← Book details Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 134

Sashe 62

Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ruqayyah tayi shiru tana kallon Minal, abubuwa da yawa suna yawo a cikin kwakwalwar ta zuciyarta tana rabuwa kashi kashi, ta girgiza kanta. "Minal tsoro nake ji, irin wadannan malaman da su da bokaye duk tafiyarsu daya. Baki san wanda yasan Alqur'ani yasan irin sirri kan da ke cikin sa kuma in zuciyarsa bata da kyau to there is no limit to what he can do ba? Kuma wadannan laifin su yafi na boka muni ba? Kinga kakan mu, Malam Shehu? Babu abinda ba zai iya yi da ayoyin Alqur'ani ba amma baya yi din, ya zabi yayi aikin alkhairi dasu saboda ya zabi lahirar sa akan duniyar sa, inna Ade ma haka, ko kin san Inna Ade tafi baban su ilimin Alqur'ani? Amma ta zabi ta koyar da shi ga mutane saboda shine abinda take so. Nima nasan iya kacin abinda na sani, banbanci na dasu shine ni ina so in samu duniya sannan itama lahirar in samu yayinda su kuma suka ajiye duniyar a gefe suke neman lahirar. Duk iskanci na Minal bana wasa da ibada ta, ba zance bana zunubi ba dan ina yin karya da sauran kananan zunubai amma ban taba aikata wani a cikin manyan zunubai ba kuma ba zan fara ba. Kinga zuwa gurin boka ko malamin tsubbu to shirka ce, ita kuma shirka ita ce oga kwata kwata saboda in kayi ta tamkar ka bar addini ne, wanda kuwa duk ya bar addini kuma ya mutu ba tare daya dawo hanyar dai dai ba to ya mutu a kafiri. Ni kuwa Minal ba zanso in mutu a kafira ba bayan ita kanta duniyar ba samunta nayi ba, two zero kenan".

Minal tayi tsaki tace "ke kam ana baki kina kin karba. Na gaya miki ba boka bane ba kuma malamin tsubbu bane ba. To gaya min, shi Malam shehun da kike yin magana akan sa mutane basa zuwa gurinsa ya taya su da addu'a akan wani abu daya shige musu duhu ko wani abu daya taso musu?" Ruqayyah tace "suna zuwa mana" Minal tace "exactly, shima wannan haka yake. Na gaya miki sunayen Allah kawai zai kira sai kuyi addu'a ku shafa shikenan. Kinsan ita addu'a baki baki ne, wani yana yi kamar yankan wuka haka take wani kuma sai yayi tayi bai samu nasara ba. Ke kina yi shima can yana yi miki shikenan" Ruqayyah dai tayi shiru tana tunani sannan tace "baya duba kasa?" Minal tayi dariya tace "babu kasa ma a gidan sa. Charbi kawai zaki gani da Alqur'ani a gaban sa".

Ruqayyah tace "shikenan, zan zo muje din amma in naga wani abu da bai kwanta min ba zan gudu, ehe, dan ba zan zo duniya a banza in koma a banza ba sannan in tarar da can din ma wayam"

Sai suka shirya plan akan cewa Ruqayyah zata je gidan su ta kai musu tsarabar tafiyar da tayi, daga nan zata ce zataje gidan su Minal din ta kai mata tata tsarabar daga nan zata wuce gida. In yaso sai suje gidan malamin tare.

Bayan tafiyar Minal ne Ruqayyah ta shiga kitchen dinta. Yau ne rana ta farko data shiga kitchen din da niyyar girki, ta bude freezer taga akwai naman da bata ma san lokacin da aka zuba shiba, sai data tambayi yan aikin ta suka gaya mata ranar da zasu dawo Aunty ta aiko aka zuba musu duk kayan amfani a kitchen dinsu. Ta bude store taga akwai kayan garar ta suna nan suma jingim dan babu wanda aka raba wa duk zuba musu kayan su akayi a store. Har da drinks a jere a gefe wanda shima aka ce aunty ce ta aiko da shi.

Tayi shiru tana tunanin me ya kamata ta dafa ne, in dai har zata bi maganganun Minal to dole ta koyi abubuwa da yawa a ciki kuwa har da girki dan ta rike Hassan a hannunta. Ta tuna Fatima tayi mata alkawarin zata koya mata girki in sun dawo Nigeria amma yanzu kuwa anya in taje zata kulata? Maybe ma ta bita da bakar magana. Ta danyi tsaki, gaskiya lamarin nan sai ta dage sosai sannan zata cimma burinta, ita zuciyarta a kusa take, ita bata iya munafurci ba shi yasa har suka fara harbo jirgin ta. Amma dole ta koya koda kuwa a gurin Hassan ne dan dama shi tun tana gida take rufe shi a bai bai kuma yake rufuwa yanzu ne dai kawai frustration dinta akan Fatima ya saka ta fara bude masa kanta shi kuma a take ya buga mata warning.

Ta kalli yan aikin tana realizing ita ko sunayen su ma bata tsaya ta wani rike ba, tace "wace ta iya girki a cikin ku?" Duk su biyun suka ce sun iya. Tace "to ayi mana girki, tuwon shinkafa miyar agushi a saka nama sosai" suka ce shikenan ? Ta daga kafada tace "eh shikenan" sai bayan ta tafi sai ta tuna ai yan gayu abinci ba kala daya suke yi ba ko? Kamar har da snacks ake hadawa da kuma dan farfesu haka. Sai ta koma ta gaya musu suyi farfesun kaji sai su saka naman kasuwa a cikin miyar. Suka gaya mata babu fresh kayan miya sai markadaddu, babu kuma kayan kamshi, ta koma sama ta dauko kudi ta basu tace su bayar a waje wani ya siyo. Tayi kamar zata zauna suyi aikin tare, maybe ta koyi wani abu, amma sai ta kasa zaman kar su fahimci bata iya ba su raina ta. Ta debi drinks ta tafi dasu sama ta zuba a fridge din daya ke can ta kunna sannan ta koma dakinta ta gyara inda suka bata ita da Minal ta shiga toilet tayi wanka ta fito ta shirya cikin riga da skirt na atampa wanda daya ne daga cikin dinkunan da ta bayar kala ashirin kafin su tafi honeymoon. Tayi kwalliya irin wadda taga Fatima tana yi, daurin dankwalin ma shigen nata tayi. Sannan ta saka awarwarayen gold kamar yadda taga tana yi sai tayi sallar azahar sannan ta koma kitchen din ta tarar sun kusa gama abincin. Sai ta dawo sama ta kunna tv tayi kwanciyar ta akan kujera tana danna wayarta. A lokacin ne taga an saka ta a sababbin groups, ta kuma fahimci aikin Minal ne, taga wata ta aiko a bata shawara akan uwarmijinta da ta sako ta a gaba, mutane kowa yana fadar albarkacin bakinsa wasu suna bata shawarar da hatta ita Ruqayyah ta fahimci ba dai dai bane ba wasu kuma suna bata shawarar dai dai, masu cewa tayi addu'a kuma suna ta fada. Tayi shiru tana ta lissafi, tabbas social media guri na na samun abubuwa da yawa, alkhairi da sharri dukka, ya danganta da menene a zuciyar mutum.

Tana nan a zaune yan aikin suka hawo da abincin suka shiga dashi dining room sannan suka tambayeta in akwai wani abu kuma, da hannu tayi musu alamar suje kawai, har laasar tayi sannan ta tashi ta koma daki tayi sallah tana jin anya kuwa zata iya cigaba da jiran Hassan dan ita yunwa take ji already, sai ta tunawa kanta da cikin da yake jikinta dan haka tana fitowa ta tafi gurin abinci ta bude zata zuba. Kallo daya ta yiwa tuwon tasan bai tuku ba, tana saka shi a plate kuwa ya fara tarwatsewa. Tayi tsaki tana jin ranta yana baci, ta tuno da tuwon da taci ranar nan a part din aunty wanda ko kwayar shinkafar baka gani a ciki. A bude miyar taga babu laifi a ido, ta dan zuba tana ci taji gishiri yayi yawa. Ranta bai kara baci ba sai data bude farfesun. Gaba ki daya kazar ta narke romon kuma yayi ruwa tsululu. Ta zauna ta zuba tagumi, yanzu ya zata yi kenan? Ita da taso in abincin yayi dadi ta nuna masa kamar ita ce tayi? Wannan ai ita suka bawa kunya.
Chapter 62 · 0% Book details