Sashe 44
Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Suna nan zaune har Hassan yazo, suna jiran suga ya zo da motoci kanar yadda Hussain yazo dashi sai gashi daga shi sai Jabir. A palon sama suka zauna sannan Hassan ya kira wayar Sumayya yace mata gasu sunzo. A dole suka fito da Ruqayyah daga toilet suka kara gyara ta sannan suka lullube ta da mayafi suka fita da ita, sai taji a ranta cewa bata son mayafin ta irin alkyabbar gimbiya take so. Suka zaunar da ita a gefe sannan suka zagaye ta suna gaisawa dasu Hassan. Minal tace "ina sauran abokan?" Jabir yace "gani!" Tace "gaskiya kayi mana kadan kai kadai, ai munfi son da yawa yadda zamuyi ciniki sosai" yayi dariya yace "ciniki kuma sai kace wani kayan gabas?" Tace "ina jin dai ba ka kalli amaryar nan sosai ba, ai ta wuce kayan gabas ma ita" yace "wannan kuma sai dai a tambayi ango, ni ina ni ina kallon matar mutane?" Hassan ya dan leka kasan mayafin Ruqayyah yace "kinyi gaskiya, ta wuce kayan gabas, ta wuce kaya baki dayansu. Ni a gurina ta wuce komai fa. She is soo PRECIOUS to me" duk suka kwashe da shewa daya ta miko wa Hassan hannu tace "to kawo, tunda dai ka yaba sai ka biya" ya koma ya kwanta a jikin kujera yace "wanne biya zanyi kuma? Bayan na riga na biya sadaki ai na gama komai" tace "sadaki wannan nata ne, wannan kuma mu zaka sallama" Jabir ya zaro kudi daga aljihun sa wanda dama ta riga ya tanada saboda su ya ajiye a kan cinyar ta kusa dashi yace "duk tsadar ku dai wannan ya ishe ku" Minal ta dauka tana kimasta adadin kudin tace "wannan din, haba dai, kar ku bada mu mana, a matsayin sa na the whole CEO of H and H ai mota muka saka ran zai sallame mu da ita".Duk kawayen suka yi shiru suna kallonsa kamar yadda shima yake kallon su daya bayan daya, sannan suka juya suka kalli Ruqayyah, shima ya juya ya kalleta duk da fuskarta tana rufe da mayafi. A hankali Ruqayyah ta saka hannu ta kamo hannun Sumayya ta rike a cikin nata, kamar me neman karin courage daga gareta. Minal ta sake cewa "wai kana nufin ba kaine CEO ba?" Hassan yace "ke waye ya gaya miki nine?" Jabir ya dafa kafadar Hassan yana kallon Minal yace "to ke menene naki a ciki? In shine in ma bashi bane ba ina ruwanki? Ku dai ba kudin siyan baki kuke so ba kuma gashi an baku?" Wata a kawayen tace "to ai matar tasa ce ta gaya mana shine CEO, wannan yasa muka fitar da kudi masu yawa muka yi kwalliya da sauran abubuwa dan kar azo aji kunya, kuma dan muna saka ran zamu fanshe kudin mu a jikin ku, yanzu kuma gashinan daga dukkan alamu ashe yaudarar mu tayi bashi bane ba ko kuma shine yake boye mana dan kar ya bamu abinda muke nema. Mu kuma ba za mu bar gidan nan ba sai an bamu mota"
Hassan yayi kokarin mikewa, ransa yana baci zuciyarsa tana baƙi, bai taba tsammanin yadda yake jin farin ciki a ransa lokaci daya zai iya komawa baƙin ciki ba. So yake ya kira security din gidan su zo su fitar musu da wadannan marasa kunyar yaran masu niyyar haddasa musu fitina a daren farkon auren su. Jabir ya sake rike shi fuskarsa da murmushi yace "to ke yanzu baiwar Allah da kike ta wannan jawabin akan lallai sai an baku mota in aka baku din me zakuyi da ita? Ku kusan goma sharing zaku ke yi?" Tana juya idonta tace "siyarwa zamuyi mana, mu raba kudin ko ma samu na kashewa zuwa wani lokaci" Jabir yace "shikenan, yanzu wata a cikin ku ta turo min account details dinta sai in tura muku kudin motar ku" Hassan yayi sauri zaiyi magana Jabir ya sake yi masa alamun yayi shiru da hannunsa. A take suka bashi kuma a take ya tura musu kudin. Yana shigar musu suka duba "ahhh wannan ai sai dai karamar mota zamu siya" yayi dariya yace "ku da ya kamata ku gode min na taimaka muku ba sai kunyi wahalar neman mai siyan mota ba? Kuma in kuka tashi siyarwa tayin wulakanci za'a yi muku ba lallai ne ma ku samu irin wannan kudin ba. Yanzu kuwa babu ruwanku da jira, kafin kuje gida ma zaku iya raba abin ku" da haka ya shawo kansu suka yadda, sannan suka dan saya fuskar Ruqayyah kadan yadda za'a gani. Jabir ya dan leka fuskar yace "to amarya, Allah ya sanya alkhairi, sai nazo cin ta tsotse" ya mike yana mikawa Hassan hannu "ango, Allah ya bamu alkhairi, na yi maka wannan yakin saura kai kuma kayi naka" ya fada da dariya a muryarsa amma Hassan bai mayar masa da dariyar ba kuma bashi da niyyar rama wasan da yayi masa. Minal tayi wa Jabir fari da ido tace "kuma tafiya zaka yi, ko dan ragin hanya babu?" Yace "rufa min asiri kar matata tayi min duka, sai dai ku fito a samo muku driver ya kai ku har gidajen ku, amma ni yanzu ma kira na take tayi nayi dare" ya fada yana duba wayarsa duk da babu wani missed call a kai.
Suka kwashi tarkacen su ba tare da wata kyakkyawar sallama ga Ruqayyah ba ballantana ga mijinta daya tasa ta a gaba yana kallon ta , fuska babu walwala. Suna fita gidan yayi tsit kamar an kawo sakon mutuwa. Sumayya ta cire hannun ta daga na Ruqayyah tana jinta totally out of place ta mike. "Tooo da haka haka, nima bara in kara gaba" Ruqayyah ta sake rike mata hannu "ba sai gobe zaki tafi ba? Dare fa yayi sosai" ta sake zare hannunta daga nata tace "ai ina da me kai ni, tun dazu ma yana waje yana jirana" ta fada tana kallon fuskar Hassan tana jiran ya bata amsa tunda yasan wanda take nufi amma sai taga ko kallonta bai yi ba. Ta shiga daki da sauri ta dauko jakarta ta fito sannan tace musu sai da safe ta sauka da sauri tun kafin bomb din ya tashi da ita, tana fita taga Adam a tsaye a jikin mota yana danna wayarsa, ya dago kai yana kallon ta yace "I thought you are never coming out" tace "kai dai tunda na fito shikenan" bata jira ya buɗe mata kofa ba ta bude baya ta saka jakarta sannan ta bude gaba ta zauna. Ya shiga ya kunna motar suka bar gurin, ta juya tana kallon gidan Hassan a ranta tana jin kamar wani ticking bomb ne a gidan wanda zai iya exploding any time. Ta san dama shi ramin karya kurarre ne amma bata san zai kure tun a ranar farko ba. But something yana gaya mata Ruqayyah will find a way out of this.
Sun jima a zaune, ita kanta a kasa, hannayenta a kan cinyarta, shi kuma yana facing dinta ya jingina bayan sa da jikin kujera. Studying dinta yake yi, amma sai ya kasa karantar fuskarta, so yake ya hango guilt ko kuma tsoro ko kunya amma bai ga komai ba sai dan guntun murmushi a fuskarta. Ta danyi gyaran murya yace "CEO? Really?" Ta dan dago fuskarta ta kalle shi sai ta mayar da kanta kasa tace "ceo? Menene ceo?" Ya bata fuska yana jin confusion yace "kawayen ki suka ce kince nine CEO na H and H" ta daga kafada tace "ba fa kawayena bane ba, ni kasan ba kawaye ne dani ba, da za'a yi bikin ne Sumayya da Minal suka gayyato su dan su tsaya a matsayin kawayena tunda bani da kawaye" yace "wacece Minal?" Tace "yar makotan muce a wancan gidan, wadda ta zauna anan" ta fada tana nuna inda Minal ta zauna. Ya sake cewa "amma suka ce kince musu nine CEO?" ta danyi dariya tace "ni fa na ce maka bansan abinda hakan yake nufi ba" yadda ta fadi maganar so innocently ya sa ya fara yarda da ita, to ita ina zata san wadannan business terms din? Yanzu fa ta gama secondary school kuma ga yanayin gidan su. A ina zata san me duniya take ciki? Yace "amma da suka fada me yasa baki karyata su ba a gabansu, duk da baki san term din ba sai ki musa ki ce ke baki fada ba, dan nan gaba kar su sake yi miki karya" ta dan sunkuyar da kanta tana dan rufe fuskarta kamar mai jin kunya tace "siyan baki na fa akeyi, in ana siyan baki fa ba'a magana" ya dafe kansa da hannu biyu yana jin kansa yana neman fara ciwo. Zuciyarsa da kwakwalwar sa suna yaki a tsakanin su, but son Ruqayyah yana rinjayar sense dinsa. Ya cire hannun sa daga kansa sannan ya taso ya dawo kusa da ita ya zauna. Ya kamo hannun ta ya rike a nasa, ta sunkuyar da kai cikin jin kunya tana kokarin karbe hannunta amma yaki cikawa sai ta bar masa.