Sashe 109
Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yana kokarin saita numfashin sa yace mata "me kike tunanin kina yi?" Ta juyo tana kallon sa sannan ta mike tsaye tace "sannu da zuwa mijina" yace "me kike tunanin kina yi? Wa ya baki izinin shigowa nan har da kwaso kaya? Ki zo ki fita daga gidan nan" tace "na shigo ne saboda gidan mijina ne, kuma fita ta ba yanzu ba, am here to stay. Idan kai baka so mu muna so ni da yayanka, zaka iya cigaba da zama a can gidan duk sanda kake bukatar ganin mu sai kazo ka ganmu anan. Amma mu anan zamu zauna" yace "ni nine mai gidan, kuma ni nace ki fita, ba'a nan nayi niyyar ki zauna ba kuma ba'a nan zaki zauna ba, ki fita ko kuma in saka a fitar dake. Na gama magana" ya fada dead serious, ya juya zai fita daga dakin sai tace "ni kuma ban gama magana ba, in fact, ban ma fara magana ba tukuna, in har kana ganin zaka iya sakawa a zo a fitar da matarka da yayanka daga cikin gidan ka bismillah. Amma ni ba zan fita ba kuma ba zan barka ka bayar da ko kwandala daga cikin kudin nan ba" ya juyo yana kallonta yace "and how are you going to stop me? Taya zaki hana ni yin abinda na yi niyya?" Itama ta juyo tana kallon sa tace "da ace kasan abinda nayi kafin in samu kudin nan da baka tambaye ni yadda zanyi in hana ka rabar da su ba" ya kara matsowa cikin mamaki yace "kika samu? Yaushe kika samu? Me kuma kika yi? What have you done?" Ta danyi murmushi tace "komai, from the beginning to the end" sai ya dakata a tafiyar da yake yi, a lokaci daya yana realising truth, tun farko ba shi ta aura ba dukiyar da tayi tunanin tasa ce ta aura, daga baya kuma da ta san ba tasa bace ba ta zauna dashi ne saboda tana tunanin zai samu, tana burin ya samu. Zuciyarsa tayi sinking a cikin kirjinsa, ji yayi kamar ta koma cikinsa ta bar kirjinsa. Cikin muryar da yaji kamar ba tashi bace ba Yace "me yasa kika taimaka min ranar nan? Me yasa kika yi saving rayuwata?" Sai ta sake wani murmushin, she hates breaking his heart amma yau ranar gaskiya ce, dole ta fada masa dan ya san dalilin da yasa zata aikata abinda ta riga tayi niyyar yi.
Tace "Baba yaje neman aiki gurinka, sanda aka sace ka sai ya bamu labari, shi ya dauka kaine mai kamfanin dan haka ce mana yayi kai ne mai H and H. Muna ta following labarin batanka saboda Baba ya damu da kai sosai, and then sai gaka a toilet din mu, daga yanayin ka da kayan jikinka nayi tunanin kai ne shi yasa na saka rayuwata a hadari na taimaka maka dan inaso ka rike taimakon da nayi maka a ranka kar ka manta, dan ina so ka biya ni. Na dauka wasu kudi zaka bani wanda zai fitardani daga talauci sai kai kuma ka yi Maganar aure na and I thought auren mais even better dan maybe abinda zaka bani din zai iya karewa amma in na aureka komai naka ya zama nawa. That's why I married you"
Ya dafe kirjinsa yana jingina da jikin bango dan ji yake yi kafafuwan sa kamar ba zasu iya daukarsa ba. Yana girgiza kansa yace "kina nufin ba kya sona Hassana? Kudina Kika aura bani ba Hassana?" Ta bata rai tace "I can't say gaskiya, ban sani ba ko zaman da muka yi da kai na fara sonka amma ban sani ba but abinda na sani shine bana son wannan sunan da kake gaya min, I hate it, kullum kuma ka gaya min raina baci yake yi" ya bude baki zaiyi magana amma sai ya kasa, his heart breaking into pieces, bleeding, kunnuwan sa har kara suke yi masa dan suna so su daina jin maganganun Ruqayyah amma sai ta cigaba da cewa "nasan heart dinka zata yi breaking kaima kamar yadda tawa tayi breaking lokacin da aka kawo ni gidan nan na fahimci cewa ba kai ne mai kudin ba, na fahimci cewa you are just your brother's puppet. But I thought zan iya juya ra'ayin ka tunda naga kana sona, I thought zan iya hada ka da brother din naka yadda zaka kwasar mana wani abu daga cikin dukiyar sa da muma mu kafa kanmu amma kaki bani hadin kai, saying wai kafi son sa akan kowa".
Hassan ya tuna da maganganun da Ruqayyah tayi ta gaya masa akan Hussain, akan Fatima, wato duk karya ce kenan, duk da ta hada su ne, wato duk dan taci dukiyar Hussain ne. Ya tuno maganar Baba, ya tuno maganar Hussain kamar yanzu yake gaya masa "me yasa bata je ta kira iyayenta sun taimaka maka ba sai ta zabi ta kama katanga ta haura?" Sai yau Hassan ya samu amsar sa.. yace "bayan wannan kuma sai me kika yi?" Tayi shiru tana kallonsa, yace "kina da hannu a gurin batan Adam?" Ta juya hannu "what does it matter? Sai me? Ni ba zan bari yaruwata ta auri wannan inyamurin drivern ba" yace "ke kika aikawa iyayensa suka zo suka tafi dashi" ta juya idonta, me za'a yi mata in an sani? Karkarinta Sumayya tayi fushi na wani lokaci da zarar kudi sun zauna kamar yadda take saka rai shikenan komai zai dawo normal tsakanin su tace "eh ni na aika musu, me za'a yi min?" Yace "you are not human being Ruqayyah ke shaidaniya ce. A devil in human form".
Sai kuma wani tunani yazo masa, tunanin da ya sa ya mike straight yana mantawa da ciwon da yake ji a zuciyarsa ya karasa gabanta tare da rike hannunta yace "what else did you do saboda kudin Hussain? Me kika yi? Did you cause the accident? Did you kill Fatima and her baby saboda kici gadon su?" Tayi kokarin kwace hannunta amma karfin rikon da yayi mata yasa ta kasa kwacewa, cikin wata irin budaddiyar murya yace "answer me!" Saboda karfin muryar da yayi mata magana da ita sai da taji dakin ya motsa, ta kalle shi taga yana yi mata wani irin kallo mai nuni da cewa zai iya yi mata komai, ta kalli cikin idonsa tace "wallahi, tallahi, billahillazi la ilaha illa huwa ban kashe Fatima ba ballantana abinda yake cikinta, kuma bani nayi sanadiyyar accident din mu ba" a idonta yaga cewa gaskiya take fada masa sai ya saketa, ta matsa baya tana murza hannunta inda ya rike din, ya juya hannunsa dafe da kirjinsa zai bar dakin sai tace "ina sake tuna maka, kar ka bayar dako kwandala a kudin nan" ya juyo yana kallonta da juyayyun idanuwa yace "are you threatening me?" Direct Tace "yes" ya juyo a kufule yace "me zaki yi? Idan na rabarda dukiyar mezaki iya yi akai? And after duk abinda kika gaya min kina tunanin zanyi abinda kike so?" Tace "ba zaka yi ba amma ni zan saka ka kayi. Ba dai Hussain ba? Ba dai dan kana son Hussain ne kace zaka rabar da dukiyar sa ba? To albishirinka, in dai kayi haka ni kuma sai na tabbatar nayi destroying duk wani kykykyawan fenti da Hussain ya shafa wa kansa sanda yana da rai, I will make sure mutanen da suke sonsa suke kuma yi masa addu'a sun dawo suna kinsa suna kuma tsine masa" yaji tamkar ta saka mashi ta chaki zuciyarsa, yace "and ta yaya zaki yi hakan?" Sai ta koma bakin gado ta dauki Hussain da yake kwance tace "zan je gidajen rediyo in fadi cewa wannan yaron dansa ne ba naka bane ba, in ce raping dina yayi har na haife shi. Nasan wasu ba zasu yarda ba amma da yawa zasu yarda saboda mutane sunfi yarda da labarin karya aka na gaskiya. Zan ce kudinsa na cult ne, ta yaya Mutun mai kananan shekaru kamar sa zai tara kudade irin wadannan? Zan fada cewa baban ku ya fara bayarwa, shine silar yin kudinsa, zan kuma ce sanadiyyar mutuwar sa shine matarsa aka ce ya bayar tare da abinda yake cikinta, shi kuma yaki bayarwa shine suka sanye jininsa a gabanka tare da drivern ku shi yasa drivern ya bata har yau ba'a ganshi ba, sannan kuma suka yi causing accident dinda matar da mutu da tsohon ciki dan su dauki fansar kin bin maganar su da yayi. Am sure wasu ba zasu yarda ba amma wasu zasu yarda. Kuma am sure su kansu wadanda basu yarda ba dinzan saka musu doubt a kan sa. Zan kuma ce wannan dalilin ne yasa ka rabar da dukiyarsa saboda kace ba zaka iya cin dukiyar haram ba........."
Wata shakada yayi mata tare da bugata da bango ce tasa sauran maganar ta tsaya a makogwaronta, idanuwan ta a waje, ta saka hannunta duk biyun tana kokarin raba hannunsa da wuyanta amma ta kasa, a take ta fara jin kamshin mutuwa, ta fara fitar da rai da rayuwa, lallai tayi playing too bad dan wannan rikon da yayi mata bata jin zai sake ta har sai numfashin ta ya bar jikinta. Ya fara magana da karfi kamar zai tsaga dakin "why??! Why?! A kan kudi? Akan kudin da baki san ta yadda yayi ya tara su ba? Akan sa zaki yi ikirarin yi masa wannan mugun sharrin? Saboda duniya? Saboda kina so ki samu duniya, Allah wadaran ki Ruqayyah. Allah wadaran haduwata dake Ruqayyah. Kaico na, ina ma dai na mutu a ranar dana hadu dake da ban kawo wa family na jaraba ba. Allah wadaran aure na dake Hassana"
Kafafunsa yaji an kama ana jan wandonsa, ya sunkuyar da idonsa da yake cike da hawaye zuwa kasa yana kallon yan biyun sa da suka rike kafafuwan sa suna kuka, bai ji shigowar su ba bai kuma ji kukan su ba kawai taba shin da suka yi ne ya dawo da hankalin sa kansu. "daddy don hut mommy" yusuf ya fada yana matso hawaye, Aminu yaje ya kama rigar Ruqayyah data kusan suma saboda azaba yace "mommy mommy".