← Book details Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 134

Sashe 43

Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Da zasu fita Aunty tace da Ruqayyah "in anyi magrib mai kwalliya zata zo tayi miki, sai ki fito da duk kayan da zaki bukata ki ajiye su a kusa sannan ki yi Sallah da wuri kar ta zo tana jira tunda ita zata yiwa Hassana ma. Fatima ta taho da nata" Ruqayyah ta gyada kai amma sai taji zuciyarta ta tabu, dan me aunty zata ce mata Fatima ta taho da nata? Ko tana tuna mata ne cewa ita bata taho da tata ba?

Bata yi wanka ba tunda tayi dazu, dakunan kasa aka budewa yan uwanta suka yi ta shirin su a ciki, bata tuna da kawayenta ba sai data ji hayaniyar su sun shigo sannan suka hau sama gurinta. Suna ta hayaniyar su kuma mostly zancen basu akan waye mai gidan kusa dana Ruqayyah ne, ita Ruqayyah sai taji suna kara mata pressure ne , tayi nadamar ina ma bata yi hayar su ba? Kadan daga cikin su ta sani suma kuma Minal ce kawai wadda ta sani sosai, duk sauran hada ta akayi dasu. Anan suka shirya, tare da hargitsa wa Ruqayyah kayan kwalliyar ta, wasu suka debi rabon su a ciki. A karshe ma sai da Sumayya ta faki idonsu ta kwashe kayan ta saka a closet ta rufe sannan aka samu lafiya. Shima suka yi ta mata mita. Ruqayyah kuwa sai shiga toilet tayi ta rufe kanta saboda hayaniyar su tayi mata yawa. Sai da aka ce ga mai makeup din tazo sannan ta wanke jikinta tayi alwala ta fito. Sai data yi sallah sannan ta zauna suka fara kwalliyar, yarinyar ta kware sosai a aikinta dan haka nan da nan ta mayar da Ruqayyah zuwa irin matan da take ganin hotunan su a Instagram. Ta taimak mata ta sak kayanta, making some adjustments here and there, yadda rigar ta zauna sosai, sannan ta saka mata duk accessories din da suka dace, wanda taga baiyi ba kuma tace a chanja wani, har ta gama shirya ta tsaf yadda Ruqayyah tasan ko a Instagram din ne ma sai an duba kafin a samu amaryar da tayi kyawun ta.

Sumayya ta fito da ita palon sama ta zaunar da ita sannan itama ta tafi ta fara nata shiryawar. Itama irin ankon kawayen Ruqayyah ne ta saka sai dai nata dark pink nasu light pink. Ita kuma amarya peach. Sai a lokacin Ruqayyah ta kira Hassan. "Ka manta dani" ta fada da muryar shagwaba, yace "kin taba ganin inda mutum ya mance da rabin jikinsa a wani waje? Tace "gashi kuwa, tun safe fa baka ko bi ta kaina ba" yace "sake dubawa dai, ki lissfa missed calls nawa na ajiye miki a wayar ki" tace "ni ban gani ba" yace "kun shirya? Cos Gamu nan fitowa yanzu" tace "mun gama ai, ku kadai muke jira"

Abun ya matukar kayatar yadda angwaye Hassan da Hussain suka shigo su kadai a mota daya, Hussain da kansa ne yake driving Hassan yana gaba, suka fara zuwa kofar gidan Hassan Ruqayyah ta fito a bisa rakiyar kawayenta ta shiga sannan suka karasa kofar gidan Hussain Fatima ta fito itama ta shiga ita kadai, suka rufe mota suka ja suka yi tafiyar su. Sai bayan sun fita sannan aka fara rububin shiga motoci ana bin su a baya. Suna zuwa gurin taron suka yi packing a bakin kofar shiga gurin sannan suka yi zaman su a mota.

Tun da Fatima ta shigo take ta yabon kyawun da Ruqayyah tayi, wannan yasa Ruqayyah ta kara kumbura tana ta faman fasa kai duk kuwa da cewa tun da Fatima ta shigo motar taji ta raina kanta, hatta kamshin da take yi na daban ne yanayin kwalliyar ta ma haka. Fatima irin cikakkun matan nan ne masu cikar kirji da hips, wannan yasa kayan jikinta suka yi mata matukar kyau suka fitar da kyakykyawan fasalinta duk da cewa ba kama mata jiki suka yi ba, ga kuma dogon trail din da aka dinka a jikin rigar kamar yanayin dinkin alkyabba daya taso tun daga kafadar ta ya rufe mata kurjinta sannan ya sauka har kasa yana jan kasa yana binta a baya, sai ya zamanto kamar yayi serving a matsayin mayafi kenan. Angwayen kuma anko suka yi, komai nasu iri daya ne hatta agogon hannayensu, sai a lokacin Ruqayyah ta kara tabbatar da kamannin su. Hira suke tayi, Hussain yana ta tsokanar kowa har Fatima bai bari ba ita ma kuma sai ta rama, yace wai kowa a cikin su ya kure adaka dan ace sunyi kyau shi kuma yasan duk ya fi su kyau, har da posing yake yi wai matso kyan sa yake yi, wai sai lallai sunce duk yafi su yin kyau. Ita Ruqayyah yadda taga Fatima tana magana da dariya sai abin ya bata mamaki, sai taga kamar ba wannan gimbiyar da bayi suke kwanciya a gabanta bace ba. Ita ta dauka ai da kyar take magana saboda mulki. Sunyi ta hotunan su a cikin motar, itama Ruqayyah ta dan ware tayi magana da taji Hussain ya saka ta a gaba wai in bata magana zata haifi kurma. Suna ganin mutane suna ta shiga hall din, sai da aka tabbatar kowa ya gama shiga sannan aka zo kiran su, a lokacin itama Hassana da angonta Saeed sun karaso. Sannan sai suka jera suka shiga. Kawayen sune suka fara shiga a layi, kawayen Ruqayyah a farko, sai na Fatima sannan na Hassana, kowanne sunyi anko. Daga sai masu gayya masu aiki, Hassan rike da hannun Ruqayyah a gaba, Hussain da Fatima a tsakiya, Hassana da Saeed a baya. Sai kuma abokan angwaye suka take musu baya. Abin gwanin burgewa.

Komai ya tafi bisa tsari, anci an sha an bar abinci, anyi programs masu kayatarwa yawancin su na barkwanci, sannan Aunty ta gabatar da jawabin godiya ga duk wanda ya samu halartar bikin. Daga nan kuma sai akayi ta daukan group pictures. Anyi kida nayi rawa, amma sai amaren duk kamar sun hada baki suka ƙi yin rawar. Angwaye kan sun cashe abinsu, abin mamaki sai ga Hassan ya biye wa Hussain suna ta rawa, ai kuwa nan take guri ya dauki ihu da tafi aka fito akayi ta musu ruwan kudi, kudi dai kam kamar ba'a talauci a Nigeria. Daga nan sai suka yanka cake akayi addu'a aka tashi.

Daga gurin taro aka wuce da Hassana gidan mijinta, wannan yasa duk yan gidan basu dawo gida ba can suka wuce, amaren ne kawai da kawayensu suka dawo. Kamar yadda aka dauke su haka aka dawo dasu, aka fara sauke Ruqayyah sannan aka karasa da Fatima.

A gajiye Ruqayyah ta shiga gida. Gidan ba kowa tunda su suka fara fita amma tas tas dashi yan aikin da aka kawo mata sun gyara mata shi kamar ba'a yi taro ba. Ta wuce sama ta cire tarkacen kayan jikinta dama duk sun bi sun ishe ta sannan ta kwanta akan gado yana mayar da ajjiyar zuciya. Ta lumshe idonta tana tunanin event din, gaskiya ya kayatar da ita, tayi ta kokarin ta gano fault a ciki amma ta kasa, sai dai kawai tasan kawayen Fatima sunfi nata haduwa, ta kuma san mutanen gurin sunfi bada karfin su ga Hussain da Fatima akan ita da Hassan.

Tana nan kwance ta jiyo hayaniyar kawayenta suna shigowa. Kamar yadda suka sabarwa kansu direct bedroom dinta suka zarce suna ta hayaniya. "Ni ban gane ba Ruqayyah, naji a gurin kamar ana cewa kanin mijinki ne mai kamfanin ba mijin ki ba, menene gaskiya wai?" Wata tace "ni kuma ji nayi ance nasu ne su biyu wai Hassan and Hussain shine h and h din" Sumayya data fara rage kayan jikinta itama tace "to ku menene naku a ciki? Me zaku karu dashi in kun san waye?" Minal da take kwance rashe rashe akan gado tace "dan musan yadda zamu yi pricing kudin siyan baki mana? Ai iya kudin ka iya shagalin ka ne abin" ita dai Ruqayyah baya ce musu komai ba, sai kuma suka koma hirar wai waye yafi haduwa a tsakanin angwayen, kowa tana fadar gwaninta tana kuma fadar dalilin ta. Can suka ji tsayuwar mota sai suka garzaya taga suna leken motocin da suka tsaya a gaban gidan Hussain. Wata tace "wai Allah! Wannan gida! Gaskiya Ruqayyah da sake, in dai har kamfanin nan nasu ne su biyu to ki tubure ki ce sai dai ku zauna tare a can gidan, ai zai ishe ku" wata kuma tace "ni ta mijin nake bata gidan ba, gayen ya hadu karshen haduwa gashi ya iya daukan wanka"

Ruqayyah ta mike ta shiga toilet ta rufe kanta kamar dazu, bata so su kara mata bakin ciki, ta samu zuciyarta ta dan kwanta su kuma suna so su kara taso mata da ita. Sumayya ta cire kayan ta ta saka simple ones sannan ta hada duk kayan da tazo dasu a jakarta, ana gam siyan baki itama zata tafi gida, sun riga sunyi magana da Adam yana jiranta a waje zai je ya kaita.
Chapter 43 · 0% Book details