← Book details Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 134

Sashe 104

Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Ina mai bawa wadanda suka sayi littafin nan hakuri na rashin jina da basuyi ba jiya, nayi tafiya ne kuma gurin da naje suna matsalar nepa, naso in muku typing da yawa dan in wanke muku zuciya amma shima ba zai samu ba. Ayi min afuwa. Biki ne muke yi na dana, zaku jini shiru yau da gobe amma insha Allah jibi za'a samu mai tsaho kuma mai dadi. Zamu ji third wave din da zata yi hitting Ruqayyah.*

Ayi hakuri Please

Wannan littafin na siyarwa ne, in kin ganshi a wani gurin na sata ne. In kina son ki karanta halaliyar ki kiyi min magana through WhatsApp ta wannan number din 08067081020*The Third Wave*

Kusan watanni biyu kenan da rasuwar Hussain. Kusan watanni biyu kenan da rushewar farin cikin rayuwar Hassan. A cikin wata biyun nan ba zai iya tunawa da ranar da yayi murmushi ba ko da kuwa na yake ne, ba zai iya tunawa da ranar da yaji farin ciki a cikin zuciyarsa ba komai kankantarsa kuwa kuma baya jin zai kuma jin farin ciki a kusa, bao san abinda ubangiji ya tanadar masa in the future ba amma ya san da wahala ya samu waniabu da zai maye masa gurbin abinda ya rasa, babu abinda zai maye masa gurbin Hussain da family dinsa including his own family.

Amma kuma duk da haka yasan abinda ya rasa, bayan rashin Hussain ya rasa wanda zai rarrashe shi ne kuma wannan rarrashin da kalamai masu dadi da kantar da hankali su yake bukata, soyayya da kulawa yake bukata, babu kuma abinda ba zai iya bayarwa ba dan yaga ya samu abinda yake so amma shima kanta yasan abin da kamar wuya wai gurguwa da auren nesa. Dan inda zai samu wannan, wadda take da hakkin bashi wannan ita yanzu sam hankalin ta baya kansa ma kwata kwata yana kan nemawa kanta lafiya. Yes, yasan abinda ya faru da ita is quite unfortunate yasan dole ita din abar tausayi ce amma abinda yaso tayi shine ta fawwalawa Allah komai ta gode masa akan niimomin da already ya riga yayi mata bawai ta tayar da hankalin ta kamar yadda ta tayar a yanzu ba. Ba zai iya tuna ranar da yaje dubata ya tarar bata kuka ba, ko kuma ranar da suka yi waya yaji muryarta babu alamar kuka ba. Yanzu gashi doctor din da yake dubata yanzu yace jinin ta ya hau, on top of everything kuma tana kokarin ta dora wakanta hawan jini.

Tunda aka yi mata aikin kunne aka samu nasara kuma aka saka mata hearing aid jin ta ya dawo yaso ace ta dauki kaddara ta dawo gidan ta ta zauna a hankali har asan yadda za'a yi da matsalar kafarta, tunda dai kafar ba wai ciwo take yi mata ba amma sai taki yarda ta tubure masa ta fara bin asibitoci desperately tana neman miracle, kuma kowanne likita in taje gunsa abinda zai gaya mata daban da wanda wani likitan ya fada. Yayi yayi taki hakura, su Baba ma sunyi taki jin maganar su, har ta fara tunanin wai dan nakasa ta same ta shine ba zasu taimaka mata ta samu lafiya ba, shi kuma tace masa dama ba sonta yake yi ba so yake ta zama nakasashshiya dan ya ajiye ta a gefe ya sake sabon aure, shi yasa yace ba zata nemi lafiya ba.

Jin haka yasa ya rabu da ita, kuma duk bill din da akayi masa na magani yana bayarwa amma baya zama tare da ita yana gida yana jinyar tasa zuciyar, dan shi yanzu sam baya son barin gida, baya son abinda zai saka yayi nisa da kabarin Hussain inda kusan kullum nan ne gurin zamansa. Indai ana nemansa a gida nan ake zuwaa same shi ya tasa kabarin a gaba ya zuba tagumi yana tunani, nan ne spot dim tunaninsa tunda dama Hussain ne abokin shawarar sa to yanzu tunda babu Hussain din shine ya mayar da garden din da aka binne Hussain gurin zam yayi tunani, a cikin tunanin ne kuma ya yanke shawarar da tun sanda Hussain ya raba dukiyar sa biyu ya bashi yabi ya fara yinta. Kuma babu gudu babu ja da baya abinda zai yi kenan.

Ya nemi lauyoyin H and H group of companies sun zauna meeting, ya gaya musu kudirin sa kuma kamar yadda ya riga yayi tsammani sun nuna masa rashin amincewarsu. "Ba haka ake business ba Sir" ya mike yace "am not a business man, dan haka ba business ne a gaba na ba. Hussain ne business man kuma yanzu baya duniyar, cigaba da business daga inda ya tsaya ko kuma akasin haka ba zai kare shi ko ya rage shi da komai ba. An riga an rufe littafin sa, abinda zai amfane shi kawai shine sadakatul jariya da yayi sanda yana da rai ko kuma akayi da sunan sa. Ko kuma sadakar da akayi da sunan sa bayan bashi da rai, ko kuma yayan da ya bari a duniya, to shi bai bar Da a duniya ba dan haka abinda ya rage wanda zai amfane shi a yanzu shine sadakar da akayi da sunan sa" ya jawo takardar da already ya riga yayi drafting har ya saka hannu ya mika musu yace "I am going to sell H and H group of companies and all its assets. Zan kuma rabar da dukkan kudin, nawa share din da nasa, ga mabukata da niyyar Allah ya kai ladan kabarin Hussain"

Sai yaga dukkan jikinsu yayi sanyi. Yaji shima zuciyarsa ta karye, yana tunawa da duk irin fadi tashin da Hussain yayi gurin kafa Kamfanin, but keeping kamfanin ba zai amfani Hussain da komai ba a yanzu, bai kuma bar dan da zai gaji sunansa ba ya kuma cigaba da running kamfanin, shi kuma da ya ke da share mafi yawaya gadonsa bashi da wani interest a yin kudi ko kuma living lifestyle irin na Hussain, bashi da interest din zama Hussain dan yasan shi ba Hussain din bane ba, shi a yanzu ma bashi da wani interest na rayuwa kawai dai yana yin ta ne. Abinda zai amfani Hussain kawai yake nema dan da ace idan yayi sallah za'a kaiwa Hussain ladan da kullum in yayi tashi sai yayi masa shima. Dan haka ya yanke wannan shawarar.....

Bayan ya koma gida ya dauko wayarsa da take ta faman ruri tun dazu amma baya cikin mood din amsa waya dan haka yaki dauka, sai da yayi packing sannan ya daga yaga sunna Ruqayyah, sai da gaban sa ya Fadi dan yasan complain din wani abu zata yi masa ko kuma kuka zata yi masa. Ya dauka, kukan kuwa yaji tana yi "tun dazu nake kiran ka mijina kaki ka dauki wayar" yace "am sorry Hassana. Ina meeting ne da lauyoyin H and H shi yasa ban dauka ba" ta danji sanyi a ranta, at least dai dukiyar ta na nan, at least dai komai nakasarta still ita matar mai kudi ne, still ita matar CEO din H and H ce dan haka zata shana kuma zata huta ko da kuwa a Nigeria din ne kadai. In ma kuma kasar take son bari ai ana iya tafiye tafiye a mota ko a jirgin ruwa, yes, zata iya yin tafiya a jirgin ruwa tunda dai mijinta yana da kudin da zai kaita duk inda take so.

But before that, tana bukatar kafarta.

Tace "doctor ne dama ya rubuta mana sallama" Hassan yace "to alhamdulillah. Masha Allah" ta fara kuka "haka ma zaka ce? Ba zaka kira shi ka gaya masa cewa ban warke ba? Ta yaya zai sallame ni bayan ban warke ba?" Ta kwantar da kansa yana dora hannun sa a goshinsa yace "Hassana alhamdulillah fa nace, idan bam godewa Allah ba me kike so ince masa? Ko a bakin kura nake dole ne na godewa Allah tunda har ya halicce ni kuma yasa na rayu cikin imani har lokacin da yayi niyyar daukan raina" tace "kullum haka kake cewa, sai kake acting kana making dina ina feeling guilty ina jin kamar bana godewa Allah bayan da bana gode masa da yanzu zuciya ta ta buga na fadi na mutu" yace "ni ya akayi tawa zuciyar bata buga na mutu ba? Bani da uwa bai da uba dan uwana kuma ya tafi, ina ma zamu iya exchange din guri ni da ke? A dawo min da iyayena da Hussain a karbi kafata daya da kunnuwa na, ke ni ko da idon aka ce za'a hada zan bayar dan nasan Hussain zai kula da ni kamar yadda Sumayya take kula da ke. But you never appreciate her. Ban taba jin kin gode mata ba ko kuma kinyi mata magana mai dadi ba duk da kokarin da take despite halin da ita ma tata zuciyar take na rashin masoyinta" ai kuwa kamar ya tsokano wata rigimar "ni ina mamakin ku kai da Sumayya, yanzu duk halin da nake ciki amma wai baku manta da maganar inyamurin drivern nan ba, baku san irin takaicin da kuke saka min a zuciya ta in kunyi maganar sa ba....." Sai ya cire wayar daga kunnensa ya ajiye ta a gefe ya lumshe idonsa, baya bukatar wani bacin ran in ba so yake shima nasa jinin ya hau ba, sai da ya bar wayar ta huta a gefe sannan ya dauka ya mayar kunnensa yace "hello" tace "shine kayi shiru ko?" Yace "to ai babu abinda zan ce miki ne. Gobe zan taho kanon da wuri insha Allah, ku shirya kafin inzo, ina zuwa sai mu karbi takardar mu taho gida" daga nan ya katse kiran sannan ya kashe motar ya fita, ya daga kai yana kallon gidan Hussain wanda har yanzu yake a rufe, har yanzu ya kasa samun courage din shiga ballantana ya samu damar duba personal kayayyakin Hussain.
Chapter 104 · 0% Book details