← Book details Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 134

Sashe 106

Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sumayya ta shiga baya shi kuma ya tayar da motar, sai Sumayya taga ya kamata tayi masa maganar da tunda tazo kanotake zuciyarta kawai dai bata son ta takura masa ne saboda ganin yadda abubuwa suka cunkushe masa, amma ganin dama tana so ta barta sai tace "yaya Hassan, dama tunda muka zo nake wani tunani" bai kalle ta ba yana kallon gabansa yace "wanne tunanin fa?" Tace "Adam. Nan ne garin su, ban sani ba ko kana da address din gidansu?" Ya dan kalle ta ta mirror yace "gidan su? Wai kina tunanin ya tafi gida ne? After what he went through kina tunanin zai juya ya koma gidan su kawai saboda Hussain ya mutu? Abandoning karatun sa? Abandoning you?" Ya danyi shiru sannan ya dora da "abandoning his religion?" Ta girgiza kanta "no, Adam ba zai taba yin haka intentionally ba. But what if he was forced to go? Maybe iyayensa somehow sun samu labarin inda yake kuma suka zo suka dauke shi forcefully, ina nufin what if he was Kidnapped by his own family?" Hassan yayi shiru, tabbas maganar ta abin dubawa ce, jin yayi shiru sai tayi ajjiyar zuciya tace "nasan hakan is not possible, sorry for bothering you, kawai dai hausawa sunce idan rakumin ka ya bata har cikin kuratandu kake nemansa" bai ce mata komai ba sai taga yayi setting wani address a Google map sannan sai yayi u turn kamar yadda map din ya nuna masa, da sauri tace "ina zamuje?" Yace "let's check out gidan nasu mu gani" taji wani irin dadi a ranta dan tana ji a jikinta cewa ko da ba'a samu Adam a gidan ba za'a samu wani hint na inda yake.

Ruqayyah tana jin su suna maganganu sama sama amma bata fahimtar su sosai, amma kuma tana so ta san me suke magana akai sai dai kuma duk su biyun fushi take yi dasu, gani take yi kamar basu damu da samun lafiyar ta ba dan har wani murna taga suna yi cewa an sallame ta daga asibiti duk da cewa ko kama hanyar warkewa bata yi ba. Sai ta dauko handbag dinta ta dauko hearing aid dinta ta saka dan taji abinda suke cewa sosai. Sai kuma taji sun daina maganar sai dai taga chanji a yanayin Sumayya kamar tana murna da wani abu, sai kuma ta lura da cewa motar ce take guiding Hassan zuwa inda zasu je. A haka har suka je kofar wani gida suka tsaya, yayi horn sai ga mai gadi ya fito ya tsaya yana kallon motar da alamar rashin sani a fuskarsa, sai Hassan ya fita ya tafi gurin sa, Sumayya tana hango su suna maganganu amma bata jin mai suke cewa sai ta tashi ta fita itama dan zuciyarta ba zata bari ta zauna a mota tana jira ba bayan zata iya samun labarin daya shafi Adam idan ta fita. Tana zuwa taji Hassan yana yiwa mai gadin kwatancen Adam yana cewa shi suke nema, friends dinsa ne. Sai taji mai gadin yace "Joseph?" Da sauri tace "eh shi" sai ya girgiza kansa yace "about five years kenan rabo na da in ga Joseph. Tun daya musulunta ya gudu ya bar gida ban kuma ganin sa ba" Hassan yace "kuma baka da ko labarin inda yake? Ba ka ji masu gidan suna fadar wani abu daya shafe shi ba?" Yace "banji suna fada ba. Amma kusan wata hudu da suka wuce a guy came here yana gaya min wai yasan inda Joseph yake a Kaduna, nace zan shigar dashi gurin mai gida amma sai ya ce shi ba zai shiga ba, yace wata ta turo shi ya fada anonymously, kamar tana son helping parents din ne su same shi" Hassan ya kalli Sumayya wadda itama shi take kallo sai yace "ko zaka iya gaya mana address din daya gaya maka please? Maybe ko zamu same shi acan din? Neman da muke yi masa mai muhimmanci ne sosai" sai mai gadin ya tsaya yana kallon su da alamar rashin yarda, sai Hassan ya zaro kudi masu yawa ya bashi yace yayi cefane, kamar ba zai fada ba kuma sai ya fada, address din gidan su Hassan. "mutumin yace wai aikin driver yake yi a gidan" Hassan yaji kansa ya dau zafi, yana iyakacin kokarin ganin bai nuna tashin hankalin sa a fili ba yace "kuma ka gayawa parents dinsa?" Mai gadin ya gyada kai "sosai. Sun jima suna nemansa, suna sonsa sosai" Hassan yace "yanzu masu gidan suna ina?" Mai gadin yace "mai gidan watansa biyu rabonsa da nan, Madam kuma da yara three weeks ago suma suka bishi, sun tafi state din su, imo".

Ikon Allah ne kawai ya dawo da Sumayya cikin mota, bata iya zama ba sai ta zauna ta fara kuka a hankali. Hassan ma da ya shigo bai yi wa kowa magana ba sai ya tayar da motar yayi reverse suka bar gurin. Sai a lokacin Ruqayyah tayi magana "ina kuka je wai? Kun fita kun barni a mita ni kadai, ne kuka yi? Ta juyo tana kallon Sumayya tace "ita kuma wannan mai aka yi mata?" Babu wanda ya amsa mata a cikin su, sai Hassan ne ya kalli Sumayya yace "ki daina kuka Sumayya, farin ciki ya kamata kiyi, ko babu komai munsan cewa yana da rai yana kuma da lafiya, kar ki manta maganar mai gadin da yace suna sonsa sosai? They will never harm him" Ruqayyah ta sake cewa "wai waye kuke maganar sa?" Hassan yace mata " Adam" tayi sauri ta kalle shi idanuwa a bude, yace "yes, gidan iyayen sa ne nan, kuma muna suspecting wata ce daga gida ta aiko gidan su ta fadi inda yake, dan haka muna tsammanin iyayensa ne suka dauke shi" Ruqayyah ta dauke kai gefe tana kallon titi, trying so hard ta boye tashin hankalin ta, ta jima tana juya maganar sannan tace "at least yanzu zaku ragewa kanku damuwa saboda, he is in the safest of places for him. Yana tare da iyayensa".

Har suka je Kaduna babu wata maganar kirkin da suke yi a tsakanin su, gidan sa ya zarce dasu direct kuma suka tarar already Aunty ta aiko an yi duk gyare gyare-gyaren da ya kamata a yi a cikin gidan, har abinci an kawo musu an ajiye a dining. Suka ci abinci suka yi wanka sannan sai ga su Aunty sun shigo sun duba Ruqayyah. Daga baya kuma sai ga Inna Ade da Baba dasu Sulaiman, Baba ya barsu a gidan bai dawo daukarsu ba sai dare, a lokacin ne kuma inna Ade ta saka Ruqayyah a gaba da nasiha saboda ta fahimci ta sauki maganar ciwon nan da zafi sosai. Sumayya kuwa jin su kawai take yi tana tunanin maganganun mai gadin nan, kalmar wata mata ta tsaya mata a zuciya, wacce matar? Kuma wai a gidan take. Wacece ita? Tunani da yawa yana crossing mind dinta amma sai ta kawar dashi, no, it can't be, her sister can't be that cruel da har zata raba ta da happiness dinta saboda selfish reason dinta. It can't be. Idan haka ta kasance zuciyarta ba zata iya dauka ba, idan haka ta kasance babu ita babu Ruqayyah, har abada.

But she is going to find out, zata yi bincike da kanta saboda bata son tayi zargin yaruwarta........

Sai dare Baba ya dawo ya dauke su gaba ki dayan su har Sumayya suka tafi gida. Bayan sun tafi ya rage Ruqayyah da Hassan da kuma yara su guda uku. Shi yayi wa yaran wanka yana jin missing dinsu a ransa ya fito dasu ita kuma ta fara shirya su da kayan baccin su suna tayi mata gwaranci da alama sunyi missing dinta sosai. Sai ya jawo kujera ya zauna yana kallon su yana jin dadi, ta daga kai tana kallon sa tace "mijina. Nace wai yanzu tunda ba zan iya shiga jirgi zuwa kasar waje ba, why not kayi min kokarin yadda za'a yi shi doctor din yazo nan ya duba ni?" Ya nade hannunsa a kirjinsa yana kallonta yana mamakin ta, yace "yazo nan ya duba ki? Da wadanne kayan aikin? Da wannan kudin kuma zan iya hayar likita kamar wannan yazo har Nigeria ya duba matata?" Ta tsaya da abinda take yi tana kallonsa Tace "ban gane ba? Kai fa kace min zaka yi duk iyakacin kokarin ka kaga na samu lafiya, I am just trying to hold you to your promise" yace "haka na fada kuma haka zanyi, amma abinda kike fada is not possible" tace "not possible? A gurin ka? Kar ka manta fa yanzu fiye da rabin abinda Hussain yake dashi sanda yana da rai ya zama naka" sai ya mike tsaye yana kallon ta yace "tunda kince haka let me tell you plans dina duk da ban gaya wa kowa ba yet. Nayi putting up H and H gabaki dayan ta for sell, already har ance dangote ya fara tayawa, zan siyar da komai, in nace komai ina nufin komai including gidan nan da muke ciki da motocin da Hussain ya bari duk zan siyar, za'a fitarwa da Fatima gadonta a kaiwa iyayen ta, za'a fitar dana sisters din mu a basu abinsu sannan sauran zanyi sadaka dashi, gaba dayansa, da fatan Allah ya kai ladan kabarin Hussain".

Wannan littafin na siyarwa ne idan kika ganshi a wani gurin na sata ne, in kina so ki karanta halaliyar ki kiyi min magana through WhatsApp ta wannan number din 08067081020

*Ina masu bukatar hadadu kuma ingantatun turarukan wuta da khumra masu dadin kamshi kuma a farashi me sauki to ga dama tazo muku Awwaba scent nada turarukan wuta humra burners kasko shisa coal dorot stool dilka body milk dadai sauransu masu bukatar na iya nemansu a whats app ko kuma kira ta wannan lambar 08034236800*
*bugu da kari duk wanda ya sayi humra ko turaren wuta a cikin wannan watan akwai kyautar dilka me kyau tafiyaya daga kasar chad wadda zata gyara jiki tay expoliating skin acikin minti 20 kawai ku garzayo dan kwasar garabasa*
*Adress kundila zoo road kano muna tura sako ko ina da iznin Allah*The Fourth Wave*
Chapter 106 · 0% Book details