Sashe 40
Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Har an fara fita ana shiga motocin da zasu tafi dasu airport sai Aunty ta kira Hassan dakinta suka tsaya tace "nace ka sallami Ruqayyah kuwa?" Yace "sallama kamar yaya?" Aunty tace "eh mana, zaka bata kudi sanoda liƙi da sauran abubuwa" ya zauna akan kujera yana dafe kanta "Aunty ita tace miki tana bukatar tayi liki? Shin wai ma menene amfanin yin likin? Yana daga cikin sharudan biki?" Aunty ta hade rai "to mu dai ko kayi mana wa'azi dai sai munyi, ya zamu je gidan biki gidan fitar kunya kuma na tabbatar za'a yi kida sannan kace ba zamu fita muyi wa amarya da ango liki ba? Ita kuma ya kake so tayi? So kake ta zauna ta zuba tagumi tana kallon mu muna yi?" Yace "Aunty, ke kinfi kowa sanin dalilin da yasa tuntuni naki auren yayan masu kudi saboda bana son macen data saba da barnar kudi da saka kaya masu tsada da sauran su, saboda a hala zata tarbiyyan tar da yaya na, a haka family na zasu tashi. Kuma babu wanda yasan abinda gobe zata zo mana dashi. Ni daban Hussain daban, kudi na daban na Hussain daban. Ranar da bani dashi kuma yaya zanyi dasu aunty? Shi yasa nayi murna da Allah ya hada ni da Hassana saboda background dinta da kuma halayyar ta sannan da yarintar ta yadda zanji dadin tarbiyyan tar da ita akan tsarin rayuwa ta ita kuma ta tarbiyyan tar da yaya na. To yanzu idan kuma na fara nuna mata zubar da kudi a kasa a gurin biki dole ne me akayi kenan? Ai anyi ba'a yi ba ko?"
Aunty tace "to mister smart, komai sai ka nuna wa mutane kai kamar ka fimu iyawa. Wannan dai biki ne, kuma har yanzu bikin ku ne ba'a gama ba, ka dauko kudin liki ka bata tun muna shaida juna ni da kai" yayi ajjiyar zuciya yana shafa aljihun sa sannan yace "i don't have cash on me, in na fita zan samu sai in bata" ta nuna masa kofa, "jeka daki ka dauko ka kawo mata ina nan ina jiran ka" yayi murmushi yana karya wuya, tace "ai na fika wayo, ni na haife ka fa ba kai ka haife ni ba". Dole ya tashi yana murmushi ya tafi tsohon dakin sa, ya bude drawer ya dauko kudi yana jujjuya, ya gama plan din abinda zaiyi da kudin nan, yayi tsaki sannan ya mike ya fita.
Yau dai sai ga Ruqayyah da Sumayya a jirgi. Ruqayyah ta maze wai dan kar tayi kauyanci ayi mata dariya amma lokacin da jirgi zai tashi ji tayi kamar dodon kunnen ta ne ya fashe a cikin kunnen, amma taki tabawa dan kar wani ya gani yace tayi kauyenci, ta kankame rigarta cike da tsoro amma fuskarta babu ko alamar tsoro a ciki. Ta shanye kayanta. Suna sauka suka tarar an aiko da motocin da zasu tafi dasu gidan sarautar kano, suka shiga aka kaisu sannan akayi musu jagora har masaukin su, daga nan aka shiga hidimar kawo musu abinciccika na alfarma irin na sarauta, wani kalar abincin ma Ruqayyah bata taba ganin sa ba. Nan take bayi da hadiman gida suka fara saving dinsu, daga kinyi motsi za'a ce "me kike so? Me za'a karo miki? Ko kafafuwan ki sun gaji a tausa miki su?" A haka har sai da aka tabbatar kowa is fully satisfied sannan aka yi musu jagora zuwa wani katon palo da yafi kama da hall din taro amma yasha shimfidu da kujeru na alfarma. Anan Ruqayyah take tambayar kanta ko wannan ce fadar? Amma kuma bata ga karagar sarki ba, sai taga an nuna musu kujerun suka zazzauna sannan sai ga matan gidan suna isowa daya bayan daya ana gaisawa dasu cikin mutunta juna da karramawa. Duk inda Aunty zata je hannunta yana rike dana Ruqayyah, duk Wadda suka gaisa kuma zata nuna mata Ruqayyah tace "ga daya ƴar tawa, matar Hassan ce, jiya aka kawo ta" nan da nan sai taga an jata an rungume "ga yar uwar Fatima" "Allah ya baku zaman lafiya" "Masha Allah, kyakykyawa daita kuwa, ya sunan ki?" A haka a haka har laasar tayi, Ruqayyah tana cewa "wato ita ogar ba zata fito ba ko?" Bakin cikinta kawai kar kwalliyar ta ta karasa lalacewa ba tare da Fatima ta fito ta ganta ba, kar ta raina ta, tunda taji ance first impression matters alot.
Ba'a fito da Fatima ba sai da suka je suka yi sallar laasar, dole Ruqayyah ta wanke kwalliyar ta tunda zata yi alwala amma duk da haka sai Nafisa ta dan gyara mata fuskar dai dai gwargwado kuma ta mayar mata da head dinta. Sannan suka koma suka zazzauna side daya dangin ango daya side din kuma dangin amarya, akayi ta rabon snacks da drinks daga can gefe kuma ga masu kidan kwarya nan suna yi . Sannan sai ga amarya nan an fito da ita lullube da alkyabba fara tas mai adon golden, ko tafin kafarta ba'a gani, aka zaunar da ita akan kujerar da aka tanada musamman domin ta sannan kawayenta suka zagaye ta duk sun sha ankon lace kalar zaren da akayi dinkin alkyabbar ta dashi. Kasanta kuma bayinta ne a jere duk sunyi ankon riga da zani na atamfa mai hoto da sunan ta a jiki. Hannayensu rike da shantu suna kida da cinyoyinsu sannan suna rera waka, a cikin wakar taji an ambaci sunan gimbiya Fatima, sannan ne ta fahimci wakar ma musamman saboda ita aka shirya ta.
Nan take guri ya tashi da sowa da tafi, wasu kananan yammata suka fito suma a jere hannayensu rike da mahutai wadanda side dinsu daya tambarin masarautar daya side din kuma hoton gimbiya fatima, suka jeru suna rawa gwanin ban sha'awa. Mutum biyu ne aka nema daga dangin ango suka je suka bude fuskar gimbiya sannan suka feshe ta da turare, duk da haka sai ya zamanto rabin fuskar ne kawai a bude idanuwan ta da goshinta still suna rufe, amma duk da haka zaka iya hango tsantsar kyawunta ta bakinta da yake dauke da murmushi da kuma dogon hancinta da yake tsaye chas. Ruqayyah tayi tsaki a ranta. "Ashe ma na fita hasken fata" ta fada a hankali tana hararar iska. Sai dai ita kanta tasan koda tafi Fatima haske to kuwa kulawar da fatar fatiman ta samu ba zai bar hasken Ruqayyah ya haska ba.
Daga nan sai taga an fara shigowa da kaya ana jere wa a tsakiyar gurin wai kayan gara ne, amma abin mamakin shine ba wai kayan abinci bane ba kamar yadda tasan ana yin gara aa wannan kayan suttura ne kawai, akwati akwati, jaka jaka. A al'adar gidan sarauta duk wadda aka yiwa aure a gidan sarauta idan wani gidan sarautar aka kaita to kuwa hatta bayin gidan sai an yi musu suttura kuma an basu kudi albarkacin ta, idan kuma ba gidan sarauta bane ba to kuwa za'a binciko duk dangin angon na nesa dana kusa sai kowa ya samu rabonsa albarkacin gimbiya, yan uwansa shakikai kuwa da iyayensa da gwoggonninsa nasu na musamman ne, sai an yi musu kamar wani karamin lefe. Haka akayi ta kiran sunan tun daga iyayen Hussain dangin uwa da dangin uba har zuwa kan dangin dangarere, wasu ma basa gurin, wasu ma ko kadunan basu je ba ballantana kano amma an kira sunan su kuma an basu rabon su, kowa aka bashi kaya kuma sai an hada da kudi, maza da mata.
A cikin rabon sai taga na Hassan, sunanshi na biyu daga Aunty sai shi, akwatin sa guda mai cike da dangin shaddoji masu tsada, da yar karamar jaka ita kuma takalma ne a ciki da huluna da turaruka na maza. Tunda babu maza a ciki dan haka ita aka ce taje ta karbo masa, ta taka kaje har gaban gimbiya, ita bakin cikinta kenan wai sai anje gaban gimbiya, ta tsaya a gefen gimbiya akayi musu hoto sai mai hoton ya yi mata magana da cewasai ta sunkuya saboda ita gimbiyar a zaune take, ita kuma Ruqayyah a ganin ta in da sunkuya kamar gimbiyar ta sunkuyawa amma ganin mutane suna kallo dole ta sunkuya din tana kirkirar murmushin karya aka sake daukan wani. A lokacin da zata bar gurin ne taji gimbiyar ta riko hannunta tayi mata alamar data sunkuyo, bakin ciki ya toshewa Ruqayyah makogwaro, amma dole ta sunkuya sannan ne suka hada ido, da murmushi a fuskar gimbiya fatima, ga wani fitinannen kamshi yana tashi daga jikinta tace "ban san dake aka zo ba ai, da tun dazu na aika an kawo min ke gurina, ke bakuwa tace ai bata mutan gida ba" Ruqayyah tayi yake "yeah right" sannan ta zare hannun ta ta bar gurin, ko ta kan kayan bata bi ba. Ita sunkuyawar da tayi wa gimbiya shi yafi komai kona mata rai. Tana dawowa ta fara sansana kanta dan taji ko tana irin kamshin da gimbiya fatima take yi?
Abin takaici sai gashi tana zama an sake kiran sunanta again, wannan karon kuma nata kayan taje aka bata, exactly zubin da akayi wa Hassan irin sa akayi mata kawai dai nasa na maza nata na mata. Wannan karon da akace taje suyi hoto cewa tayi ai tayi, tayi tafiyar ta.