya. Yanzu gashi babu shi babu matar babu dan. Duniya labari, duniya zancen banza, duk wanda ya dauke ta gurin zama tabbas yana tare da babbar nadama.

Baba ne yace da Inna Ade tazo su tafi gidan mutuwar, Sumayya kuma da Sulaiman su zauna a gurin yar uwarsu a asibiti gobe sa je suyi musu gaisuwa. A gidan mutuwar ne suka tarar da abin mamaki, layin gabadaya a cike yake da mutane maza da mata daga lunguna da sakuna na garin kaduna, wasu a zazzaune wasu a tsatstsaye kowa yana addu'ar samun rahama ga Hussain da iyalinsa saboda Hussain yana da wata al'ada ta kyautata wa duk wanda ya hadu dashi dan yana cewa

"ita haduwa kaddara ce, rabuwa dole ce. Duk mutumin da ka hadu dashi a rayuwa to kayi amfani da wannan damar wajen kyautata masa dan babu tabbas din zaku kuma haduwa, ko baka bashi komai ba kayi masa magana mai dadi, ko baka yi masa magana mai dadi ba kayi masa murmushi dan shima sadaka ne"

Cikin gidan kuwa da Inna ta shiga dakunan duk a bude suke kuma duk da mutane a ciki duk kuwa da cewa yan Gombe basu karaso ba, kowa kuka, musamman ma'aikatan gidan da suke ganin ba zasu kuma samun wani uban gidan kamar Hussain Aminu Abdullahi ba.

Labarin Mutuwar Fatima ya dira tamkar kibiya a zuciyoyin iyayenta, yanuwanta da masoyansa ta. Nan take masarautar kano ta hargitse kowa kukan rashin Fatima musamman da suka ji irin mutiwar da ake tunanin tayi. Wai ko gawar ta ba zasu gani ba, wai ko sun gani din ma ba zasu gane taba saboda ta zama gawayi. Fatimah dai ta su, Fatima da suke ji da Ita tamkar kwai ita ce ta mutu kuma wuta ta kone ta. Wannan wanne irin tashin hankali ne?

Mai martaba sarki duk da cewa ya dimauce ya gigice da alhinin mutuwar yar tasa amma duk da haka sai ya hada kan ya'yansa maza gabaki daya suka hau jirgi a daren suka tafi Abuja. Da assuba suka yiwa gawar da suke tunanin ta yar uwar su ce sutura tare da ta driver aka yi musu sallah sannan aka binne su a gurin da suka mutu. Daga nan kuma sai ya juyo ya koma kano dan fara karbar taaziyya daga mutanensa, yayan sa kuma ya tura su Kaduna dan su halarci jana'izar Hussain wadda aka daka karfe goma sha daya na safiyar asabar.

Abinda yake bawa kowa mamaki a gidan gaisuwar shine Hassan. Da kansa yayi wa gawar Hussain wanka ya kuma suturta ta tare da taimakon limamin gidan tun cikin dare. Kallonsa kadai idan kayi ya isa abin tausayi amma zuciyarsa tana tsaye. Yana zaune a gaban gawar yana yi masa addu'a kamar yadda cikin gidan da wajen gidan yake cike da mutane da suke masa addu'a har gari ya waye. A lokacin yan Gombe suka karaso, dangin maman su da dangin babansu. Da gari ya waye ne Hassan ya kira Aunty, wadda duk ta gama fita daga hayyacinta, tare da dukkan yan uwansu mata su biyar yace su zo suyi sallama da Hussain. Kuka suke suna karawa, haka yahada su ya rungume duk a jikinsa in ya share hawayen wannan sai ya share na wannan yana cewa "ku daina masa kuka kuyi masa addu'a, ku ringa cewa innalillahi wa inna ilaihir rajiun zaku ji sanyi a zuciyoyin ku" sai daya kaisu sannan ya dawo ya kama Aunty da kyar ya daga ta ya tafi daita itama. Suka zagaye gawar Hussain suna ta karanta masa suratul ikhlas suna maimaita wa, yadda suke kallon Hussain a kwance a cikin likkafanin sa duk sai sukaji duniyar gaba ki daya ta fita a kansu, suna tuno da sutturu irin na Hussain wanda baya saka kaya idan ba na zamani ba, komai nasa latest ne, in kuwa akayi wani design din to ya daina saka wancan design din. Amma yanzu gashi da brand din kaya irin wanda ake sakawa tun dubunnan shekaru da suka wuce, babu safa ballantana takalmi, babu agogo da sauran kayan adon maza, sai dai in suka kalli fuskarsa sai suji dadi a ransu, yayi kyau irin wanda bai taba yi ba koda kuwa yayi ado da kwalliyar. A hankali suka daina kuka suka cigaba dayi masa addu'a tare da sallamar bankwana, ban kwana na har abada, ban kwana na sai a lahira kuma ba dai a duniya ba dan haduwarsu a duniya ta kare. Sai dai ko bayan sun daina kukan ma in suka tuna da Fatima sai su sake wani, a lokacin babu abinda ba zasu bayar babko da kuwa kawunan sune, babu abinda ba zasu iya yi ba idan za'a dawo musu da Fatima da abinda yake cikinta. Musamman Khadijah wadda tun zuwan Fatima gidan ita ce suka fi shakuwa akan duk sauran, kullum suna tare, tasan irin son da Fatima da Hussain suke yiwa cikin Fatima ta kuma san irin shirin da suke yi na taryar sa, ashe ba mai rayuwa bane ba, ashe ko numfashi bashi da rabon shaka a duniya.

Auncle din su ma da aunties dinsu duk sun shigo sunyi sallama da Hussain, yaron da yayi achieving abinda mutum goma in aka hada ba zasu iya achieving ba. Shi mutum daya ne tamkar dubu. Mutum ne da su kansu sunsan za'a jima a dangi ba'a samu irinsa ba a arziki, alkhairi, kyautata wa da kuma yawan jama'a. Mutuwar Fatima itama ta daga musu hankali ba kadan ba, dan da tana nan da suna saka ran zata haifar musu abinda zasu ke gani suna tunawa da Hussain.

Abokan Hussain, abokan business dinsa da sauran abokan muamalar sa duk sunzo jana'izar sa, a ciki har da Sadiq wanda mutuwa ta riski Hussain a hanyar sada zumunci tsakanin su. Ya koka sosai da mutuwar abokin nasa kuma ya jinjinawa karfin hali irin na Hassan. "Ban san bashi da lafiya ba, bai taba gayamin bashi da lafiya ba. And his family, ohhh dear God. Fatima and His baby! Kullum sai sai ya bani labarin Fatima ta kusa haihuwa. Wannan mutuwar mutuwa ce da ba zamu taba mantawa da ita ba".

Karfe goma da rabi aka fito da gawar Hussain daga cikin gida, abinda ya saka yanuwansa suka kara rikicewa, Khadijah da Hassana suka zube a kasa. Sha daya dai dai aka yi masa sallah a cikin compound din gidan Aunty, amma mutane sun rufe gabaki daya titin unguwar har da bayan layin da cikin gidajen mutane, kowa yana so ya halarci zanazar Hussain saboda ya taba rayuwarsa in positive way. Dama shi alkhairi haka yake, in ka shuka shi to kuwa zai bika ne tun a duniya kafin ka je lahira, shima kuma sharri haka yake, babu yadda za'a yi ka shuka dawa ka kuma girbi shinkafa.

Hassan da hannunsa tare da taimakon Jabir mijin Safiyya, Saeed mijin Hassana, uncle Mustapha kanin Alhaji Aminu da Baba Amadu yayan su aunty suka saka Hussain a cikin kabarinsa akan barin sa na dama sannan fuskarsa tana kallon gabas, sai kuma aka jejjera itatuwa a saman gawar tasa aka kuma bi da kwababbiyar kasa aka lullube itatuwan tare da like duk gurin da yake da kofa. Sannan aka mayar da kasar da aka fito da ita daga gurin sai kuma aka yayyafa ruwa a saman kasar.

Sai aka durkusa kuma aka yi doguwar addu'a ga ruhin Hussain, masu kuka a hankali nayi nasu dauriyar zuciya nayi har aka shafa sai kowa ya fara kama gabansa. Hassan yana tsugune, tunda ya saka Hussain a cikin ramin ya koma gefe ya tsuguna yake kallonsa har aka rufe shi da itace ta daina ganin sa amma bai dauke idonsa daga inda yake ba, yana kallo aka gama komai aka kuma yi addu'a, ya daga hannunsa, duk da cewa kunnuwan sa basa fahimtar me ake cewa amma yasan addu'a ce akeyi ga Hussain. Yana kallo aka shafa shima ya shafa. Sai kuma yaga mutane sun fara tashi suna tafiya, na kusa dashi kowa in zai tafi sai yazo ya dan dafa shi alamar bada hakuri sannan ya wuce, a haka , a hankali a hankali har kowa ya watse, har aka barshi shi kadai tare da kabarin Hussain.

A hankali yace "Hussain. Amanar da ka bar min ta danka ban sami damar rike ta ba saboda shima ya biyo ka, shi da Fatima, ina fatan zai zamo mai ceto a gare ku damu baki daya" sai ya mike tare da daga kansa ya kalli dogon gidan Hussain wanda tun daga nesa ake hango shi saboda girmansa da kuma kyawunsa, sannan ya sunkuyar da kansa ya kalli kabarin Hussain. Lallai wannan ma wani darasi ne da mutum mai hankali ne kadai zai iya ganewa.
Chapter 95 · 0% Book details