← Book details Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 134

Sashe 60

Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Automatically kanta ya motsa da alamar eh, ya saki fuskarta sannan ya dan buga kafadar ta yace "good girl" sai kuma yayi kissing side din fuskarta ya juya ya bar gurin. Ta lushe idonta tana jin zuciyarta data zama kankara tana narkewa ruwan yana taruwa a idanunta, ko a cikin mafarkinta bata taba tsammanin Hassan zai iya furta mata wadannan kalaman ba, yes, ta san he is strong tun sanda yana zuwa zance gurin ta amma bayan bikinsu, irin son da taga yana yi mata ta dauka ta kama shi a hannun ta, musamman a matsayin da take rike dashi na wadda tayi saving life dinsa ga kuma darajar abinda yake cikin ta. Ta dauka zai zabe ta akan kowa a duniya, amma shine ya furta mata to her face cewa yafi son Hussain akan komai, harda jaddada mata in yace komai yana nufin komai, harda misaltawa da abinda yake cikinta, wato ita bama ta cikin layin da Hussain din yake ciki.

Taji duk wani shiri nata yana kuncewa yana bin iska. Taji duk wani abu da yake kanta yana sauka kasa yana farfashewa. Taji duniya tayi mata zafi.

Tasa hannu da niyyar goge hawayen da ya taru a idonta amma sai taji babu. Ita dama haka take in ranta ya baci irin wannan to sai hawaye yaki zubar mata sai dai tayi na zuci. Sai dai in kukan karya ne to da gudu hawayen yake zuwa. Ta mayar da hankalinta zuwa inda Hassan yayi forcing dinta ta kalla taga Hussain har yanzu yana tsaye hannunsa rike dana Fatima suna dariya tare da wasu mutanen su da suka rako waje. Ta dauke kanta gefe tare da rufe idonta, mafarkin ta yana karasa tarwatsewa a gaban idanun ta.

Ta saki karfen, sannan ta juya tamkar kazar da kwai ya fashewa a ciki ta shiga dakin Hassan, ta jiyo motsin sa a toilet daga dukkan alama wanka yake yi sai ta fita daga dakin a ranta tana cewa "yau sai dai kaje ka rungume Hussain ba dai ni ba"

Dakin ta ta tafi ta yar da jakar hannunta a kasa sannan ta haye kan gado tana kara jin zafin maganganun Hassan a ranta. Tabbas sai ya san ita ya gaya wa haka, sai yayi nadama. Ta jima a kwance taji motsin shigowar Sumayya, sai ta jita ta murda dakin ta shigo da sallama. Bata motsa ba har tazo gaban gadon ta dan taba ta tana cewa "Ruqayyah ki tashi ki cire kayan ki mana, a haka zaki yi bacci? Kiyi wanka mana ki tafi dakin mijin ki" ta karasa maganar cikin nishadi, da alama tana cikin farin ciki, to mai zai hana ta farin ciki ita kuwa tunda bata da wani problem a rayuwa? Komai yana tafiyar mata yadda take so ga Adam kullum yana kara cika ta da kaunarsa?

Jin Ruqayyah bata ce komai ba yasa ta kuma taba ta, ta dauka bacci take yi. Sai taga ta bude idonta tana kallonta a take gabanta ya fadi, tasan irin wannan jan idon tasan irin wannan kallon, tace "Ruqayyah? Me ya faru?" Ruqayyah tayi juyi tana kara hayewa can saman gadon, tana jin kamar zuciyarta zata fito waje ida bata gayawa Sumayya ne yake damunta ba.

Sumayya ta zauna a kan side drawer tace "me ya faru Ruqayyah? Wani ne ya bata miki rai a gurin taron?" Ruqayyah ta dauke kai gefe tace "mijina ne, baya sona kuma yanzu, yace yafi son Hussain a kaina. Kamar yadda Baba yace yafi son ki a kaina" sai kuma hawayen suka fara zuba. Sumayya ta hau kan gadon ta jawo ta jikinta tana cewa "Ruqayyah, ba wai ke ce ba'a so ba kuma kema kin sani, duk muna son ki sosai da sosai kawai wasu daga cikin halayen ki ne ba'a so. Na tabbatar shima wani abu kika yi masa har ya fadi haka, amma son ki daban a ransa son Hussain kuma daban, ai ku din ba abu daya bane ba kowa da gurbin da yake zaune a kai" Ruqayyah ta fara kokarin kwace jikin ta daga Sumayya tana cewa "cewa fa yayi har abin da yake cikina zai iya hakura dashi saboda Hussain yayi murmushi, wanne irin so ne wannan? Wacce irin magana ce wannan?"

Sumayya tayi murmushi tace "Ruqayyah! Hassan duk duniya bashi da kamar Hussain kuma har a nade ta ba zai samu kamar Hussain ba. Abinda yake cikin ki kuwa zaku kuma samun wadansu har goma ko fiye da haka, kinga kuwa ai ba za'a taba hada soyayyar su a guri daya ba. Amma ke me kika yi masa haka da zafi har ya gaya miki wannan? Na tabbatar kin kure hakurin sa ne" Ruqayyah tace "dama ai ba hakurin ne da shi ba, fada ne dashi da saurin fushi. Shine har da yi min warning wai kar in kara gaya masa laifin Hussain baya son ji"

Sumayya tace "ai tun farko dama sai dana gaya miki, nasan duk boye boyen halinki da kike yi dole sai ya sani tunda shi hali ai baya boyuwa indai har za'a zauna tare ballantana zama irin na aure. Kin nuna masa ke mai hakuri ce da kawar da kai bayan kuma ba haka bane ba yanzu zafin zuciyar taki da mita kika nuna masa ko? Ni bansan halin maza ba amma nasan ko a matan ma ba kowa ne yake son zama da mutum mai mita ba. Ballantana har ki kai ga fadin aibun dannuwansa a gaban idonsa. Gaskiya baki kyauta ba, kuma duk abinda ya gaya miki ke kika jawo wa kanki. Amma nasan hakan daya fada ba wai dan baya sonki bane ba sai don yana so ya nuna miki cewa abinda kike yi din ba dai dai bane ba. Nima kuma na gaya miki ba dai dai bane ba, dan nasan yadda nake sonki nasan kuma ko menene zaki yi na rashin kyautawa ba zan so inji wani ya fada ba ballantana kuma in naji anyi miki sharri"

Ruqayyah ta dago kai da sauri "sharri? Au sharri nake yi masa? Bashi da son a sani ne da nuna wa mutane basu isa ba? Shi fa jinsa yake yi tamkar sama yake da kowa, jin kowa yake yi a kasan sa dan nayi kokarin ankarar da danuwansa shine nayi laifi? Dan shi fa nake yi ba dan wani ba, dan in kwato masa yancinsa nake yi badan komai ba" sai tayi shiru tana kallon hannunta, Sumayya ta gyara zamanta tace "gaya min, menene plan dinki? Me kike so kiyi archiving? What are you up to?"

Ruqayyah ta danyi tsaki fuskarta tana nuna bacin ranta ta share hawayen da ya rage a idonta tace "ke kinfi kowa sanin ban taba tunanin zan auri mutum kamar Hassan ba sai da na ganshi. Na kuma dora raina akan cewa kudin nan nasa ne, na riga na gama saka zuciya ta akan hakan. Bayan naga Hussain naso ace shine Hassan, naso ace shi zan aura, naso ace shine wanda na tarar ranar nan a toilet amma kuma na hakura na karbi Hassan din tunda a lokacin ina tunanin shi yake da kudin, yanzu kuma na fahimci suma kudin ba nasa bane ba" ya danyi tsaki tana girgiza kanta tace

"na tsani wannan Fatiman ta fiya iyayi da gulma da munafurci da nuna isa, na kuma fahimci Hussain yana matukar sonta, sannan yana son Hassan sosai" ta sake yin shiru kamar mai tunani sannan tace "I just want to be her. I want her husband, her house and her power" Sumayya ta zaro ido "Ruqayyah baki da hankali? Ta yaya zaki so mijinta bayan ga naki? Ta yaya zaki so gidan ta bayan ga naki? Ta yaya hakan zata yi wu?"

Ruqayyah tace "hakan ba zai yiwu ba na sani, na fahimci Hussain tun da nazo gidan nan na gane baya kaunata ko kadan, ko kallo ban ishe shi ba, bana jin ko babu Hassan a duniya Hussain zai kalli inda nake sai dai ko da niyyar taimako amma ba da niyyar aure ba. Wannan yasa na hakura dashi. Sannan nake so in mayar da Hassan shi ya koma Hussain din. So nake in mayar dashi CEO"

Sumayya tace "how?" Ruqayyah tace "niyya ta in hada rigima tsakanin Hassan da Fatima, ta hanyar amfani da abinda yake cikina saboda na fahimci irin son da Hassan da shi kansa Hussain suke yi wa cikina. So nake su yarda bata son abinda yake cikina yadda duk abinda ya samu cikin ita za'a yi zargi. So nayi in rura wuta tsakanin su ta yadda Hussain will be forced to choose between them kuma nasan cewa Hassan zai zaba duk kuwa da cewa rabuwa da Fatima zata yi destroying dinsa. And that destruction shi nake after. Idan ya zama ba zai iya cigaba da rikon kamfani ba dole Hassan will take over. Idan kuma something bad ya faru dashi komai ya zamana Hassan din"

Sumayya da mamaki ya ishe ta ta katseta ta hanyar cewa "something bad as in?" Ta daga kafada tace "babu wanda ya san gawar fari dan haka dan Adam babu abinda zai yi fata illar Allah ya bashi rayuwa mai tsaho" Sumayya ta dafe kanta tace "Ruqayyah wai kina nufin kima fatan Hussain ya mutu saboda Hassan ya samu gado" tayi shiru kamar ba zata yi magana ba sai kuma tace "kowa ma wata rana zai mutu ai"

Ruqayyah tace "exactly, hakan yana nufin kema zaki iya kwanciya yanzu gobe kuma ba zaki tashi ba. Shi kuma Hussain zai iya ya kara shekaru saba'in ko fite da haka a rayuwa. Dan Allah Ruqayyah ki gaya min cewa ba wai kina tunanin harming Hussain bane ba saboda dukiyarsa. Dan Allah Ruqayyah ki gaya min babu wannan tunanin a ranki"
Chapter 60 · 0% Book details