← Book details Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 134

Sashe 39

Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suka shiga kitchen Sumayya tana ta santin kitchen din da duk kayan da suke ciki, sannan suka fita waje ta kofar baya Sumayya tana yaba shuke shuken da akayi a surrounding area din, flowers masu kyau da kamshi aka zagaye backyard din gidan dasu, gidan Hassan mai kyau ne, mai matukar kyau ne, sai dai ace masa karami, kankantar ma za'a fada ne in akayi comparing da gidan Hussain. Amma sai Ruqayyah ta daga kanta kana kallon gidan Hussain, ita so take ta shiga ciki taga menene a cikin wannan katoton gidan, tasan anyi wa gimbiya jere so take taga dame dame aka saka mata, so take taga sun kai nata kyau ko kuma sunfi nata? Sumayya ta kama hannun ta suka koma, tanata yi mata hirar yadda mutane suka yi ta santin gidan har suka koma dakin ta sannan Sumayya ta cire kayanta ta shiga bandaki zata yi wanka. Kayan bandakin ma sai data yi ta gwadawa kafin ta iya gane yadda zata yi amfani dasu. Bayan ta shiga toilet din ne sai Ruqayyah taga kofa a tsakanin windows, ta saka hannu ta bude ta shiga. Nan take taji farin ciki ya kamata "a balcony!" Madaidaicin balcony ne mai kyau da tsari, railers din sa kawai abin kallo ne ga set din kujerun hutawa da dan karamin teburin su. Ta zauna akan kujera daya tana murmushi, sai ta juya da niyyar ganin gari, da niyyar ganin Kaduna a kasan ta amma sai taga gidan Hussain yayi bakevake ya tare mata hanya. Ta daga kanta tana hango karshen gidan sai taga balcony a can karshe, meaning idan matar Hussain ta fito ita ma ta fito to matar Hussain zata ke hango ta a kasanta. Taji zuciyarta ta buga, ranta ya baci, hankalin ta ya tashi. Ita gidan Hussain take so, wancan balcony na sama shi take so ba wannan ba. Ta mike da sauri ta shige ciki ta rufe kofar ta murda key sannan tazo ta wuce Sumayya da take ta santin closet din data bude duk da babu kaya a cikin ta, ta shiga toilet, ta jefa key din a toilet tayi flushing dinsa.

Suna gama wanka Aunty ta sake aikowa tace su tafi can main house din suyi breakfast, suka shirya sama sama sannan suka fita tare da yar aiken data ce musu ita cousin din su Hassan ce. "Mamana ita ce Hussainar Maman su yaya H1" ta fada proudly, kawai sai Ruqayyah taji yarinyar bata yi mata ba duk kuwa da cewa bata yi mata komai ba. Sumayya tace "hmmm. Lallai kice akwai twins da yawa a wannan family din" ai kuwa kamar ta tsokano Magana sai ta fara lissafa mata su, gidan Aunty wance gidan gwoggo wance gidan auncle wane, Sumayya tace "haka kuke da yawa ashe? Lallai Ruqayyah kina da aiki a gaban ki. Duk sai kinyi kokari kin gane su saboda gaba" yarinyar tace "au wai ba ke ce yayar tamu ba? Ni fa ba gane ku nake yi ba" Ruqayyah tace "in dai kika yi magana kika ji an cika miki kunne da surutu to ba ni bace ba" Sumayya tace "in dai kika yi magana kika ji an baki amsa gida daya an dauke kai to ita ce yayar taki" duk sukayi dariya. Suka wuce ta gaban gidan Hussain sannan suka shiga wani dan karamin gate da akayi a tsakanin gidajen guda niyu yadda ba sai an zagaya ta babban gate ba, suka shiga main gidan su Hassan, inda Aunty take.

Suna shiga suka tarar gidan a cike da yan uwa, ana ta hayaniya. Nan da nan aka fara drama din banbance Ruqayyah da Sumayya, a karshe har sai da aka kira Hassan a waya aka ce ya fadi bambanci guda biyar. Nan ya fara jero musu "nutsuwa, kunya......" Suka katse shi, physical banbanci muke so kafada mana ba abstract ba" yayi dariya yace "let me close my eyes and think. Kunga na farko fuskar Ruqayyah tafi ta Sumayya tsaho, idanuwan Ruqayyah kwantattu ne na Sumayya kuma zagayayyu ne, lips dinsu ma ba iri daya bane, na Ruqayyah sunfi siranta na Sumayya sunfi kauri. Sannan Sumayya ta danfi Ruqayyah kiba kadanita kuma Ruqayyah tadan fi ta tsaho kadan. Hassana ta bata da yawan magana sosai, tana dai da yawan murmushi, Sumayya kuma tana dariya as much as she talks".

Duk mutanen gurin suka kwashe da dariya. "Wallahi to kowa ya jika a gurin nan har su Aunty" ya kashe wayar yana dariya. Kowa a gurin jan su yake a jiki, ana ta nan nan dasu, aunty tayi wa Sumayya godiya data zauna a tare da Ruqayyah. "In kina nan zata fi sakin jikin ta, tunda ita ba mai magana ba ce ba sosai"

Suka yi breakfast tare da family ga baki daya, sannan aka fara shirye shiryen tafiya, aka kai su Ruqayyah dakin yaya Hassana akace su shirya a can. Suna ta tunanin wadanna kayan zasu saka, su a niyyar si na jikinsu da shi zasu tafi dan a cikin sababbin kayansu suka dauko, amma sai sukaji ance suje su canja kaya su shirya. Ma'ana na jikin nasu basu yi ba. Suna cikin tunani sai ga kaya an kawo wa Ruqayyah, iri daya Aunty tayi musu ita da Hassana tunda sune amare, Ruqayyah ta saka doguwar rigar jan lace din mai kwalli tana kallon kanta a mudubi, tana noticing yadda shape din jikinta mai kyau ya fito sosai a jikin rigar, ashe duk tailors din da suke yi mata dinki bata mata kaya suke yi?

Ita kanta tasan tayi kyau sosai duk da bata yi kwalliya ba, amma kuma sai taji a ranta tana tunanin ko gimbiya fatima zata fita kyau? Ta dai ga tana da kyan fuska a hoto, ko tana da kyan jiki irin nata? Sai kuma taji tana fatan ya kasance bata da shi din da at least ya kasance ta fita da wani abu. "Ai babu wanda yake perfect" ta gaya wa kanta. Bayan ta gama shiryawa ne sai akace tazo ayi mata kwalliya, mai kwalliya ce aka dauko ta Musamman zata yiwa amare sannan da wata wadda zata yi wa sauran mutane duk mai so. Aka yiwa Hassana sannan aka yiwa Ruqayyah aka daura mata head, Ruqayyah ita kanta data kalli kanta a madubi bata gane kanta ba. "Dama haka take da kyau amma tsumma ya boye mata shi?" Tayi murmushi, tabbas tasan tafi gimbiya Fatima kyau.

Sumayya ma taje aka gyara mata tata fuskar akayi mata simple makeup, tayi kyawunta ita ma sosai da sosai. Ana ta hidimar shiryawa sai ga angwaye sun shigo tare da abokan su, suka je gurin su Aunty suka gaishe su aka yi ta saka musu albarka sannan akayi hotuna, Aunty ta aika aka kirawo su Ruqayyah, Ruqayyah ta taho idonta a kasa hannunta rike da jakarta, tana takawa a hankali yadda duk hankalin mutanen gurin ya dawo kanta. Hassan ya juyo ya kalle tavsai ya dauke kai, sai kuma ya sake juyowa da sauri yana kallon ta, wai Hassanar sa ce wannan, jinyake kamar ya rashi yaje gurinta ya gaya mata irin kyawun da tayi a idonsa amma yana jin nauyin iyayensa da suke gurin, sai ya bo ta da idanu kawai, a ransa yana jin dadin mayafin data saka ta rage bayyanar surarta. Nan akayi ta jera su ana daukan hotuna dasu, iyaye kowa ya shigo ayi dashi haka kanne ma da sauran yan'uwa. Anan Ruqayyah taga Hussain. Kaya iri daya suka saka shi da Hassan amma sai taga kamar tasa shaddar tafi haske ta Hassan tayi duhu, ko dan hasken fatarsa ne? Ko kuma a idonta ne taga hakan. Fuskarsa cike da annuri, idanunsa suna haske, dimple dinsa yaki komawa saboda murmushin da yaki daukewa daga fuskarsa. Kowa a gurin in ya gaishe shi sai ya ambaci sunansa kuma ya tambaye shi a game da wani abu daya shafe shi, ma'ana yasan kowa kenan, yasan affairs din kowa, kuma sai taga kamar yan uwan sunfi tafiya inda Hussain yake akan inda Hassan yake, ko ita ce take ganin haka?

Sai da aka shigo aka tuna musu da cewa lokaci fa yana tafiya sannan suka bar hotunan haka. Sai a lokacin Hassan ya samu magana da Ruqayyah. Yana kallon fuskarta yace "kinyi kyau sosai matata" tayi murmushi tace "kaima kayi kyau mijina" ya danyi gajeriyar dariya yace "maimaita in kara ji" ta saka hannu ta rufe fuskarta tare da dan juya bayanta kadan. Yayi dariya "zanji ne ai, one way or another. Kinsan wani abu?" Ta bude fuskar tana girgiza kai, yace "ji nake kamar in fasa zama in biku kanon nan" ta ji ranta ya fara baci "zaka bi mu kuma? Kai fa kace hutawa zaka yi" yace "yadda naga kwalliyar nan anya zan iya zama in sake kwana ina rungumar pillow" ta sake juya masa baya "kai dan Allah!" Sai kuma ta juyo tace "In ka bimu ma fa ba tare zamu zauna ba, ku kuma waje ko kuma kuna hotel mu muna cikin gida. Ni nafi si kayi zamanka anan kar kabi Hussain da abokansa su zo suyi ta wahalar da kai" yana murmushin gefen baki yace "really?" Tace "eh mana. Kaga gobe daurin aure biyu ne daku ga dinner da dare. You rest today" ya daga murya yana kiran Hussain "ka ga inda aka damu dani ake so in huta, kai kana mitar nace ba zan je ba ita tana cewa inyi zamana in huta" Hussain ya juyi yana kallon su sannan yace "soyayyar da muke yi maka ce daban daban, ni nafi sonka by my side through thick and thin, ita kuma ta fi son ta sha wahala ita kadai kai kuma ka huta" ya dauke kansa, Hassan yayi dariya yana ce mata "fushi yake yi wai nace ba zan je ba. I think zan je ɗin kawai, kar ransa ya kara baci" tayi shiru tana hararar bayan Hussain a fakaice, shine zai zamanto obstacle dinta kamar yadda gidan sa ta toshe mata ganin ta. Ya kuma tsaya mata a zuciyarta.
Chapter 39 · 0% Book details