Sashe 85
Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai dai duk wannan abin da take dasu bai saka saka farin ciki a zuciyarta ba, kullum ranta babu dadi zuciyarta bakikkirin musamman inta lissafa taga plans dinta duk babu su, Adam din ma da take ta kokarin ganin ta raba shi da yar uwarta har yanzu abin ya gagara sai kara samun karbuwa yake yi a gurin iyayensu da kuma a gurin Hussain, hatta Hassan din data juya wa ra'ayi akan Adam yanzu ya fara chanjawa dan kwana biyun nan har hira taga suna zama suyi su kuma yi dariya. Ta saka ta warware ta kuma saka wa ta kuma warwarewa amma har yanzu ta kasa samun mafita. Then one day, bayan Hussain din ta yayi wata daya a duniya sai taga Hassan yana aiyukan files din staff din da suke dasu a gidan, kowa da file dinsa tun daga kan masu gadi har zuwa masu ban ruwan fulawa. Ta zauna tana taya shi sorting, yana ware wasu wadanda yake so zai yiwa karin albashi a ciki har da Adam, ta miko masa file din ya bude yana going through, anan ne idonta ya sauka akan sunan Adam na gaskiya da kuma address din gidan iyayen sa mahaifa. Anan wani plan ya fara forming kansa a zuciyarta. Bata ce komai ba har suka gama aikin sannan ta tafi dakin ta. Ta kira Minal a waya "Minal ya kike ya nauyi? Dan Allah taimako nake so" Minal tace "taimako? Taimakon me?" Ruqayyah tace "ina neman wanda zan aika kano, a sirri, wanda zan aika din bana son ya san ni zan aike" Minal tayi dariyar "me kika kulla wa?" Ruqayyah tace "ke dai bari, ina ganin na samo hanyar da zan kori wannan yaron daga gidan nan, kuma in raba shi da Sumayya" Minal tace "wanne yaron fa?" Ruqayyah tace "Adam. So nake ki samu wani ki aika shi kano on my behalf, yaje unguwar badawa layout gida mai number 49 ya gaya wa masu gida cewa dansu da suke nema yana kaduna, ya basu address din gidan nan ya gaya musu cewa yana nan ynaa aikin driver".
Minal tace "ke Ruqayyah! Ji nake kin ce min iyayensa christians ne. In kuma suka tafi dashi suka mayar dashi Christian fa?" Ruqayyah tace "in haka ta faru to na tabbatar dama musuluncin nasa bana gaskiya bane ba, ai in dai da gaske yake to ba zai koma ba. Ni dai ina son in daina ganinsa anan gidan ne kawai, yadda ya gudu daga can ya taho nan haka in suka zo nemansa nan ma zai gudu ya kara gaba" Minal tayi shiru tana tunani, Ruqayyah tace "ni in ba zaki yi min ba ki gaya min in samu wanda zai yi min" Minal tace "babu komai, akwai wani yaron Alhaji Kabiru da nake dan saka wa aiyuka, zan tura shi Kanon" Ruqayyah tayi murmushi "shi yasa nake son ki Aminiya" Minal tace "babu wani Aminiya, yaudhe rabon ki da gida na? Ni kuma kullum ina kan hanyar zuwa gidan ki. Ina son ma zanzo ki raka ni in karasa siyayyar haihuwar nan" daga nan suka cigaba da hirarrakin su.
And so it happened....
Sanda cikin Fatima ya shiga watan haihuwa, a lokacin ne kuma sako ya samu Hussain na dawowar abokin sa Sadiq zuwa garin Abuja tare da balarabiyar matarsa da kuma dan su da suka haifa. Sai Hussain ya shirya da niyyar tafiya yaje ya gano abokinsa da kuma sabon family dinsa, sannan kuma yana son ya ga likitansa daga nan. Tunda yayi maganar tafiyar Fatima take kuka, ita bata so ya tafi, ita so take ta bishi amma kuma cikinta yayi nauyi sosai. "kiyi hakuri Fatima, Abuja ne fa ba wani guri ba, a yau zanje in dawo" amma ta tubure dole ya hakura da tafiyar sai gobe, goben ma ya kuma daga wa sai wata goben a haka har sati, dan haka ya yakice ya tafi da kyar ba wai dan ya damu da ganin abokinsa ba sai dai dan ya damu da zuwa gurin likita, ciwo ya dame shi sosai, ga kuma jini da yake fitarws sosai. Sau da takai shi har bakin mota yayi kissing dinta sannan ya sunkuya yayi kissing cikin sannan ya shiga mota shida Hassan Adam yana tukawa suka tafi.
A hanya suka yi hira sosai da Hassan, hira mai dadi duk da cewa baya jin dadin jikinsa, Adam ma kuma suna sako shi a cikin hirar yana jin labaran irin yarintarsu da kuma abubuwan da suka faru lokacin tasowarsu. A haka har suka iso garin Abuja suka shiga har cikin palace, sai dai kuma fitowa daga mota ya gagari Hussain. Nan take hankalin Hassan ya tashi ainun ya kuma umarci Adam daya juya motar zuwa asibiti, kafin su karasa asibitin jikin Hussain ya rikice gabaki daya dan sai tura shi akayi zuwa dakin likita kuma take aka saka masa oxygen dan numfashin sa sama sama yake fita. In hankalin Hassan yayi dubu to ya tashi gaba ki daya, amma a dole aka cire hannunsa daga na Hussain aka shiga da Hussain ciki shi kuma aka barshi a waje yana jira.
Bayan tsahon lokacin da Hassan ba zai iya tunawa ba sai doctors din suka fito sannan suka bashi damar ya shiga ciki gurin dan uwansa. Yana shiga Hussain ya dago hannunsa yana masa alamar yazo, ya tako a hankali ya zo ya jawo kujera ya zauna tare da kamo hannun Hussain ya rike a cikin nasa. Hassan yace "Hussain " Hussain yace "don't talk. Just hold me. Let me talk" Hassan yace "a'a kayi shiru ka rufe idonka ka huta kaji? Ka samu kayi bacci in ka tashi zaka ji ka warke" Hussain yayi murmushi, sai Hassan ya jinjina masa cewa duk da halin da yake ciki amma still yana iya yin murmushi. Ya bude baki a hankali yace "take care of our kids bro. All of them" Hassan ya maimaita "all of them" Hussain ya sake cewa "take care of everyone at home" sai kawai Hassan yaji yana so ya karanta masa kalmar shahada, sai ya karanta masa sau uku sannan ya maimaita sau daya. And then he is gone. A hankali Hassan yaji hannunsa yana zamewa daga cikin nasa, sai ya kara rike hannun hopping yaji ya rike amma bai rike ba sai kara saki da yayi, sai Hassan yaji tamkar wani bangare na ruhinsa ya fita ya barshi, tamkar ya zama rabi ne shi ba cikakken mutum ba. Tamkar ruhin Hussain ya fita ne tare da wani sashe na daga nasa ruhin.
*********. ************. **********
Tunda su Hussain suka fita Fatima bata koma cikin gida ba, sai ma ta samu kujera ta kafa a bakin kofar ta zauna tana jiran dawowar sa, kowa ya yi mata magana amma taki shiga ciki, gani take yi bata da wani sauran abinyi a cikin gidan, gani take yi kamar rayuwar ta ta kare a cikin gidan. Bayan awa biyu da tafiyar su ta dauki wayarta ta kira Hussain, tana so taji ko sun sauka lafiya amma wayar shiru ba'a dauka ba, ta kuma kira still shiru, sai ta kira ta Hassan shima bai dauka ba. Ta mike tana dosar part din aunty, a lokacin ne Ruqayyah ta shigo a mita tare da Minal sun dawo daga soyayyar zasu dauki wasu kayan sannan ta kai Minal gida. Suka tsaya a gefen Fatima, Ruqayyah tace "Fatima ya dai nag kamar hankalin ki a tashe? Wani abu ya faru ne" Fatima tace "yauwa Ruqayyah ki gwada kira Hassan da Allah muji ko sun sauka lafiya" Ruqayyah tace "sun je wani guri ne? Ni tun safe bana gida" Fatima tace "sun tafi Abuja, shi da Hussain, na kira Hussain bai dauka ba, ina so ne kawai in san ko sun sauka lafiya. Ruqayyah da Minal suka kalli juna suna tabe baki. Sannan Ruqayyah ta dauko wayarta ta kira Hassan amma bai dauka ba tace "bai dauka ba" Fatima ta fra yarfe hannu, "na shiga uku, ni gaba na faduwa yake yi. Ji nake yi kamar babu lafiya, kamar wani abu ya sami mijina" Ruqayyah ta tabe baki tace "kin san dai halin su in suna tare, na tabbatar da cewa hira ce ta saka basu ga kiran ki ba" Fatima ta sake girgiza kanta, sannan ta hango wani driver lawan ta kira shi "lawan dan Allah dauko mota ka kaini Abuja yanzu" Ruqayyah ta saki baki "for real? Wai bin sa zakiyi dan bai dauki wayarki ba? Fatima tace "ba rashin daukan waya bane ba, it is something else" sai ta juya ta nufi inda lawan yake fito da motar.
Minal ta kalli Ruqayyah tace "wai ke ma ba da mijin ki akayi tafiyar nan ba? Ke ba kya jin wani iri a jikin ki?" Ruqayyah ta tabe baki tace "ni lafiya nake jin jikina" Minal tace "dalla tashi ki bita, kema ki nuna kin damu da naki mijin" Ruqayyah tace "Abuja? Na bar fa dan jariri na tun safe a gurin Aunty" Minal tace "ba zai mutu ba ai, ki tashi ki bita ki ce kema naki jikin babu dadi mijinki kike so ki gani" Ruqayyah ta karasa packing sannan ta fito, Minal ma ta fito sai kuma lokaci daya tayi tunanin to in taje gida ma me zata yi? Ai gwara kawai ta bisu ta ga yadda dramar zata kare, sai kawai ta tafi itama ta bude gaban mota ta shiga ba tare da tayi tunanin bata tambayi mijinta ba ko kuma tunanin abinda zai je ya zo, Fatima kuma tare da Ruqayyah suka shiga baya sannan lawan driver ya ja suka dauki hanyar Abuja.
Wannan littafin na siyarwa ne, in kika ganshi a wani wajen na sata ne, in kina so ki karanta halaliyar ki kiyi min magana ta wannan number din through WhatsApp 08067081020.*The Accident*
Ko bi ta kan wayar ta sa da ya yar bai yi ba, bai kuma kula da mutanen da suke tambayar da ko lafiya suka gandhi a rikice ba, kokarin sa kawai shine ya ganshi a gida ya ganshi a gaban Hussain kuma ya yi convincing dinsa su tafi asibiti. Ko parking bai kammala ba ya fito ya rufe kofa ya doshi part din Hussain dan yaga Adam ma'ana Hussain yana gida kenan.