← Book details Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 134

Sashe 74

Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun Ruqayyah tana zuba idon ganin saukowar Hussain har ta hakura ta hau saman, ta ga kofar dakin a rufe tasan kuma suna ciki, tayi tsaki ta shiga nata dakin, sai data yiwa twins dinta wanka ta shiryasu sannan ta fito dasu falo, still tana tunanin menene suke ta magana haka a cikin daki. Ta kira mai renon twins ta bata su tace su tafi gidan Aunty duk da tasan cewa basu gaisa da baban su ba ballantana uncle din su daya shigo, sai dai kuma ita bacci take so ta koma.

Suna tafiya Hassan ta bude kofa suka fito shida Hussain, fuskar Hassan kadai ta saka taji gaban ta ya fadi. Ya dan kalle ta yace "zamu fita, sai mun dawo" ta dan bata fuska "abinci fa? Ba ka karya ba fa" ya wuce ta yana cewa "ki ajiye min, inna dawo zan ci" shi a ransa ya ma manta da wani abu wai shi abinci. Hussain yace "sorry Madam. Na dauke miki miji ko? Aro na dauka zan dawo miki dashi in one piece". Ta bi si da kallo har suka fita a ranta tana tunanin something is up, kuma koma menene it is not good.

A ranar suka gama binciken oncologist din daya kamata Hussain ya gani, a India yake, a ranar kuma suka fara kokarin booking yadda zasu ganshi.

Ruqayyah tana zaune a palo suka kuma shigowa tare shida Hussain, gaisuwar ta kawai Hassan ya amsa ya wuce daki, Hussain ne ya dan tsaya yayi wa twins wasa sannan yabi bayan Hassan din suka shige dakin sa. Ruqayyah ta saki baki tana kallon wani sabon salo wai kiran sallah da usur sai kuma taga Hussain ya fito shi kadai yayi mata sallama ya fita.

Bata bi ta kan Hassan ba sai data gama duk abinda zata yi ta kwantar da babies dinta tayi wanka tana shirin kwanciya sannan dai tace bara ta leka shi. A kwance ta tarar da shi ya lullube har kansa kuma ya kashe acn dakin. Ta zauna a bakin gado tana dan bude shi kadan sai dai tiririn da taji yana taso wa daga jikin sa kadai ya sa ta fahimci cewa bashi da lafiya

"subhanallah. Ai zazzabi ne a jikin ka mijina" ya bude ido sa yana kallon ta, tayi kokarin daga shi "ka tashi ka sha magani, ko in kira Hussain ya kaika asibiti?" Sai ya kama hannun ta ya rike "Hussain? Bana son komai ya samu Hussain" daga yadda yayi maganar ta san magagin zazzaɓi yake yi, tace "babu abinda zai samu Hussain kuma kai ma babu abinda zai same ka, zazzaɓi ne kawai kake yi" tayi kokarin tashi sai ya jawo ta jikinsa yana cewa "babu abinda zai same shi? Thank you, ohhh thank you" ya fada yana shigar da ita cikin bargon sa tare da lullube su tare.

Washegari Ruqayyah ta tashi da murnar Hassan ya fara saukowa, a ranar ne kuma doctor din da suka yi contacting jiya ya aiko musu da email na cewa zasu iya ganin sa next week, dan haka tun a ranar suka fara shirye-shiryen tafiya.

A dakin Fatima tana zaune tana kallon Hussain da yake shirya mata maganar zuwan da zasuyi India shida Hassan saboda Hassan din da yake son ganin likita a can. Tayi kamar zata yi kuka, "kuma yanzu tafiya zakayi ka barni? Ni baka taba yin tafiya ka barni ba fa dan Allah. Ni bana son ka tafi ka barni, zan biku kaji?" Yayi murmushi yana zama kusa da ita. "Haba Princess, in nace zan tafi dake Hassan ba zai ji dadi ba tunda shi yace ba zai tafi da Ruqayyah ba, kinga babu dadi ko? Itama Ruqayyah ba zata ji dadi ba. Ki bari akwai tafiyar da zan shirya mana muna dawowa daga indiyan nan, daga ni sai ke kuma duk kasar da kike so ita zaki zaba" ta fara biga kafarta kamar me shagwaba "ni dai bana so ka tafi ka barni. To ka lallaba Hassan din mana ya tafi da Ruqayyah kaga sai mu tafi gabaki daya"

Yace "Ruqayyah tana shayarwa kin manta? Tafiyar ba zata yi mata dadi ba da babies har biyu ko?" Fatima tace "zan ke tayata rainon ai, sai in karbi daya in bar mata daya" ya hade hannayensa "Please Princess kiyi hakuri, nima bana so in tafi in barki babu yadda zanyi ne" sai yaji maganar tasa tana bada wata ma'ana ta daban wadda tasa yaji jikinsa yayi sanyi. Ita kuma sanyin da taga jikin nasa yayi ne ya sa ta sauko. "Shikenan, Allah ya kiyaye hanya. Amma dan Allah kar ku dade. Kuma kullum sai munyi video call sau biyu" yayi murmushi yace "sau uku ma zamu ke yi, safe da rana da daddare".

Ruqayyah kuma da Hassan ya gaya mata zancen tafiyar tasu cewa tayi "yanzu daga zazzaɓi sai tafiya India? Bana baka magani ba tun a ranar kuma har ka warke" ta fada cikin zolaya, sai dai baiyi dariya ba kuma bata ga alamar zaiyi dariyar ba. Yace "bamu san tsahon lokacin da tafiyar zata dauke mu ba amma muna saka ran insha Allah ba zamu dade ba"

Ta fara kokarin kawo masa korafin cewa ya kamata su tafi tare amma a take ya nuna mata hakan ba zai yiwu ba, daga shi sai Hussain zasuyi tafiyar. Dole ta ja bakin ta tayi shiru, a ranta tana mita "ni sanda ina da ciki har na haihu cewa yayi ba za'a fita dani ba, amma da yake shine daga yin zazzaɓi har anyi booking ganin likita a India"

Babu bata lokaci suka tafi, su ka bar yan'uwa da iyalin su da tunani amma kowa ya dauka Hassan ne marar lafiyar musamman yadda a cikin kwana biyu yayi rama sosai sannan annurin fuskarsa gabaki daya ya disashe. Suna isa Mumbai suka zarce asibitin da Dr din yake suka shigar da information dinsu da komai sannan suka tafi suka kama hotel. Ranar kwana suka yi suna hirar childhood memories, irin rashin jin Hussain da kuma kaffa kaffan Hassan, farkon kafa H and H da kuma yadda tafiyar ta kasance zuwa yanzu. Sai kuma suka yi hirar future dinsu yadda suke son ta kasance, yadda suke da burin yayansu su taso tare and maybe wata rana idan har an samu wadanda suka daidaita a tsakanin su a hada su aure.

Sai bayan da suka yi sallar asuba sannan suka kwanta suka yi bacci tunda appointment din Hussain sai 12. Bayan sun tashi suka yi wanka suka shirya suka fita waje suka ci abinci sannan suka tafi asibitin, duk cikin su babu wanda yake maganar ciwon Hussain amm kuma abin duk yana ransu suna kuma tsoron sakamakon da binciken zai bayar.

A office din bayan sun gaisa da doctor din sai ya saka Hussain ya kwanta a kan wani gado ya mike kafafuwansa sosai sai doctor din ya tsaya a kusa dashi yana yi masa tambayoyi yana amsawa, sai ya dora hannunsa a kasan cikin Hussain ya dan danna da dan karfi, Hussain ya mike zaune da sauri yana damkar hannun doctor din ido a waje yace "ouch, zafi sosai fa" sai doctor din ya bishi da kallo kawai, Hassan ya mike da sauri yana rike hannun Hussain wanda lokaci data gumi ya rufe masa fuska, jikinsa har rawa yake yi.

Sai doctor din ya koma ya zauna yayi rubutu a takarda. Hassan ya koma gaban doctor din ido a bude yana tambayar, "yani zafi, me hakan yake nufi doctor?" Doctor ya dago yana kallon Hassan, ya kasa kallon Hussain yace "ba zan iya ce maka komai ba a yanzu. Zan tura ku dakin gwaje gwaje za'a yi hotuna kuma za'a dauki samples ayi gwaje gwaje. Sai result ya fito sannan zan iya cewa komai" Hassan ya karbi takardar da sanyin jiki sannan ya taimaka wa Hussain ya mike suka fita Hussain yana rike da marar sa. Wata maaikaciyar lafiya tayi musu jagora zuwa katon lab dinsu, inda aka fara gudanar da bincike sosai akan Hussain amma sai daya ja musu kunne kar wanda ya kuma danna masa marar sa, nurses din suka yi dariya suka ce ba zasu yi ba.

Har dare suna can, sai da suka yi exhausting energy din Hussain gaba ki daya sannan suka rabu dashi yana ta yi musu mita. Suka ce washegari ya dawo za'a yi mishi abinda suka kira da colonoscopy. Hassan dai ya lallaba shi suka tafi, a daren Hussain yayi ta bincike akan menene colonoscopy din sai ya fahimci zasu zura mishi micro cameras ne cikin hanjinsa ta yadda zadu ga ko menene a cikin hanjin a screen, anan zasu fi fahimtar in akwai ko babu kuma zasu san exact location din da ciwon yake da kuma stage din da yake ciki. Shi dai a ransa baya so, zuciyarsa tana ta gaya masa cewa ya hada kayansa cikin daren ya gudu ya dawo Nigeria amma yasan in ya gwada yin haka sai sunyi rigima da Hassan, kuma shi yayi alƙawarin ya daina fada da Hassan amma kuma yasan gobe za'a tabbatar masa da cewa yana da wannan ciwon, shi kuma baya son a tabbatar masa din saboda yana son ya cigaba da rayuwarsa freely har zuwa mutuwarsa, wadda yasan zata iya riskar sa gobe ko kuma nan da shekaru masu yawa, Allah ne kadai masani, akwai hikima a cikin tsarin ubangiji da ya hane mu da neman sanin gaibu dan ba zai yi maka dadi ba, ta yaya zaka iya rayuwa in aka gaya mata nan da wata biyu ko uku zaka mutu?

Bai gudun ba ya zauna, ranar da sassafe suka je suka zuwa akayi preparing Hussain aka yi masa allurar bacci, sai Hassan yaji zuciyarsa ta karye dan haka doctor din ya amince masa cewa zai iya shigowa ayi a gabansa. "It is not a surgery, we are just going to view the tumor on a screen and classify it. Then take a sample, that's all".
Chapter 74 · 0% Book details