← Book details Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 134

Sashe 82

Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan hakan ne Minal tazo mata ziyara. Suka shige cikin dakinta suka zauna Minal tana cewa "kai Ruqayyah wannan dakin naki ai yayi datti da yawa, kwanan ki nawa rabon da ki share shi?" Ruqayyah tace "wannan kuma matsala ta ne. Ke dai ki zauna a nan dan yallaban gidan nan ya xe baya son mu'amala ta dake kuma dama kwana biyun nan ba dadi muke yi dashi ba" Minal tace "mijin naki ne ba kwa dadi da shi? Lallai sannun ki da aiki, in dai ta nine ya kwantar da hankalin sa in baya son inzo gidan sa ba zan kuma zuwa ba dan nima ina da gidan mijina ba wai a titi nake ba" Ruqayyah tace "ke ba akan ki bane ba, ni din ce dai kawai duk zuciyata babu dadi kwana biyun nan. Kinsan matar gidan nan kuwa ciki ne da ita?" Minal tace "wacce matar gidan? Aunty?" Ruqayyah tayi dariya tace "ke yar iska ce Allah. Auntyn ce zata yi ciki dan baki da kunya. Gimbiyar gidan nake yi miki magana matar dan goten kaduna" Minal ta bude ido "to fa babbar magana. Ni da nake ta saka ran ta hanyar rashin haihuwar ta ne maganar Malam zata tabbata" Ruqayyah tace "ke dai bari, abin nan ba karamin daga min hankali yake yi ba wallahi, musamman ace ta haifi namiji shikenan fa mu da dukiyar su daga hange sai leke sai harara daga nesa, duk yayan da zan tara zasu yi ta bin yayanta ne a baya kamar yadda mijina yake bin mijinta a baya" Minal tace "ki zo mu koma Ruqayyah, kina bukatar taimako, rayuwarki tana cikin matsala sai an hada miki da addu'a. Kinga fa ni yanzu albishir din da na zo inyi miki shine ciki ne dani, idan kinga yadda Alhaji, mahaifiyarsa da yan uwansa suke nan nan dani sai kinyi mamaki, ita fa uwargidan nasa da suke cewa matar so yanzu babu son duk ya dawo gurina da abinda yake cikina. Tana nan kamar zata mutu kullum kofarta a rufe" Ruqayyah tace "Allah Minal? Yanzu ciki ne da ke? Kai amma na taya ki murna wallahi Allah ya raba ku lafiya" daga nan sai ta bata labarin nata cikin itama suka taya juna murna suka cigaba da plans din su na yakar mutanen da suke gani a matsayin makiyan su.

Rayuwa ta cigaba da tafiya ba tare da kowa yasan cewa Hussain ba wai warkewa yayi da gaske ba, hatta Hassan bai san cewa ciwo yana cin Hussain kadan kadan ba, itama kuma Fatima saboda tana fama da nata laulayin cikin sai ta gaza gurin fahimtar changes din da yake samu. Ciwon ciki ne yafi damunsa mostly idan yaci abinci amma sai ya boye yaki yarda fatima ta gani. Duk sanda kuma baya jin ciwon hakan keeping wide smile a fuskarsa wanda yake boye damuwar da take cikin idanuwansa, amma duk da haka damuwar bata boyu ga Hassan ba, tambaye shi "wai kai me yake damunka ne?" Sai yace "ni babu abinda yake damuna, maybe idonka ne yake nuna maka hakan" "babu wani ido na, gashi nan har ramewa naga kayi? Are you sick or something?" Hussain ya daga kafada yace "babu wani abu, gajiya ce kawai, aiki yayi min yawa ina bukatar hutawa. Ga kuma marar lafiya ina da ita a gida" ya fada yana murmushin dan ya kawar da maganar amma Hassan bai yarda ba, sam zuciyarsa bata yi masa dadi da yanayin na Hussain.

Baya son abinda zuciyarsa take fada masa akan yanayin na Hussain amma kuma dole ya kamata ya bincika wannan angle din ko dan ya samu nutsuwar zuciya. Wannan ya sa ya tura sako zuwa ga doctor din Hussain, ya roki sanin health status din Hussain duk da cewa yana tunanin ba zasu bashi ba amma kuma ganin cewa ya tura sakon ne da same email da ya fara registering Hussain sai ya saka ran samu. Sai da aka kwana biyu sannan sai ga phone call daga doctor din.

Yana office ne a lokacin, yaga number da code din India sai jikinsa ya bashi doctor din ne tunda bashi da business da wani a India kuma yana saka ran ji daga doctor din. Sai dai kuma sai yaji yana tsoron dauka dan bai san abinda zaiji ba, da kyar dai ya hakura ya dauka ya kara a kunnensa yare da cewa "Hello" doctor din yace "are you Hussain aminu's brother?" Hassan yace "yes, I am" sai ya fara fada "then why are you not bringing him back to hospital? He should be in the hospital right now taking treatment" Hassan ya runtse idonsa yana jin tamkar wukake doctor din yake soka masa a kirjinsa yace "but he said the operation was a success" doctor yace "no it wasn't, and we told him that. You should bring him in again, he is .... ....." Hassan bai karasa jin maganar doctor din ba ya saki wayar hannu sa ta fadi kasa.

*Kuyi hakuri babu yawa, bana so in barku jira babu dadi shi yasa na baku a haka, tomorrow's episode will insha Allah be longer and more action packed*.

Wannan littafin na siyarwa ne, idan kin ganshi a wani guri na sata ne, in kina so ki karanta halaliyar ki kiyi min magana through WhatsApp ta wannan number din 08067081020*The Accident*

Ko bi ta kan wayar ta sa da ya yar bai yi ba, bai kuma kula da mutanen da suke tambayar da ko lafiya suka gandhi a rikice ba, kokarin sa kawai shine ya ganshi a gida ya ganshi a gaban Hussain kuma ya yi convincing dinsa su tafi asibiti. Ko parking bai kammala ba ya fito ya rufe kofa ya doshi part din Hussain dan yaga Adam ma'ana Hussain yana gida kenan.

Yana shig ya samu daya daga cikin yaran Fatima "ina Fatima take? Me gidan yana ciki?" Ganin Yadda hankalinsa yake a tashe ya sa ta rude "gimbiya bata nan, sun fita dazu ita da Aunty Khadija, amma yallaban yana ciki banga saukowarsa ba....." bai jira ta karasa bayanin ta ba ya wuce ta ya haura sama da sauri ya nufi wing din Hussain. A palo ya same shi a kwance akan doguwar kujera da diary dinsa a gabansa, idonsa a rufe, hannun daya akan cikinsa dayan kuma akan diary din. Motsin shigowar Hassan ne ya saka shi bude idonsa da sauri. Sai kuma yayi kokarin mikewa zaune yana dan cije lips dinsa amma kuma fuskarsa da murmushi "hey, gidan mijin aure ne fa kake shigo min kai tsaye, ko baka san ni mijin aure bane ba?" Hassan ya share shi ya nufi diary din kamar zai dauka sai Hussain ya riga shi, a tura shi bayan sa yace "sirri ne na gaya maka" Hassan yana kallon sa yana lura da yadda yake iyakacin kokarin sa na ganin yayi keeping straight face sannan yace "why? Me yasa zaka yi mana karya Hussain? Ko zaka yi wa kowa karya ni mai yasa zaka yi min Hussain? Why do you choose to suffer alone bayan ba kai kadai aka haife ka ba tare dani aka haife ka? Me yasa zaka ware ni when you need me the most?" Hussain ya dauke kansa gefe, ya fahimci cewa ya sani, sai ya girgiza kansa yace "what does it matter in na gaya maka din, babu abinda zaka iya yi min, babu abinda kowa zai iya yi min, wanda zai yi min komai na gaya masa na kuma roke shi ya bani lafiya, na saka kun taya ni rokonsa ya bani lafiya, tunda ka ga bai bani ba to lafiyar bat da alkhairi a gurina, shi kadai yasan me yake nufi da ni".

Zuciyar Hassan ta karye ya durkusa a gaban Hussain tare da dafa gwuiwar sa yace "Hussain dan Allah kazo mu koma asibiti, dan girman....." Hussain yayi sauri ya rufe masa baki "mun gama maganar nan Hassan, na roke ka kuma ka amince, kayi min min alkawarin ba zaka sake mayar dani asibiti ba. Hassan likitoci ba zasu hana mala'ikan daukan rai ya dauke ni ba, kudina dukka ko zan karar dasu ba zasu kara min adadin kwanakin da aka kayyade min ba. Dan Allah Hassan kar ka tilasta min komawa asibitin nan, bana so in mutu a zagaye da likitoci da injina,bana son in karasa sauran kwanaki na a asibiti looking at faces din mutanen da basu da muhimmanci a rayuwata. Na fi son in zauna a gida tare da ku, tare da Fatima, nafi son inyi making use of my last days doing abinda zai amfani lahira ta ba wai neman lafiyar da babu wanda zai bani ita ba. Wancan aikin da akayi min na gaya maka na amince ne dan in faranta maka ba wai dan raina yana so ba" Hassan ya sake girgiza kansa "ba dan ni ba, yanzu kayi dan Fatima, dan abinda yake cikin Fatima" Hussain ya dauko diary dinsa yana budewa yana murmushi yace "Allah baya taba barin wani dan wani yaji dadi, ko babu ni nasan abinda yake cikin Fatima yana da uba, nasan ba zai yi kuka maraici ba, zai samu gatan uba a gurinka kuma a bangaren mahaifiyarsa ma ba zaiyi rashin komai ba".

Hassan ya zauna sosai yana kallon Hussain guiwoyin sa sunyi sanyi da suka kasa cigaba da daukan sa, ya runtse idonsa yana fatan hawaye yazo masa ko zaiji sanyi a zuciyarsa. A ransa yana addu'a "Allah in zaka dauki wani a cikin mu Allah ka dauke ni ka bar Hussain, Allah ka dawo da ciwon Hussain kaina shi ka bashi lafiya ya Allah. Allah kar kasa Hussain ya tafi ya barni Allah" ya bude idonsa sai suka hada ido da Hussain yana yi masa murmushi yace "don't cry bro, kar kabada maza mana, everything is going to be okay".
Chapter 82 · 0% Book details