← Book details Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 134

Sashe 93

Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk da Ruqayyah taji wani iri kuma taji a jikinta wani abu ya faru da Hassan amma itama a yanzu taimakon take bukata ido rufe, tace "sunana Ruqayyah, ni ce matar Hassan Aminu Abdullahi. Ina cikin daji munyi accident tare da gimbiya Fatima matar Hussain Aminu Abdullahi da kuma drivern mu, motar mu ta kama da wuta, Allah yayi musu rasuwa, ni kadai na rage yanzu. Ina neman taimako dan bansan a inda nake ba" san sandan ya juya yana kallon yanuwan sa, sai kuma ya kalli gawar Hussain yana jinjina hikima ta ubangiji daya dauki ran mata da miji a lokaci daya ba tare d kowannen su yasan da mutuwar dan uwansa ba. Tabbas wannan labari ne da zai iya saka Hassan yayi abinda yafi suma ma ba suma ba, briefly ya fada wa sauran abinda matar tace, sai wani a cikin su ya karbi wayar yayi setting dinta ta yadda zasu ke tracking wayar hannun Ruqayyah suka ga inda take sannan suka sanar mata da cewa gasu nan zuwa, sai kuma suka yi waya station aka turo musu da wata motar suka hadu a hanya suka rabu biyu wadansu suka tafi gurin Ruqayyah wadansu kuma suka wuce da gawar Hussain da kuma unconscious Hassan.

Ruqayyah kam tsoro take ji, ta bar gurin motar tayi hanyar da zata mayar da ita kan titi dan ji take kamar gawawwakin da suke cikin mota suna miko hannu zasu jata zuwa cikin sauran wutar da bata karasa mutuwa ba. Sannan kuma tana jin tamkar Fatima tana binta a baya, tamkar nemanta da tayi ra rasa ta zama fatalwa ne zata galaka ta saboda yar mata da yaron ta da tayi. A idonta take ganin kamar wulkawar Fatima ta gefenta, in kuma ta rufe idon ko da da niyyar kifta shi ne sai taga idanun Minal suna kallonta kamar yadda ta ganta a cikin mota a mace. Ga kafa ta rike, sam taki lankwasuwa sai janta takeyi ta sandare kamar wani ita ce. Duk kuma wannan da sauki akan abinda take ji a zuciyarta, wani irin feeling wanda ba zata iya misalta shi ba.

Ta fara tuno masoyan ta, ƴaƴan ta guda uku, Sumayya, inna Ade da Baba, suleiman da Zunnur dan duk abinda take yi, duk wannan fadi tashin da take yi da wannan dakakkiyar zuciyar tata amma ita kanta ta san tana son su sosai sai dai kawai ita bata iya nuna soyayya ba, ga kuma Hassan , da kin ta da sonta he have come to be part of her, ba zata ce tana masa so na soyayya ba amma ta damu dashi. Ta runtse idonta tana matse hawayen daya taru a idonta yake disashe mata ganin ta amma kuma hoton fuskar Minal data gani shi ya saka ta yi saurin bude idon tana kokarin kara sauri ama kafa taki bada hadin kai. Gani take kamar gawawwakin ne suka rike mata kafar. A kunnuwan ta har ji taje yi kamar ana maganganu kasa kasa. Sai kuma taji kukan jaririn data ajiye yana amsa kuwwa a kunnuwan ta.

Kuka take yi sosai, tana kokarin yin sauri iyakacin iyawarta amma in ta waiga sai taga babu inda taje, still bata wani yi nisa da motar ba. Sai data kwashe lokacin da a gurinta kamar ya kai tsahon shekara guda sannan taji gunjin mota tana shigowa gurin, sai kuma taji hayaniyar mutane sannan taga an haske ta da fitila. Hasken da ta ji shi har cikin zuciyarta, ta sauke ajjiyar zuciya tana tunanin karshen wahalar ta yazo. But that is just the beginning.

Tana ji suka karaso inda take suka kamata suka sakata a motar da suka zo da ita sannan wasu suka tafi gurin accident din suna kokarin karasa kashe sauran wutar da take ci, tana jin su suna ta yawa suna fadar abinda ta gani, sun dan fara yi mata tambaya amma ganin yadda take a rikice yasa wani wanda take tunanin shine babban su yace su rabu da ita kawai, a lokacin wata motar ta karaso kamar ta fite service da kuma wata karamar mota again, taji suna ta maganar abin taji kuma sun ambaci mutuwar Hussain, sun kuma fahimci abinda take so su fahimta na cewa Fatima matar Hussain ce a cikin motar, sun kuma fahimci wacece Fatima dan take taji wani yana waya Kano cewa a sanar da gidan sarautar kano sunyi rashin yarsu, gimbiya Fatima.

Ta lumshe idonta tana jingina da jikin kujerar motar, the dead is now complete, ta haka ta binne sirrinta babu gudu babu ja da baya, amma kuma ina Fatima take? In kuma bata mutu ba fa? In kuma tashi tayi ta tafi fa? In kuma yanzu already tana hanyar Kaduna kuma fa? In ta fada tace ta haihu ta bawa Ruqayyah dan ya zata yi kenan? Me zata ce?

Ta girgiza kanta da sauri tana cewa "uhm uhm" a fili kamar wata zararriya. It is going to be her words against fatima's. Zata musa ne da duk iyakacin iyawarta tace ita bata karbi da ba, tace Fatima sharri take yi mata. To amma kuma in aka tambayeta game da gawar da take cikin mota wadda ta riga ta furta cewa ta Fatima ce fa? Me zata ce akan hakan? Tabbas bata haƙa ta binne sirrinta ba, tabbas yana nan a bude kuma yana tare da Fatima a duk inda take. But What if ta mutu da gaske wani ne ya dauke gawarta, ko matsafa, ko naman daji? There is still hope for her amma bata da tabbas, kuma tasan wannan rashin tabbas din tabbas zai ke hana ta bacci. A koda yaushe, Fatima zata iya bayyana kuma bayyanar ta yana nufin bankaduwar sirrinta.

Wannan kuma yana nufin rasa komai nata.........

Including iyayenta, dan tasan direct Baba zai tsine mata inna Ade kuma tace babu ita babu ita har abada

But for now, shin gawar Minal tayi konewar da ba za'a Iya gane ta ba? Ta tambayi kanta tana lekawa ta taga, kamar amsar tanbayarta taji wani a gurin yana cewa. "Ayi wa yanuwansu waya, sai dai a binne su anan dan ba zasu dauku ba, sun zama gawayi" ta lumshe idonta da niyyar yin ajjiyar zuciya amma fuskar Minal data gani ya saka ta bude idon da sauri.

Motar da take ciki aka bawa umarnin ta tafi, a kaita Kaduna gidan mijinta, wannan yasa taji hankalin ta ya kwanta, sai dai suna barin gurin ta juya tana kallon gurin. A nan ne rayuwarta ta kare, anan ne kuma rayuwarta ta fara. Su Kusan rai shida suka bar Kaduna a mota, amma a cikin su ita kadai zata koma garin Kaduna.

***************. **********. **********

Da taimakon maaikacin lafiyar da yake cikin ambulance din Hassan ya fara dawowa hayyacin sa, amma sai dai shi har cikin zuciyarsa bai so dawowar tasa ba, so yake ya tafi shima, so yake yabi Hussain, baya so ya cigaba da rayuwa. Wannan wacce irin jarabawa ce uban giji yake yi masa?

Ya kamo hannun Hussain ya rike "Hussain! Ka tafi dani nima mana! Hussain Fatima ta bika ka roka min ubangiji nima ya dauke ni in biku! Hussain Fatima ta tafi , ta taho tare da abinda yake cikin ta. Innalillahi wa inna ilaihir rajiun" duk rarrashin duniya babu wanda ba'a yi masa ba amma ya kasa yin shiru. So yake wai maybe in ya ishe su da magana su gaya masa cewa ba gaskiya bane ba, su gaya masa Fatima da abinda yake cikinta suna raye, su gaya masa Ruqayyah ba gaskiya ta fada ba ko kuma anje an tarar basu mutu ba but instead of su ce haka sai yaji suna waya da yanuwansu na can akan a gaya masa gawar Fatima ba zata dauku ba sai dai a binne ta a can.

Girgiza kansa kawai yake yi, so yake yayi kukan amma ya kasa sai magana kawai yake yi da gawar Hussain kamar wani tababbe. Tabbas mutuwar Hussain ta taba shi amma bata yi masa dukan da wannan ta Fatima tayi masa ba. Saboda dama yasan Hussain bashi da lafiya, kuma a hannun sa ya mutu. Amma Fatima fa? Hussain yana mutuwa ba abinda yake so sama da abinda yake cikin Fatima amma ashe ko ganin sa ba zai yi ba, ashe ko numfashi ba zai shaka ba. Wannan wacce irin jarabawa ce? Anya zai iya ci kuwa? Ace a rana daya babu Hussain babu family dinsa? Babu komai sai memory dinsa?

Memory mai dadi.......
Memory mai zafi.......
Memory mai tsayawa a zuciya......

Yana jin wayar Hussain tanata ringing amma ya kasa kallon ta ma ballantana yayi tunanin dauka. Ba zai wuce mutanen gidan su ba, ba zai wuce aunty ko yan uwansu ba, sun kira shi suji da gaske ne? Da gaske Hussain dinsu ya tafi ya barsu? Da gaske Fatima tare da babyn su sun bi shi inda ba'a dawowa?

Ba zai iya amsa musu ba.....
Ba zai iya kallon wayar ba.....
Ba zai iya kallon hoton Fatima hannayenta a dafe akan cikin ta tayi shape din heart da yatsunta a kan cikin ba, wanda shine hoton da yake kan wayar.

Sai ya saka hannu ya kife wayar, baya jin zai iya magana da kowa.

Ya tuno da nasihar da Adam yayi masa dazu "innalillahi wa inna ilaihir rajiun" ya fara fada yana maimaita wa hannunsa biyu rike dana Hussain "innalillahi wa inna ilaihir rajiun" sauran mutanen motar suka cigaba da taya shi har suka iso Kaduna suka je gida.

********. *********** *****

Tun tafiyar su Hussain Aunty take zarya a falo, in ta hau sama sai ta sauko sai ta kuma komawa sama ta kwanta sai ta tashi ta dawo kasa ta zauna. Ta rasa me yake yi mata dadi. Su Zulaihat suna kallo a palo ta kora su daki ta kashe kallon, ji tayi bata son karar tvn, bata son karar komai.

Ta jima a nan sai kuma ta koma sama ta saka hijab dinta ta fita da niyyar shiga part din Hussain ta duba gimbiya Fatima, dama tunda cikinta ya girma kullum sai taje ta dubata. Sai dai a compound din gidan ta hadu da maigadi wanda yayi mata bayanin cewa ai Fatima bata nan yaji Lawan driver yace tace zai kaita Abuja "tare suka tafi da Aunty Ruqayyah"
Chapter 93 · 0% Book details