← Book details Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 127 OF 134

Sashe 127

Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sun tafiya ta koma saman da sauri ta shiga dakinsa, ta yaba da tsaftar dakin sosai dan ba zaka taba cewa dakin namiji bane ba ta gyara masa gadon ta share ta wanke toilet ta fitar da kayan wanki sannan ta koma bata dakin shima ta gyara. Kafin ya dawo har ta kusa gama gyaran gidan, sai ya dage wai lallai sai ya taya ta aikin ta hana shi yakinyarda sai ta bashi duster ya fara goge goge, tana tayi masa dariya, ita sai taga abin mamaki namiji da aiki, hannun sa kamar yayi wa duster din girma, sai shi kuma ya fara bata labarin yadda yake aikin gidansu sanda yana saurayi "Hussain baya komai sai bata guri, ninake yin kusan komai a gidan lokacin su Hassana basu girma ba aunty kuma bata da yan aiki. Har wanke wanke nayi wa aunty. A haka na saba, ni ina enjoying gyaran gida ma sosai sai inji kamar wani responsibility ne daya kamata inyi"

Tare suka gama komai har kitchen ta gyara ta hada wa Aunty kayan abincin da ta aiko musu dashi jiya, kamar hadin baki tana fitiwa dashi ana aiko musu da wani sai ta bayar da na jiya aka tafi dashi sannan ta dauko musu plates suka zauna a kasa akan carpet ta zuba masa zata zuba nata yace sai dai su ci tare, sai taji wani iri dan jiya ma da daddare haka ya dage ta hada musu abinci gabaki daya har yara a tray suka ci gabaki daya, but wancan da yara, wannan kuwa su biyu ne kawai.

Amma bata son yi masa musu, tayi wa kanta alkawarin ba zata ke yi masa musu ba dan haka ta saka chokali a nasa suke ci tare, ya lura a takure take sai ya fara yi mata hira, a lokacin ta lura da wani abu a tare dashi, da wahala yayi dogon sentence ba tare daya ambaci sunan Hussain ba, sai ta tuna da tata twin din, ko a wanne hali take ciki? Ta dauka zata dawo da safe amma shiru har gari ya sake wayewa.

Bayan sun gama ne ya hau sama ita kuma ta gyara gurin da suka bata. Bai jima ba ya sauko yace mata zaije gidan Aunty "zanje gurin Hussain". She was confused sai daga baya ta tuna a gidan aka binne Hussain, kabarin sa zaije kenan. Sai takara jin tausayin sa sosai, lallai shi din ya hadu da jarabawowi da yawa a rayuwa, lallai shi din abin a tausaya masa ne, lallai yana bukatar mai faranta masa rai a yanzu.

Bayan ya tafi ta koma dakinta tayi wanka ta shirya tsaf da ita ta bade kanta da turare, sannan ta hada kayan wankinsa data dauko da nata dana yara da suka cire da towels din da suka yi amfani dasu duk ta je toilet din yara inda taga washing machine sabo a ciki, ta dauki manual dinsa taga yadda ake amfani dashi sannan ta dauko detergent din da ta gani a toilet dinsa ta wanke kayan tsaf ta matse su, ta zagaya baya ta backdoor inda tasan akwai igiyar shanya tun Ruqayyah tana gidan ta shaya kayan ta dawo palo tadauki wayarta tana duba messages din da kawayenta da kuma yan uwan da basu samu damar zuwa bikin ba suka turo mata.

A lokacin ne aisha ta shigo, tsohuwar yar aikin Ruqayyah ce tun tana tare da Hassan, Sumayya ta tashi zaune tana kallon ta ganin tashin hankali a rubuce a fuskarta. "Aisha lafiya? Aisha ta fara hawaye "Aunty Sumayya dan Allah ki zo, Aunty Ruqayyah tunda ta kwanta jiya da safe har yanzu bata tashi ba. Kofar dakin arufe munyi ta bugawa bata bude ba"

Wani abu ya dunkule a kirjin Sumayya, ya tokare mata hanyar da numfashi yake shiga hunhun ta. Ta mike tsaye tana kallon Aisha "tun jiya? Tun jiya da safe fa kika ce? Kuma ku baku yi tunanin ya kamata ku fada ba?" Tace "dama ita kadai taje zama, mun dauka idonta biyu ko dan bata son a dame tane ya sa ta rufe kofa, sai da muka ga duk abincin da muke kai mata bata tabawa sannan muka fara buga kofar kuma bata bude ba" ta share hawaye, "muna tsoron tayi mana fada ne shi yasa muke gudun damunta"

Cikin karkarwar hannu Sumayya ta dauki wayarta ta fara neman number din Hassan, shine a kusa shine namiji shi ya kamata ta fara kira, kuma shine zai bata izinin fita taga halin da yaruwarta take ciki. Sai dai tasan yana gurin kabarin Hussain ko zai iya daukan waya?

Bugu daya ya dauka "hello Noorie" bata kula da sunan daya kirata dashi ba tace "dan Allah kazo ka taimaka min" yadda yaji tashin hankali a muryar ta haka shima nashi hankalin ya tashi. "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Me ya faru?" Cikin rawar murya ta fada masa abinda Aisha ta gaya mata, bai jira komai ba yace ta fita ta shiga gidan, ta kira mai gadi ko duk wani namijin da yake gidan tace inji shi yace su balla kofar dakin, shima gashi nan tahowa.

Kusan a tare suka je gidan, sai dai da yake shi namiji ne yafi ta doguwar kafa sai ya wuce ta zuwa saman, sanda taje already yana kokarin balla kofar amma being kofar da Hussain ya saka sai taki balluwa. Da sauri ya fita, a lokacin Sumayya ta gama rikicewa kuka kawai take yi tana buga kofar amma babu ko alamun Ruqayyah a ciki, a hargitse ya shiga dakinsa ya binciko key din part din Hussain da ya ajiye sannan ya dawo ya shiga part din Hussain ya nemo spare keys din gidan gabakidaya sannan kuma suka fara neman key din dakin da Ruqayyah take ciki.

A ransa yana cewa gidan da Ruqayyah take so fiye da shi shine zai zama ajalinta in tayi wasa, da kyar suka samu wanda ya bude kofar dakin sannan suka shiga.

Tana kwance a kan gado, idanunta a rufe, a gefenta da robar ruwa da sleeping pills. Da sauri Sumayya ta tafi kanta tana jijjiga ta, sai taga kamar ba Ruqayyan ta ba, kamar wata ramammiya mai kama da Ruqayyah. Hassan ya karaso yana janye Sumayya daga jikin Ruqayyah sannan a hankali ya dora hannunsa a gefen wuyanta yana so yaji heartbeat. Can ya jiyo shi da nisa, she is alive but barely.

Wannan littafin na siyarwa ne idan kika ganshi a wani guri na sata ne, in kina son ki sayi halaliyar ki ki yi min magana ta wannan number din through WhatsApp 08067081020

*Ina masu bukatar hadadu kuma ingantatun turarukan wuta da khumra masu dadin kamshi kuma a farashi me sauki to ga dama tazo muku Awwaba scent nada turarukan wuta humra burners kasko shisa coal dorot stool dilka body milk dadai sauransu masu bukatar na iya nemansu a whats app ko kuma kira ta wannan lambar 08034236800*
*bugu da kari duk wanda ya sayi humra ko turaren wuta a cikin wannan watan akwai kyautar dilka me kyau tafiyaya daga kasar chad wadda zata gyara jiki tay expoliating skin acikin minti 20 kawai ku garzayo dan kwasar garabasa*
*Adress kundila zoo road kano muna tura sako ko ina da iznin Allah**Unstable*

Sorry for the typos

Ya mike tsaye tare da ja da baya, sannan ya dauko wayarsa yayi dialing number din doctor dinsu, ya fita yana waya dashi, wannan ya sa Sumayya ta koma da sauri gaban Ruqayyah ta saka hannun ta a inda Hassan ya dauke nasa tare da kara dan yatsanta na daya hannun a kofar hancin Ruqayyah, ta jiyo heart beat din sannan taji hucin numfashin ta a hannunta amma bayan wannan babu alamar rai a tare da ita.

"Ruqayyah! Ruqayyah ki tashi dan Allah, ki tashi muyi magana dan Allah" tana jim Hassan ya dawo dakin yace "doctor yana zuwa yanxu" bata ce komai ba sai ya karaso ya dauki robar maganin yana karanta wa yace "maganin bacci ne, overdose tayi maybe" Sumayya ta gyada kai tana share hawaye tace "na gane shi, tun sanda ina jinyar ta a asibiti shi take sha kafin tayi bacci, bata iya bacci tsorata take yi duk dare" sai kuma ta fashe da kuka, tausayin halin da Ruqayyah take ciki take yi sosai, wannan wacce irin rayiwa ce yar uwarta ta dora wa kanta.

Tana tuno yarintar su da irin burikan Ruqayyah amma bata taba tsammanin cewa zata kai ta ga haka ba, bata taba tsammanin kaddarar su zata zama haka ba. Ta fara kallon fuskarta tana shafa kanta a hankali tana kiran sunan ta, ga dai kaya masu kyau a jikinta amma shi jikin bashi da kyau, ta rame fiye da tunanin Sumayya, dama kuma ita Ruqayyah bata da jiki sosai. Ta mayar da idonta kan kafarta marar lafiya taga yadda kafar ta kara motse wa ta yamushe kamar ma jini baya zuwa kafar.

Sai kawai ta fara karanto mata adduoi tana tofa mata a haka har doctor din ya karaso suka shigo tare da Hassan, suna shigowa Hassan ya dauki robar maganin ya mika wa doctor din suka yi maganganu sannan Hassan yazo ya kama hannun Sumayya ya daga ta tsaye sannan ya jata suka fito waje. Sai da suka fito palo sannan ya saki hannun, tayi sauri ta saka hannun a cikin hijab tana mummurza shi tana sunkuyar da kanta kasa, ya jingina da jikin bango yana kallon ta yace "wai dan na rike hannunki shine kike wannan abin?" Ta girgiza kai da sauri, amma a ranta tasan haka ne, ita wani namiji bai taba kama hannun ta ba kuma bata taba zaton cewa Hassan mijin twin sister dinta shine zai zama na farko ba.
Chapter 127 · 0% Book details