← Book details Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 134

Sashe 38

Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ruqayyah tace "amma ba kya ganin kasancewar gidan Hussain yafi na Hassan yana nufin ba Hassan ne mai Company ba?" Sumayya tace "and so what? Hassan kika aura ko kuma Company kika aura? Ni I don't get you Ruqayyah. Na kasa gane kanki. Me kike so ne? Hassan mutum ne mai nagarta da kamala da sanin ya kamata, mai addini mai asali mai kyawun sura, mai lafiya mai aikin yi da rufin asiri, no ba rufin asiri ba, mai arziki. What more do you want" Ruqayyah ta mike kamar an mintsine ta tace cikin daga murya "but he made me believe cewa Companyn sa ne. He made a fool of me" Sumayya tayi saurin yi mata alama da tayi shiru, ta na leqa window sannan tace "yaushe? Ban sani ba ko kunyi maganar sanda bana tare daku amma ni ban taba jin ya jingina kansa da H and H ba, ni ban ma taba jin ya ambaci sunan kamfanin ba" Ruqayyah ta dafe kanta tan zama a bakin gado tare da cigaba da kuka tana jin kanta kamar zai tsage, Sumayya ta dawo ta zauna kusa da ita tace "kin taba zama kinyi tunanin ma'anar H and H?" Ruqayyah ta juyo tana kallonta amma bata ce komai ba, ita bata taba tunanin me yake nufi ba. Sumayya tace "ni ma ban sani ba, but ina tunanin Hassan da Hussain yake nufi" Ruqayyah tayi saurin cewa "meaning nasu ne su biyu right?" Sumayya tace "maybe, maybe not, but you will soon find out tunda kin auri daya daga cikin su. Am sure zai gaya miki koma na waye a cikin su. But Please Ruqayyah ki kwantar da hankalin ki, dan Allah kar ki nuna masa cewa hakan wani abu ne"

Ruqayyah ta rike hannunta tana hawaye "dan Allah Sumayya ki kwana anan. Ni goben nan tsoron zuwa Kanon nan nake ji, ban san me zan gani ba acan. Dan Allah ki zo muje tare" Sumayya ta goge mata hawayenta tace "tare zamu tafi, na taho da kayana ma jakata can a mota, tare zamu tafi ba zan tafi in barki ba. We are going to get through this together" ta samu ta lallabata ta kwanta sannan ta fita neman Adam ta karbi jakarta. Sai kuma ta sanarwa da kawayensu na kasa cewa Ruqayyah bata jin dadi ta kwanta bacci. Amma sai suka bita da tambayar "nan ne gidan Ruqayyah? Can kuma gidan waye? Ko gidan dan'uwan mijinta ne da ake bikin su tare? Waye mai Companyn ne wai a cikin su? Ruqayyah tace mana mijinta ne CEO haka ne?"

Da sauri Sumayya tayi excusing kanta tace bako ne da ita a waje ta fita, a ranta tana tunanin tabbas baki shine yake yanka wuya, Ruqayyah ta saka igiya ta daure wuyanta ta mika wa mutane bakin igiyar.

Bayan saukar Sumayya ne wayar Ruqayyah tayi kara, ta daga kai da kyar tana kallon sunan Hassan a jikin screen din "mijina" kamar yadda tayi saving. Tayi tsaki tana jin wutar data kwanta a kirjinta tana dada ruruwa. "Munafiki" ta fada a fili sannan ta kife wayar ta juya bayanta. Can kuma sai ta juyi ta daga wayar ta saka a kunnen ta "hello" ta fada da murya mai sanyi. "Hassana" ya fada da murya mai cike da conceri. "Yanzu Aunty ta kira ni tace kina ta kuka wai ko zan zo in rarrashe ki. Me ya faru? Waye ya taba min ke inzo in nuna masa matsayin sa?" Ruqayyah tayi shiru, a ranta tace "kamar gaske" yace "Please kiyi min magana mana inji dadi, in baki magana ba yanzu zan ajiye duk abinda nake yi in taho" a hankali tace "kana ina?" Yayi murmushi yace "gidan yafi karfin mu, baki sunyi yawa shine muka kama hotel mu da friends din mu. Kin gansu ma duk suna ta tsokana ta wai na kasa rufe baki saboda an kawo min amarya ta" bata ce komai ba saboda bata jin zata iya gaya masa magana mai dadi, dan haka shirun yafi. Yace "ba zaki gaya min abinda ya saka ki kuka ba? Ko sai nazo na gani da idona? Inji kuma da kunne na?"

Ta gyara kwanciyar ta tan jin cewa bata son ganinsa kwata kwata, at least not today, tace "na dauka a can zakuyi zamanku? Tunda nan din akwai mutane da zasu kwana saboda tafiyar da za'ayi kano gobe ko?" Ta shafa kansa yana runtse idonsa yace "yeah, right. Haka ne. But what about siyan baki and other traditional stuff?" Tace "it can wait ai......jibi in akayi dinner din kowa kaga zai watse ai, sai ku zo kuyi ta siyan bakin ku" yace "hakane......but ni kuma fa? Shikenan ba zanga matata ba? Ni fa yanzu ba gwauro bane ba fa" tace "ko? You will see me tomorrow ai in ka shigo da wuri kafin mu tafi" yace "ni ba wannan ganin nake nufi ba ai....." Tayi shiru, yace "ko abinda kike wa kuka kenan dazu?" Tace "good night" yayi ajjiyar zuciya yace "to ya zanyi da raina, ba haka dai aka so ba" tace "kanin miji ya fi miji kyau ba".

Wannan littafin na siyarwa ne, duk wanda yake so ya neme ni through WhatsApp ta wannan number din 08067081020

Wannan littafin na siyarwa ne, in kina so WhatsApp 08067081020Episode Twenty Two: Envious

Overlook the typos please.............too lazy to edit.

Thank you so much for the birthday wishes. I had a great day, and you guys contributed a lot to that.

Nayi mistake din numbering, na shekaran jiya twenty ne na jiya twenty one na yau kuma twenty two.

Muna ta Allah wadai da halayen Ruqayyah, ina fatan muna tsintar pieces of halayyar mu a cikin nata.
Idan kina jin haushi a yayin da wani ya samu daukaka kina jin ina ma ke ce ba shi bane ba.
Idan kina kallon saurayin kawarki kina jin ina ma dai naki ne ba nata ba.
Idan kina jin bacin rai idan kika ga business din wata ya bunkasa ba naki ba, ko wata ta chanja kayan dakinta ke bami chanja ba, ko wata ta sayi kaya ke kuma baki da kudin siya.
Idan kina jin dadi a ranki idan wani ya samu wata matsala.
Wadannan duk kadan ne daga cikin siffofin hassada.

Hassada daban kishin kai daban, kishin kai shine ki nemi na kanki a lokaci guda kuma kina yiwa sauran masu neman na kansu wadanda suke sama da ke da wadanda suke kasa dake fatan alkhairi.

Yar uwa, a duk lokacin da kike kallon na sama dake a samun abin duniya to zai toshe miki idanuwanki ki daina ganin kyawun abinda yake gabanki, abinda kike dashi, wannan kuma shi zai sa ki zamanto marar godiyar ubangiji.

Yar uwa ki kalli na kasa dake, ki duba dubunnan mutanen da suke fatan su samu daukaka irin taki, wannan zai saka ki samu wadatar zuci.

Irin wadannan halayen baka sanin kana dasu har sai kayi nisa a cikin su. A lokacin kuma sun riga sun bi jini da tsokar jikin ka.

Yes, akwai mutane irin Ruqayyah and they walk amongst us

*******************

Da kyar Sumayya ta samu ta lallaba kawayen da mostly Ruqayyah hayar su tayo, ta gaya musu babu siyan baki yau sai ranar lahadi, farko suka ki tafiya suka ce ai dare yayi sai dai su kwana da safe sa tafi, ita kuma tasan indai suka kwana din to kuwa cewa zasuyi sai anje dasu kano kuma Allah kadai yasan abinda zasu aikata acan din. Ba zata dauki wannan chance din ba, dan haka ta koma sama ta samu kudi a gurin Ruqayyah ta kuma lallabasu dashi, sannan ta fita waje ta samu Adam "Adam da Allah a cikin drivers din gidan nan ka samu wani ya mayar da mutanen Ruqayyah gida" yace "ohhh okay, gani ai, kim manta nima drivern gidan ne?" Ta nuna shi tace "banda kai, someone else" yana murmushi yace "why? Ba kya so insha wahala?" ta juya kamar zata bar gurin sannan ta juyo tace "saboda yammata ne" ta shige da sauri tana jin sa yana mata dariya.

Washegari da sassafe aka aiko su bayar da kayansu, wai kayan duk a mota za'a hada su tare da motar da zata dauki kayan lefe, su kuma in sun shirya sai su bi jirgi. Ruqayyah ko hada kayan bata yi ba, sai a lokacin Sumayya ta taimaka mata suka debi wadanda ta saka da bikinta tunda bata dinka lefe ba kuma kayanta na gida duk ta barsu a gida saboda bata bukatar su. Suka hada akan kayan Sumayya a yar karamar jakarta suka bayar. Sai a lokacin sannan Sumayya ta jawo Ruqayyah da kyar suka fito zasu zagaya gida. Tun daga kan Bedroom din da suka kwana a ciki, daya Bedroom din wanda suke tunanin na Hassan ne amma daga alama shima bai tare ba tunda babu kayansa komai a ciki sai dai set din furniture shigen nata sai banbancin design da color. Suka zagaya katon palon da yake sama mai hade da dining room, su kansu set din dining din abin kallo ne, sannan suka sauko kasa suka duba three bedrooms din da suke kasan kowanne in suka shiga sai Sumayya taga kamar yafi ba baya kyau, Ruqayyah kawai binta take yi fuskarta babu yabo babu fallasa, suka dawo falon farko komai Sumayya ta gani sai tayi ta kambamawa dan ta jawo hankalin Ruqayyah har ta samu ta dan fara yabawa da kalmomi irin " eh, yayi kyau" duk kuwa da cewa bata bata ganin makamancin shi ba ballantana wanda ya fishi.
Chapter 38 · 0% Book details