← Book details Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 132 OF 134

Sashe 132

Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin rawar murya yace "gimbiya Asma'u?" Kanwar Fatima ce wadda suke yanayi. Fatima taji zuciyarta ta amsa da jin sunan kanwar ta, taji ta kosa da taga iyayenta da yanuwanta, ta kosa taga dan jaririn ta. Tace "ba Asma'u bace Auwal, Fatima ce" sai ya saki bulalar dogarai da take hannunsa, ya sake matsowa yana kuma lekawa cikin motar sannan kuma sai ya zabura kamar wanda akayi wa allurar karfi ya fita a guje, bai bude kofar gate din ba sai ya wuce cikin gidan a guje, ba zai bari wani ya riga shi kai wannan maganar cikin gida ba.

Sai dai yana shiga gate din gida ya fara kururuwa "jama'a ku zo ku taya ni gani, gimbiya Fatima ce gata can a cikin mota tare da inyamurai. Jama'a kuzo ku tayani dubawa ko ido na ne yake yi min gizo" nan take mutane sukafara cincirindon zuwa inda yake wasu kuma suna wucewa bakin gate, sai dai daga zarar sun ga abinda ya gani sai su koma da baya suna neman suma wadanda zasu gayawa.

Ganin haka yasa Adam ya tafi da kansa ya bude gate din gidan sannan drivern ya shigo da motar suka zarce zuwa gurin da aka tanada dan packing din motocin baki. Suka bude suka fito su uku sannan Adam ya biya drivern, yana tuna lokacin da shima yake a matsayin drivern taxi.

Fitowar Fatima ya saka sauran mutane suka karasa hargitse wa, wannan hayaniyar ce Adam baya so shi yasa yayi plan din neman audiance da mai martaba sarki ko wani mai fada aji direct yadda za'a yi maganar a tsanaki. Baya son hayaniyar tayi affecting Fatimah, not now, not when ta fara samun lafiya.

Suka fara tafiya, Fatima tana yi musu jagora dan babu abinda ta manta a tsarin gidan nasu, Maman Adam tana rike da ita, supporting her, irin rikon da akeyi wa marasa lafiya. A haka suka doshi cikin gidan, duk inda suka wuce sai mutane su dare su basu hanya, wasu kuma su fita a guje. Har suka isainda Adam ba zai iya wucewa ba sai ya dakata yana jin kamar ya bisu amma babu dama dan haka yace "Mama" maman sa ta juyo tana kallon sa sai yace "take care of her please" sai tayi murmushi ta gyada masa kai ba tare da tace komai ba.

A cikin gida, a dan karamin shamakin da yake tsakanin bangaren Hajiya Fulani mahaifiyar Fatima da kuma Hajiya umma abokiyar zamanta, kamar kullum da yamma, yau ma suna zaune tare a karkashin bishiyar da take gurin suna shan fresh air tare da jin labaruka daga barorin su.

Hajiya Fulani kawai jinsu take yi amma bata fahimtar hirar da suke yi, ita yau bata jin dadi sosai gabanta sai faduwa yake yi, dama kuma ita ba lafiya xe ta ishe ta ba dan tun lokacin da labarin rasuwar yarta Fatima ya iske ta, ballantana kuma jin irin mummunar mutuwar da tayi, tun daga ranar har yau bata kuma kasancewa cikin farin ciki ba, bata kuma jin wani labari dazai saka ta farin ciki ba, bata kuma jin dadin rayuwa ba, tana yin rayuwa ne kawai dan da akwai rai a jikinta.

Sai da yawa ta kan ce "ni kullum sai inke jin kamar Fatima zata shigo gidan nan, har jin taku nake yi kamar nata" sau da yawa idan tayi wannan maganar sai mai martaba ko kuma duk wanda tayi wa maganar ya amsa mata da cewa "ai dama dole zaki ke jin haka, tunda baki ga gawar ta ba, kullum gani zaki ke yi kamar bata mutu ba zata dawo". In mai martaba ne sai ya kara da cewa "ni ma kaina dana binneta da hannu na ji nake yi kamar ba ita na binne ba, tunda babu sauran wasu kamannin ta a tare da ita".

Yau ma wannan feeling din take ji, kamar Fatima zata zo ta zauna a tsakiyar su kamar yadda ta saba yi in dai tana gidan. Takan ce "tsakiyar ku yafi dadin zama, in juya duk ta side din da nake so in kwanta akan cinya".

Hayaniyar da gidan ya dauka shi ya katse labarin da wata baiwa take basu, sannan kuma sai ga wasu bayi su biyu sun shigo gurin a guje kamar an koro su, jakadiya ta mike "kai! Lafiyar ku kuwa? Wanne irin rashin hankali ne haka?" Suka zube a kasa suna tuba sannan daya tace "wata mata muka gani yanzu mai kama da gimbiya Fatima" Hajiya Fulani ta mike tsaye, Hajiya umma ta mike itama tana tambayar "a ina? Ko yar uwa ce?" Sai suka ce "gasu nan zasu shigo nan gurin ita da wata mata, kowa gudu yake yi in ya gansu, kamar an tsaga kara ita da marigayiya".

Hajiya Fulani ta fara tafiya da sauri zuwa hanyar shigowa gurin daga waje, zuciyarta tana gaya mata Fatima ce ba mai kama da Fatima ba, kafin ta karasa su ka shigo, Fatima a rike a hannun Maman Adam. Kallo daya tayi mata tasan cewa yarta ce Fatima, tasan cewa gawar dasu Mai martaba suka binne bata Fatima bace ba.

A hankali Fatima ta saki hannun Maman Adam sannan ta mika wa Hajiya Fulani hannu tace "Hajiya ta, umma na na dawo gida"

Jin muryar ta ya tabbatar wa da Hajiya Fulani cewa Fatima ce, mai makon ta amsa mata ko kuma ta kama hannun data mika mata sai ta zame ta yanke jiki ta fadi.

Wannan littafin na siyarwa ne idan kika ganshi a wani guri na sata ne, in kina son ki sayi halaliyar ki ki yi min magana ta wannan number din through WhatsApp 08067081020

*Ina masu bukatar hadadu kuma ingantatun turarukan wuta da khumra masu dadin kamshi kuma a farashi me sauki to ga dama tazo muku Awwaba scent nada turarukan wuta humra burners kasko shisa coal dorot stool dilka body milk dadai sauransu masu bukatar na iya nemansu a whats app ko kuma kira ta wannan lambar 08034236800*
*bugu da kari duk wanda ya sayi humra ko turaren wuta a cikin wannan watan akwai kyautar dilka me kyau tafiyaya daga kasar chad wadda zata gyara jiki tay expoliating skin acikin minti 20 kawai ku garzayo dan kwasar garabasa*
*Adress kundila zoo road kano muna tura sako ko ina da iznin Allah**Back From The Dead*

Appreciate this please......
Cikin mintuna da basu kai talatin ba gaba ki daya gidan sarautar kano ya hargitse, masi gudu nayi cike da tsoro da fargabar sunga fatalwa, wasu kuma suna tahowa da gudu dan gani ya kori ji, suna so si tabbatar wa da idanuwan su cewa gimbiya Fatimah data mutu shekaru biyar itace yanzu ta shigo cikin gidan da kafafuwanta.

Fatima ta karasa cikin sassarfa ta durkusa a gaban hajiya Fulani tana girgiza ta kadan "Hajiya? Hajiya ta?" Umma da tun shigowar Fatima ta daskare a gurin ta matsa inda Hajiya Fulani ta fadi ganin cewa jakadiya da sauran barorin da suke gurin duk sun tsorata sun ki zuwa gurin. Ta jijjigata sannan ta dauko robar ruwa ta yayyafa mata tana kiran sunanta har suka ji ta sauke ajjiyar zuciya sannan a hankali ta bude idanunwanta, ta sauke su akan Fatima datake rungume da ita tana hawaye "Fatima? Fatima zahra ke ce wannan a duniya ko dai mutuwa nayi nima nake ganin ki a can?" Fatima tace "hajiya nice mana, baki gane ni ba ko? Na rame ko? Rashin lafiya nayi sosai. Nasan kuna ta nemana duk shekarun nan" sai ta kara kukan ta tace "nima ina ta neman ku Hajiya, ina ta so in taho gurin ku amma babu dama".

Umma da take jin su ta kamo hannun Fatima tace "mu bama neman ki Fatima, mu bamu taba neman ki ba ko sau daya saboda mu ce mana akayi kin mutu, mu a gurin mu kin mutu dan har anyiwa gawarki suttura an binne ki"

Fatima ta bude ido cikin mamaki, sai kuma ta waiga tana kallon yadda kowa a gurin yake kallon ta,wasu tana hango tsoro a idonsu. A lokacin Asma'u kanwarta ta shigo gurin, ita ma labari ya iske ta a dakinta cewa Fatima tayo fatalwa tana yawo a gidan, tana shigowa kuwa taga Fatima a durkushe kusa da iyayen su, ai kuwa sai ta zunduma ihu ta juya a guje, Fatima ta mike "Asma'u? Asma'u Fatima ce fa, Asma'u nice Fatima wallahi ba mutuwa nayi ba, karya ake yi min wallahi ban mutu ba" kuka yaci karfinta, tana jin zafi a zuciyarta cewa yan uwant data gama cin burin zuwa ta gansu ta rungume su taji dadi sune suke gudunta sun dauka fatalwa ce, wai ashe duk tunanin da take cewa babanta yana nan yana zazzage Nigeria yana nemanta ashe ba haka bane ba shi ya dauka bata duniya, for five full years, hakan yana nufin har sun fara mantawa da ita kenan. Hakan yana nufin badan Mama ta taimaka mata ba, da sai dai ta karashe rayuwarta a rufe babu mai zuwa cetonta kamar yadda da take tsammanin babanta zai yi bincike ya gano inda take sannan ya taimaka mata.

Sai ta juyo ta rungume Maman Adam, "Mama dan Allah ki gaya musu, ki ce musu wallahi ba mutuwa nayi ba ina tare daku, ki gaya musu su bar guduna ni ba fatalwa ba ce ba" kafin Maman tayi magana Hajiya ta tashi ta rungume ta, "ba sai kin rantse ba Fatima, ba sai kin nemo ma yi miki shaida bani nasan kece, tunda aka ce min kin mutu jikina yake bani kina raye kuma zaki dawo wata rana,ni na san bagawarki suka binne ba".
Chapter 132 · 0% Book details