← Book details Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 134

Sashe 2

Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amina a lokacin tana da shekaru goma sha biyar. Dan haka suna zuwa Kaduna aka saka ta a makaranta dan ta cigaba da karatunta, kuma yayarta da Alhaji Aminu suka rike ta sosai. Shekara biyu da auren Alhaji Aminu da Hassana sai Allah ya bata ciki, ciki mai cike da tarin laulayi tare da tarin girma. Inda tun a awon farko aka tabbatar wa Hassana da cewa tana dauke da tagwaye. Hakan ya saka su cikin matsanancin farin ciki duk kuwa da cewa dama suna saka ran hakan saboda kasancewar Hassana tana da abokiyar tagwaitaka ya saka chances dinta na haihuwar tagwaye ya zama yana da yawa.

Ganin wahalar da cikin yake bata ya saka mahaifanta suka nemi su tafi da ita gida ta haihu a can amma son da Aminu yake yi mata ita da cikin yasa ya kasa barinsu su tafi ya nemi a bar masa matarsa shi zai ke kula da ita da kansa. Aka bar masa ita, ya kula da ita tamkar sabon kwai, har lokacin haihuwar ta yayi.

Da farko sanda ta fara nakuda likitoci sun dauka zata iya haihuwa da kanta, sai data yi awanni babu wani progress sannan aka fara shawarar yi mata aiki dan gudun samun matsala. Sai da aka gama shirya ta tsaf sannan kuma sai jini ya balle mata, a haka akayi mata cs aka fitar da tagwayen maza, masu kama daya, sai dai daya ya dauko fatar babansa "baƙi" dayan kuma yayo fatar Hassana "fari".

Bayan an dawo da ita dakin hutawa ne ta farfado aka saka mata jariran a hannayenta biyu, Hassan a hannun dama, Hussain a hannun hagu. Ta rungume su a jikinta, a haka Allah ya dauki ranta. Fadar bakin cikin Aminu tamkar bata lokaci ne, dan mutane har sun fara tunanin ko zai bita ne, amma sai soyayyar yayansa ta danne bakin cikin rashin matarsa.

Da farko anyi niyyar karbar yaran daga hannunsa a tafi dasu Gombe gurin kakannin su amma Aminu yace sam babu mai raba shi da yaransa. Wannan yasa bayan dan gajeren zama tsakanin iyayensa dana Hassana aka yanke shawarar aura masa Amina. A gurin aka biya sadakin aka kuma daura auren. Bayan dan karamin biki a Gombe aka dawo da amarya kaduna gidan mijinta tare da tagwayen ƴaƴan ta.

Da farko Amina ta dauki auren ta tamkar wasan yara dan ita babu komai tsakanin ta da Alhaji Aminu bayan mutunta juna, ganinsa take tamkar yayanta da suka fito ciki daya. Abinda yake gabanta kawai shine karatunta da kuma marayun da aka bar mata wadanda ta dauki son duniya ta dora akan su, dan har ba'a iya banbance wanda yafi son yayan a tsakanin ta da Alhaji Aminu wanda kullum a jikinsa suke bacci.

An samo mata matar da zata ke tayata kula da yaran saboda lura da karancin shekarun ta da kuma makarantar da take zuwa, amma fa tana dawowa zata karbo yayanta. Ranar nan bayan ta dawo daga school ta samu mai renon tace "Baba Yaha Dan Allah ko kinsan maganin da za'a sha ruwan nono ya zo?" Baba Yaha ta kalle ta da mamaki tace "me zaki yi da ruwan nono Amina?" Tace "a makaranta an gaya mana irin amfanin nonon uwa agurin jarirai, yaran nan nake tausayi, su basu samu wannan alfanun ba tunda kinga madara suke sha. Shine nake so in samu magani insha sai inke basu nawa" baba Yaha ta jinjina irin soyayyar da Amina take yiwa yaran sannan tace "to wannan dai ba magana ta bace ba, kije ki samu mijinki kuyi shawara a tsakanin ku, in ya amince shikenan sai in samo miki, amma in bai yarda ba dole ki hakura. Dan haka sai ki lallaba shi".

Da wannan Yaha ta kashe maganar, dan a lokacin babu yadda za'a yi Amina ta samu Alhaji Aminu da magana makamanciyar wannan saboda sam basa irin wannan da shi, ko wasa ma basa yi saboda shi ba mutum ne mai son wasa ba.

Amma tsakanin mata da miji hausawa suka ce sai Allah. Tagwayen suna da shekara biyar a duniya sai ga Amina da ciki. Ai kuwa ranar da tagwayen suka fara lura da cikin a jikinta suka sakataa gaba da jerin tambayoyi har sai da ta gaya musu cewa baby ne a cikin, baby zata haifa musu watarana. Nan suka fara tsalle a saman gadonta suna adungure zuwa kasa. Alhassan yace "Please, Please aunty ki haifa mana namiji dan muke wasa tare" Alhussain yature shi yace "me za'ayi da namiji, anyi ta haihuwar mazan kenan? Mace zata haifa mana shikenan na samu budurwa" nan sai fada, harda kokawa, sai da kyar ta raba bayan sun gama doddoke ta. Sannan ta zauna tana dariyar sokonci irin na Hussain, ko ta yaya yar da zata haifa zata zama budurwar shi?

Haka yake shi Hussain, akwai surutu, akwai fitina, akwai karambani kuma akwai kokari a makaranta. Shi kuma Hassan shine mai wayo, manyance, da zarar magana. In yayi wani abin zata ce yafi karfin shekarunsa, komai sai ya nuna kamar ma ya fika iyawa kuma ba wai iyawar yayi ba. Komai na shi careful yake yinsa, in dai taga anyi barna to tasan Hussain ne, shi ko abinci kika bashi daga kitchen ya kawo daki to sai ya zubar a hanya.

Hussain ne yayi nasarar wannan musun nasu. Dan mace ta haifa wadda aka mayar mata da sunan Hassana kuma ake ce mata Hassana ɗin. Daga ita kuma sai ta haifi Safiyya, Khadijah, Nafisa, sannan Zulaihat. Duk kusan a jejjere tayi su. Daga nan kuma sai ta dakata tukuna tace sai sun girma zata sake wani set din.

Amma Allah baya barin wani dan wani yaji dadi.

A shekarar da tagwayen suka gama secondary school dinsu a shekarar ne Allah yayi wa Alhaji Aminu rasuwa bayan yar gajeriyar jinya. Ya mutu ya bar mata daya da yaya bakwai. Maza biyu mata biyar.

Wannan mutuwa ta taba ba wai family dinsa ba har wadanda suka sanshi da sauran abokan aikinsa kowa sai da ya koka kuma ya tausayawa iyalinsa, kasancewar su kanana babu wanda za'a ce ya rike kansa ballantana ya rike yan uwansa, ita kanta uwar ba wasu shekarun kirki ne da ita ba.

Bayan anyi arba'in sai yan'uwa suka nemi su koma Gombe su zauna a cikin dangi. Hussain ya shafawa fuskarsa toka ya ce babu inda zasu je "yanzu yaran nan sai a cire su daga makarantun su kenan? So kuke yi mu koma can a fara yi mana dauki dai dai? Wannan uncle din ya dauki uku wancan ya dauki biyu wannan auntyn ta dauki daya?"

Aunty Amina ta share hawayenta, dama Hussain shi take tunani, tasan shi da rigima, tasan shi zai bata problem, tace "to Hussain ya kake so muyi? Eh? Ya kake so inyi da raina? In bamu koma Gombe ba ina zamu je? Wa zai rike mu? Ni dai kasan ba zan iya ba, kasan ba aiki nake yi ba ba sana'a nake yi ba, kasan kuma ba dogon karatu nayi ba ballantana in saka ran zan samu aikin da zan rike ku dashi. Ku kuma baku kawo karfi ba tukunna, kuma mai taimaka muku kuke bukata a yanzu, kuna bukatar wanda zai shige muku gaba ku cigaba da karatun ku. Yan uwanku yaya zakuyi dasu? Duk fa primary suke Hassana ce kawai take ajin farko a secondary. Hussain dole muna bukatar taimako, ba kuma zamu samu taimakon nan anan ba sai mun koma cikin yanuwanmu".

Ya mike tsaye yana girgiza kai yace "duk wanda yake bukatar taimaka mana a cikin yanuwanmu ai zai iya taimaka mana muna zaune anan. Kuma ma ai bama bukatar taimakon kowa aunty. Mu, ni da Hassan zamu rike kan mu zamu rike ku" Hassan ya mike yana kallon sa yace "ta yaya? Ta yaya zamu rike kan mu Hussain? Gaya min me muke dashi? Ko da karambani zamu rike kan namu? Ana maganar reality ne fa anan, ana maganar future din mu ne data yaran nan kannen mu" Hussain yace "in ba zaka iya ba kawai kace ba zaka iya ba ba sai kayi min dogon sharhi ba" ya wuce shi ya dawo gaban Amina. "Aunty ki yarda dani dan Allah. Wallahi zan iya" tayi ajjiyar zuciya tace "zaka iya? Ta yaya?" Ya zauna a kan kafafuwansa yace "kasuwanci zan shiga, ba da akwai kudade a hannun mu ba? da akwai wasu a bank? Ga kuma motoci har guda uku a waje? Kuma ga filayen da Abba ya siya ya ajiye? Mu siyar dasu ku bani kudin in shiga business dasu.........."

Hassan ya dawo kusa da Aunty da sauri yace "hauka ma kenan. Yanzu in business din zamuyi Hussain sai mu dauki dukiya mu baka? Kai din? In ka lalata ta kuma shikenan sai mu dawo mu zuba tagumi? Gaba ake dubawa Hussain. Komai a hankali a kuma nutse ake binsa, kullum sai na gaya maka wannan amma kai baka ji"

Hussain yayi masa kallo daya ya dawo da dubansa kan Aunty yace "Please Aunty, ki bani wannan damar dan Allah. Wallahi zan iya, ki rabu da Hassan. Shi yana living ne in the future ni kuma ina living now, in dama tazo wa mutum kawai yayi amfani da ita ba sai ya jira wata damar tazo sanda yayi masa dai dai ba.

Yanzu ne damar mu Aunty, ki bani wannan damar dan Allah.

Aunty ta jima tana kallon sa, tasan halinsa sarai, tasan karambanin sa da daukan abinda yafi karfinsa ya dora wa kansa, tasan kuma kokarin sa dan duk sanda ya fadi baya zama a kasa yayi kuka mikewa yake yi ya cigaba da tafiya. Duk abinda yake bashi wahala kuma sai yayi ta maimaita wa har sai ya iya.
Chapter 2 · 0% Book details