Sashe 107
Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Yana kallo rigar Yusuf da take hannunta ta zame ta fadi, yanayin fuskarta ya fara chanzawa from fair to bad then to worst. Har saida yanayin ta ya juya zuwa yadda bai taba gani ba, sai yaga gabadaya ta chanja daga Hassanar da ya sani ya kuma aura zuwa wata halitta ta daban wadda bai taba sani ba. Tabbas yasan tana son kudi, yasan ta boye masa cewa tana son kudi tun ranar da tayi subutar baki a gabansa ta gaya masa cewa shi bashi da komai dan uwansa yana da komai, amma bai taba zaton son da take yiwa kudi ya kai wanda yanayin ta zai iya wannan chanzawar a lokaci daya ba dan yace zaiyi wa dan'uwan sa sadaka da kudin da dan'uwan nasa ne ya tara da kansa ba wani ne ya tara masa ba.
Yana kallonta ta mike tsaye, har tana bude Yusuf da yake kusa da ita yana jiran ta saka masa riga, amma bata kalli yaron ba kamar ma bata san ta bige shi din ba tace "what? Me naji kace?" Ya rungume hannunsa yana kara studying dinta yace "abinda kika ji shi na fada, zanyi sadakar duk abinda Hussain ya bari da kuma share din daya bani kafin rasuwar sa ga mabukata, da fatan Allah ya kai rahama kabarin sa, thats how much nake son sa"
Idonta yaga ya kawo ruwa sannan hawaye ya fara zuba daga idon, ta bude baki ta mayar ta rufe, amma bai fita ba kuma bai daina kallon ta ba yana so ya karanta wani abu a idonta, yana so ya hango ko da burbushin yarinyar nan data taimaka masa ranar nan a idonta amma babu, she is totally gone.
Ta hadiye abinda ya hana ta magana sannan tace "love? Love kake cewa? That's how much kake son Hussain, Hussain da baya duniya bayan mu kuma gamu a duniya, what about us? Mu baka son mu? Ni da yayanka. In kai baka bukatar dukiyar mu ai muna bukata, ni da yayanka, ta yaya zaka kula damu? Ko dan na zama nakasashshiya shine kake saka ran zan fita inyi bara in samo abin bukata? Wannan shine abinda kake nufi?" Fada take yi tana magana da duk kan karfinta, daga inda yake yana kallon yadda jikinta yake rawa, yana kallon yadda rage yake burning a cikin idonta. Bai taba dauka zata dauki zafi irin haka ba akan kudin da ba nata ba. Sai ya tako xuwa kusa da ita yace "yayana da ke da kannena da aunty duk responsibility dina ne, zan kula daku koda dako zanyi a kasuwa, kudin Hussain shi ya tara bani ba and am sending it back to him, nima zan tara nawa zan kuma kula da ku da iyakacin arzikin da aka rubuta min, na yanke wannan hukuncin tun ranar da Hussain ya raba dukiyar sa biyu ya bani saboda in kula da kaina in kuma kula da aunty da yan uwanmu saboda yana gudun kar Fatima ta haifi namiji in kasa gadarsa, yes, that's how much he loved me. And....." Ta kwace hannunta daga nasa tana masa wani irin kallo, tace "rabin dukiyarsa? Ya baka? Amma baka taba gaya min ba a matsayi na na matarka?" Yace "yes, saboda banyi niyyar amfani da ita ba tun a wancan lokacin, dan haka nayi tunanin gaya miki bashi da amfani" ta dafe kanta da hannu biyu tana fitar da numfashi sama sama, Wato tayi spending time a matsayin matar ceo without her knowing, kuma da tasan da wannan maybe da bata yi abinda tayi har yake hanata bacci ba. Ta bude idonta tana kallonsa tace "da kasan abinda kayi da bakayi ba, da zan gaya maka abinda kayi da kayi nadama babba" ya bude ido yace "me nayi? Dan ban gaya miki kanina yayi min kyauta ba shine zanyi nadama? I don't think so" sai kawai yaga tayi wani irin murmushi ta kawar da kanta gefe sannan tace "lallai rashin sani kukumi ne" ya saka hannu ya juyo da fuskar tata yace "me kike nufi, what don't I know?" sai ta rufe idonta saboda bata son ganin cikin idonsa, ko wuka zai saka mata a wuya ba zata fada masa abinda tayi dan ta samu dukiyar da yake kokarin rabarwa ga mutanen da ko sanda basu taba dagawa dan ganin samuwar dukiyar ba, bayan ita sai data....sai data...., Ko a cikin zuciyarta bata fadar abinda tayi ballantana a fili, ballantana a kunnen Hassan. Amma wannan hanyar daya dauko ba mai bullewa bace ba, she deserves that money, ba zata yi biyu babu ba, ba zata taba barinsa yayi mata wannan tozarcin ba, za kuma tayi komai dan ganin baiyi abinda ta gani a idonsa cewa ya gama daukan niyyar yi ba. In tace komai tana nufin komai.
Ya saki fuskarta jin bata ce komai ba. Ya yi taku biyu baya yana kallonta yace "akwai abinda kike boye min. Me kika sani wanda ni ban sani ba? Me kika aikata?kina son kudi na sani, ba kya son in bayar da kudin nan na sani, amma ina so ki san cewa kamar nayi na gama ne, ke matata ce, responsibility dina ce kuma zanyi iya kacin kokari na na ganin cewa na kula da ke na sauke duk wasu nauye nauyen ki da yake kaina. Amma dukiyar Hussain, no"
Ruqayyah tace "ni kuma zanga ta yadda zaka rabar da ita din, tsakanin ni da kai dan halak ka fasa, wallahi in dai ina numfashi ba zaka bayar da ko da kobo a cikin kudin nan ba, saboda kudin nan is as much mine as it is yours saboda ni matarka ce uwar yayan ka ce" bai ce mata komai ba sai ya juya yana kokarin barin dakin, shi duk inda tashin hankali yake yanzu baya baya yake yi dashi ba wai dan yana gudun mutuwa ba sai dan yana gudun wahala, yana gudun ya zama responsibility a gurin wadanda suke responsibilities dinsa saboda shi kansa yasan ciwo yana daf da kama shi indai rayuwa ta cigaba da tafiyar masa a haka.
Ta bi bayansa da kallo tana daga kafarta da kokarin zuwa ta tari gabansa, ta manta ma da problem din kafarta, jin kafar taki responding ya tuna mata da cewa kafar ta daina aiki wannan kuma ya kara tunxura ta tace "wallahi baka isa ba Hassan, wallahi baka isa ba kayi kadan wallahi. Wallahi sai dai ka zaba ko Hussain din da baya duniya ko kuma ni da yayana da muke da rai kuma muke da hakki akan ka. Wallahi ba zan taba barin ka ka aikata abinda kake da niyyar aikatawa ba, wallahi....." Karar rufe kofarsa ya ankarar da ita cewa ya fita ya bata guri.
Ta zauna tana rusa kuka kamar wadda aka aiko mata da labarin mutuwar Baba da Inna a lokaci daya. Dan yadda take ji a ranta bata jin ko daya daga cikinsu ne ya tafi zata ji wannan bakin cikin. Yaran ta da suka gaji da jiran ta saka musu riga suka fara wasan su a kasa ta kalla, duk mafarkan ta tana hango yaran a ciki, tana hango cewa sun girma cikin dukiya da wadata ba irin yadda ita ta girma cikin talauci da kunci ba. Duk dan su take yi, shi kansa Hassan din da yake ta wannan firirita dan shi take yi dan shine zai zauna akan kujerar da take fighting for ba wai ita ce zata zauna ba. Shi wanne irin mutum ne mai zuciya kamar dutse? Da wani irin rikakken ra'ayi kamar dangin firauna.
Sai taji a ranta tana missing Minal, da tana nan da yanzu ta dauki waya ta kirata ta gaya mata problem dinta amma Minal bata da rai a yanzu kuma babu wanda ya sani sai ita kadai. Ta goge hawayenta tana tuno da yadda gawar Minal tayi a cikin mota da yadda kaurin konewar gawawwakin ya cika dajin, sai taji a hancin ta kamar tana shakar kaurin a yanzu. Tayi sauri ta girgiza kanta dan it has been very hard for her to keep that secret to herself sannan kuma Hassan yace duk wannan a banza? Gaskiya ba zata yiwu ba. So yake tayi biyu babu? Bayan ta tafka kuskuren da ita kamta tasan zai taba lahirar ta dan ta sami duniya shine zai ce duniyar ma ba zata samu ba? Wato babu duniya babu lahira kenan!
Hassan yana fita daga dakin ya dafe kujera saboda yadda yake jin bugawar zuciyarsa yana kara gudu sosai kamar zata fito daga kirjinsa, yana jin kalaman da Ruqayyah ta bi bayansa dasu amma kuma baya son ya koma su cigaba da rigima akan dukiyar Hussain. Dukiyar da babu abinda zata kara musu gabaki dayan su. Shin wannan ita ce matar da ya zabawa kansa? Ita ce kuma uwar daya zabawa yayan sa?