← Book details Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 134

Sashe 78

Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wannan littafin na siyarwa ne, in kika ganshi a wani gurin na sata ne. In kina so ki karanta halaliyar ki kiyi min magana through WhatsApp ta wannan number 08067081020*Dear Baby*

Not edited

Kafin Hassan ya dawo dakin har nurses din sun gama da Hussain sun fita, yana shigowa Hussain yabi fuskar sa da kallo sannan ya bude hannun sa yace "now what?" Hassan ya jawo kujera ya zauna yana kallon sa yace "zamu tafi Nigeria gobe da safe insha Allahu" maimakon Hussain yayi murnar cewa Hassan ya goyi bayan tafiyarsu sai fuskarsata nuna madaukakiyar damuwa, yace "me ya faru? Dawa kukayi waya yanzu?" Hassan ya gyara zama yana kallonsa yace "Aunty ce, ta kira tace duk abinda muke yi mu koma gida yanzu" ya dan sosa kansa "wani gidan tv dazu yayi broadcasting cewa baka da lafiya, sun fadi ciwon da yake damunka da kuma asibitin da kake kwance" Hussain ya mike "what?" Hassan yayi shiru bai ce komai ba. Sai Hussain ya mike, ransa a tsananin bace ya doshi kofar fita yana huci, Hassan ya mike shima da sauri ya rike hannunsa yana cewa "me zaka yi? Ina zaka je?" Hussain yace "zanga management na asibitin nan ne, zanji dalilin da yasa suka yi releasing information dina to the press bayan sunyi min alkawarin secrecy" Hassan yace "how do you know cewa sune? Anything can happen. Yanzu mutane sun koma kiwon mutum bana dabba ba. It ca be anyone har wadanda ba zamu taba zarga ba" Hussain ya juyo yana huci yace "waye to? Hatta iyalan mu basu san abinda yake faruwa ba mu kadai muka sani sai asibitin nan, dan haka dole sune suka fitar da bayanin nan. Wallahi sai na yi sueing dinsu, wannan ai keta privacy ne. Allah kadai yasan dawa dawa ye suka ji labarin nan a yanzu" sai kuma ya dawo ya zauna akan kujera yana dafe kansa yace "Fatima! Oh my God" ya mike da sauri ya fara neman wayarsa. Hassan ya riga shi gani sai ya dauke ya saka a aljihun sa yace "don't worry about Fatima, she is fine, yanzu ka shirya zanje in karbar mana takardar sallama gobe mu tafi" Hussain yace "ba zan kai gobe a kasar nan ba. Bani waya ta. Bana so inyi fada da kai Hassan ka bani wayata in kira Fatima" Hassan bai ce masa komai ba sai ya kuma yi. Hanyar fita yana cewa "yau ko ni ko mai asibitin nan sai ya gaya min uban da ya bashi damar fitar da information dina" Hassan ya kuma rike shi "Hussain, take this easy, zata iya yiwuwa basu bane ba, akwai patients a asibitin nan kuma nasan a cikin su ba za'a rasa wanda suka zo daga Nigeria ba, ba za'a rasa wanda ya san fuskarka ko tawaba especially yadda kake watsa hotunan mu a media, wani zai iya gayawa wani, shima wanin ya gaya wa wani har maganar taje gurin yan jarida su kuma duk abinda zai dauki attention din mutane shi suke so su buga. Creating scene a asibitin nan ba zai gyara komai ba sai dai ma ya bata. Maybe yan jaridar suna waje suna kallon mu, maybe suna daukan hoton duk wani motsin mu, creating scene zai kara musu labarin da zasu buga ne, abu kadan yanzu suke nema su kara gishiri da magi su sake bugawa" Hussain ya juyo ya dawo dakin yana zura hannunsa a cikin gashin kansa, ransa a matukar bace. Ya juya bayansa ya dora goshinsa a jikin bangon dakin. Ko wanene wannan in ya kamashi Allah kadai zai raba su, it pains him that someone will make use of ciwon da yake yi ya in this way. Ko waye yayi wannan abin ko me yake tunanin zaiyi gaining???

Hassan ya kama shi ya zaunar dashi a bakin gado yace "na kira airport, babu jirgi zuwa Nigeria a yau, tomorrow da sassafe zamu tafi" Hussain ya dago kai yana kallon sa, sai Hassan ya mika masa wayarsa yace "call her" Hussain ya karbi wayar yana jujjuya ta, shi bai ma san me zaice mata ba idan ya kirata din. Ya san dole dama zata sani tunda zata ga tabon surgery din a jikinsa but so yayi ace shi zai gaya mata da kansa at his own convenient time, har ya gama shirya kalaman da zai yi mata yadda ba zata tayar da hankalin ta sosai ba, amma yanzu bai ma san ta inda zai fara ba. Ya runtse idonsa sannan ya ajiye wayar a gefensa. Hassan ya mike yana dan bubbuga kafadar Hussain da niyyar bashi courage, sannan ya nemi huka ya saka ya dan rufe fuskarsa kadan sannan ya fita daga dakin.

Hussain ya jima a zaune a inda Hassan ya barshi, zuciyarsa tana yi masa zafin abinda aka yi masa, sai kuma ya dauki wayarsa ya lalubo number din Fatima ya tura masa text
"am sorry"

Hassan ya je ya shigar da complain din abinda ya faru ga management din asibitocin, sannan kuma ya nemi a basu sallama. Farko doctor din da yake kula da Hussain ya ki amincewa da hakan amma kuma da yaga Hassan din ya dake har yana threatening kai karar asibitin sai ya hakura sai dai amma sai da ya hada su da wani doctor a Nigeria wanda zai cigaba da monitoring lafiyar Hussain din tare kuma da yarjejeniyar cewa bayan wata uku Hussain xai dawo a sake gwada shi, kuma kafin nan in dai ya ji wani chanji a tare dashi zai dawo. Hassan duk ya amince, suka gama komai aka bashi takardar sallama.

A dakin ya dawo ya tarar da Hussain a kwance akan gadon ya rufe idon sa, ya zauna a kusa dashi, sai ya bude ido yana kallon sa yace "ko da wani ya ganninko kai a asibitin nan ba lallai ne yasan takamaiman me yake damu na ba, zai dai san cewa bani da lafiya, sai dai in asibitin su zadu fadi me yake damuna" Hassan yace "Hussain......it doesn't matter. Let it go please...." Hussain ya tashi zaune yana kallon Hassan yace "babu wanda kuka yi maganar dashi?" Hassan ya girgiza kansa yace "babu" Hussain yace "ko Ruqayyah?" Hassan ya bata rai yace "what? Kana zargin Ruqayyah? Shikenan kuma dan baka son ta jinin ku bai hadu ba sai ya kasance duk wani bad abu zata iya aikatawa? Hassana ba zata taba aikata wannan aikin ba, ballantana ma ban gaya mata ba. Nasan abinda nake yi ai" Hussain ya koma ya kwanta ya mayar da idonsa ya rufe, yayi alƙawarin ya daina fada da Hassan, but zuciyarsa tana kan Ruqayyah. Hassan ya cigaba da magana. "ko da ace na gaya wa Ruqayyah ba zata taba aikata hakan ba, kar ka mata secondary school kadai ta gama, bata da wata exposure a rayuwa, bana jin ma tasan ta yadda zata fitar da maganar" Hussain yana kwance still idonsa a rufe yace "kace baka gaya mata ba, case Closed".

A ranar suka bar asibitin, washegari da sassafe suka dauko hanyar Nigeria bayan sun kira Aunty sun gaya mata cewa gasu nan tahowa. Sai a lokacin suka samu labarin cewa Hassana ta haihu, ashe itama taga labarin kuma tashin hankalin ne ya tayar mata da nakuda ta haifi danta namiji, lafiya lau take sai dai jinin ta da ya hau sosai dan haka tana asibiti har lokacin.

Kowa yaje taryen su a airport amma banda Fatima, duk kuwa da cewa an sallame ta daga asibiti amma har lokacin kuka take yi musamman da ta ga message din Hussain da yake bata hakuri, hakan yana nuna mata cewa abinda aka fada gaskiya ne kenan, shi yasa tayi zamanta a gida dan bata jin kafafuwanta zasu kaita airport din.

A airport din ne kuma suka tabbatar da cewa maganar ta watsu sosai, dan sun ga yan jarida suna ta daukan su hotuna amma sai suka share suka nuna kamar basu lura dasu ba. Hussain ya bi dukkan yan uwansa ya rungume su daga bayan daya, yazo kan Ruqayyah sai ya karbi twins a hannunta yace "welldone babbar yaya" tayi murmushi tace "barka da dawowa gida" ya juyi yana kallon Hassan yace "ga mijin ki nan na dawo miki dashi in one piece kamar yadda nayi alkawari" tayi faffadan murmushi, sai yake ji a ransa kamar murmushin nata yafi karfin na ganin mijinta, kamar a can cikin idonta akwai wanda boyayyen abu. Daga airport din asibiti suka wuce gurin Hassana, suka duba ta suka kuma ga sabon dansu. "Hussain ya rike hannunta yace "kin ganni lafiya kalau ko? Kar ki kuma tayar da hankalin ki akaina girlfriend" haka yake ce mata tun suna yara, ta goge kwallar idonta, "amma ai gashi nan naga duk ka ka rame boyfriend" yayi dariya yace "ke kuma kinyi kiba ba, wa ya sani ma ko ke ce kike tsotse ni?" Ya fada cikin tsokana dan yasan bata son ki ba kwata kwata, ta bata rai "bata kiba nayi ba yaya H2, kumbura nayi kuma zan sace ne kafin suna". Ya zauna a kusa da ita tmya dauki babyn yana yi masa addu'a, sai yaji a ransa yana fatan inama inama.

Basu dade ba suka tafi gida saboda ita ma yanzu ake shirin sallamar ta tunda bp din ya fara normalizing, kuma shi hankalin sa duk yana kan Fatima musamman saboda ganin yadda tunda suka zo Ruqayyah take makale da Hassan. Shima sai yaji yana son yaji tashi matar a jiki sa. Sai dai yasan akwai drama a tsakanin su.
Chapter 78 · 0% Book details