← Book details Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 134

Sashe 105

Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Gidan Aunty ya shiga, ya tarar tana cin abinci shima ya zauna ta zuba masa da kanta ya fara chachchakula kamar mai cin magani, tunda akayi rasuwar nan haka yake cin abincin sa dan shi kansa ba xai iya tuna ranar da yayi enjoying abinci ba. Ta zuba masa lemo tana cewa "Fulani Hadiza, kishiyar Maman Fatima tayo min waya jiya" ya tsaya da taunar abincin ya dago kai yana kallonta yace "me tace?" Tace "cewa tayi gobe idan Allah ya kaimu zasu aiko a debi kayayyakin Fatima" ya ajiye chokalin yana jin abincin ya tsaya masa a kirjinsa, a idonsa yana tunawa da ranar da aka zo akayi jeren kayan Fatima ana ta kide kide da fara'a da wasa da ɗariya, babu wanda zaiyi tunanin shekara biyu ne kadai ya rage mata daga ita har mijinta a duniya, yatuna da irin lodin kayan da aka zuba mata har sai da aka juya da wadansu duk kuwa da yawa da kuma girman dakunan ta.

Can cikin makwogwaron sa yace "Allah ya kaimu goben. Akwai keys a nan ko?" Tace "eh akwai" sai ya gyada kai kawai yana ture abincin. Zuciyarsa tana yi masa zafi, tragic deaths of family din dan uwansa yana dawo masa sabo. Aunty ta lura da chanjin yana yin sa sai ta fara kokarin cheering dinsa ta hanyar bashi labarin twins dinsa da da irin rigimar da suka yi tayi mata da taje gurin Inna ganinsu suna cewa sai sun biyo ta,ta san babu abinda yake faranta masa kamar labarin ƴaƴan sa amma sai taga ko murmushi bai yi ba ballantana dariya, yi yayi ma kamar baya jin abinda take cewa har sai da yaji tayi shiru sannan ya mike yayi mata sallama ya fita.

A ranar da daddare ya bude gidan Hussain ya shiga. A palon farko ya tsaya ya kunna fitila, idonsa ya sauka a kan katon hotonsu shi da Hussain, ya taka a hankali ya je gaban hoton ya tsaya ya a kallon fuskar Hussain, a kansa yana bitar maganganun da suka yi lokacin da akayi hoton da yadda Hussain ya ringa gyara zama wai shi lallai sai yayi zaman da yafi kyau. "Ka tabbatar na fishi kyau fa!" Ya gaya wa camera man din. Hassan ya saka hannu ya shafa fuskar sa, a hankali yace "ranar da ka bar duniya kafi kyau akan kowacce rana".

Sai ya juya ya doshi stairs din da sauri kafafuwan sa har suna hardewa cikin junansu. Bangaren Hussain ya shiga ya kunna fitila yana kallon gurin kamar yau ya fara shiga, taste din Hussain yana da karfi sosai dan haka sai yake ganin kamar komai na gurin kama yake yi masa da Hussain. Sannan ya wuce cikin Bedroom dinsa, ya tarar da komai a gyare tas kamar jiran mai dakin ake yi yazo, sai dai yar kura da dakin yayi. A kan bedside ya ga hoton su replica na wanda yake dakinsa, ya dauka yana kallon yace "mai gasa kawai. Dan na saka a dakina shine kasa a dakin ka ko?" Sai yaji a ransa kamar Hussain yace masa "ni ba zanyi fada da kai ba" shima sai yace "nima ba zanyi fada da kai ba" sai ya ajiye hoton ya zauna akan gado, har yanzu ya kasa yanke hukuncin abinda zaiyi da gidan, shima da yayi niyyar zai siyar da shine kamar yadda zai siyar da duk sauran gidajen Hussain amma yanzu da ya shigo gidan, da yaga gidan, sai yaji kamar ba zai iya siyarwa din ba, akwai memories na mutanen gidan sosai a cikin gidan, sweet sweet memories da ba zai so ya rabu dasu ba. Da ya shigo dakin sai yaji ya rage jin loneliness, kamar Hussain din yana tare da shi.

Ya ja pillow ya dora kansa yana tuna ranar da Hussain yaje kan gadonsa ya kwanta har ya tsokane shi yace pillow din Ruqayyah ya kwanta akai, shima sai ya ture pillow din kamar yadda Hussain ya ture a lokacin, a nan ne idonsa ya sauka akan diary din, diary din da Hussain kullum yake ta faman rubutu a ciki kuma ya hana kowa karanta wa. Ranar nan babu yadda baiyi ba ko page daya ya bashi ya karanta amma ya hana shi. Ya saka hannu ya dauka a ransa yana tambayar kansa if it's right ya karanta a yanzu. Shin Hussain zai so ya karanta a yanzu da bashi da rai ko kuma zai so yayi destroying ba tare da ya karanta ba? Ya jima yana lissafin abin sannan a karshe ya yanke shawarar zai fara karantawa amma in yaji abin da bai kamata ya karanta bane ba zai fasa karantawa sai ya kona shi.

A zauna akan study table da yake can gefe ya kunna lamp din gurin sannan ya fara karantawa.

Dear baby ....

A hankali yake bin handwritten rubutun Hussain yana karantawa har ya gama page din farko ya bude na biyu, a lokacin ne ya fahimci wasiyya ce Hussain ya rubuta zuwa ga abinda Fatima zata haifa. Sai ya rufe diary din yana jin hawaye yana sauka a gaban rigarsa ba tare da yasan lokacin da suka fito daga idanun sa ba. "Yah Allah, kai ka barwa kanka dalilin da yasa wannan abin ya faru, ya Allah ka bani zuciyar dauka".

Bai kuma bude diary din ba saboda baya jin zuciyarsa zata iya daukan abinda yake ciki, musamman idan ya tuna da cewa shi wanda ya rubuta din bai san cewa wanda ya rubutawa ba zai zo duniyar ba ballantana har ya girma har ya karanta. A dakin ya kwana ranar, amma sai ya kasa daukar komai kamar yadda yayi niyyar daukan very personal abubuwan Hussain. Da safe ya tashi yayi sallah a dakin sannan ya dauki diary din ya je karshen sa ya rubuta date din da Hussain ya rasu sannan ya bude safe box din Hussain, wadda su biyu kadai suka san code din ya saka a ciki ya rufe. For some unknown reason sai yaji yana so ya ajiye diary din, duk da cewa a zuciyarsa yana jin komai dadewar mutuwar Hussain ba zai iya karanta wa ba.

Bayan ya koma part dinsa ya shirya sai ya dauki hanyar kano shi kadai. A kan hanya ne ya yanke hukuncin zai saa sake bincika masa kwararren likita guda daya wanda Ruqayyah zata ke gani amma kuma zai gaya mata da kakkausar murya cewa shi kadai zata ke gani babu chanji, sai su jira kuma suga abinda hali zaiyi.

Yana zuwa gurin likitan dayake dubata ya fara zuwa, dama sunyi waya tun kafin ya karaso, sai likitan yayi masa bayanin cewa sunyi iyakacin kokarin su wajen ganin cewa sun fahimci inda ciwon Ruqayyah ya dosa amma basu fahimta ba, in sunbi ta nan sai kuma suga wani abu daban. "Sai dai in zaku gwada wani asibitin kuma ko kuma ku fitar da ita waje" Hassan ya gyada kai yace "haka ne, mungode sosai. Allah ya saka da alkhairi" daga nan bai kara komai ba.

Yana zuwa gurin su Ruqayyah ya tarar sun shirya, sai dai wai tun da assuba Ruqayyah taki saka hearing aid dinta taki yiwa Sumayya magana duk da ita Sumayyan bat san laifin da tayi mata ba. Shima ya yi kokarin yi mata magana amma ta dauke kanta gefe taki kula shi duk da tasan magana yake yi mata. Tunda yaga haka sai ya rabu da ita suka gaisa da Sumayya wadda already har ta saka hijab dinta tana ganinsa ta dauki jaka, dama duk zaman asibitin ya ishe ta. Sai ya daukar mata daya jakar ya juya kallon Ruqayyah yace "mun tafi" yasan ta fahimci abinda yace, kamar ba zata tashi ba kuma sai ta yunkura ta tashi tana kokarin gyara karfen da aka saka mata a kafa, sai ya ajiye jakar hannunsa ya durkusa yana gyara mata sai ta ture hannun sa, a idonta yaga hawaye ya taru sai yaji babu dadi a zuciyarsa, tabbas ita din abar tausayi ce. Ya dago kai yana kallon ta cikin ido yace "am sorry" ta fahimci abinda yace daga motsin bakinsa, sai ta dauke kai ta mike tsaye ta fara tafiya tana jan kafa har ta bar dakin.

Ya juyo yana kallon Sumayya wadda itama shi take kallo fuskarta da alamun tausayi, tace "kayi hakuri, haka take very edgy. Yau kuma tafi kullum zama worst" ya gyada kai yace "ke zan bawa hakuri ai, zama da Ruqayyah a irin wannan yanayin nata sai ke din. I was selfish dana tafi na barki da ita. Ya kamata ace na zauna tare da ku" tace "babu komai, ai kana kokari ma tunda ba wai baka zuwa bane ba kullum kana kan hanya, sannan kana da abubuwa da yawa a gabanka" yaji dadin fahimtar sa da tayi sai ya dauki jakar itama ta dauki tata suka fita tare, suna hango Ruqayyah har ta danyi nisa, Hassan ya kara sauri dan ya kamota, tare suka isa gurin motarsaya bude mata ya sake kokarin taimaka mata wajen shiga amma taki karbar taimakon nasa ta shiga ita kadai ta zauna tare da rufe idonta.
Chapter 105 · 0% Book details