← Book details Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 134

Sashe 86

Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yana shig ya samu daya daga cikin yaran Fatima "ina Fatima take? Me gidan yana ciki?" Ganin Yadda hankalinsa yake a tashe ya sa ta rude "gimbiya bata nan, sun fita dazu ita da Aunty Khadija, amma yallaban yana ciki banga saukowarsa ba....." bai jira ta karasa bayanin ta ba ya wuce ta ya haura sama da sauri ya nufi wing din Hussain. A palo ya same shi a kwance akan doguwar kujera da diary dinsa a gabansa, idonsa a rufe, hannun daya akan cikinsa dayan kuma akan diary din. Motsin shigowar Hassan ne ya saka shi bude idonsa da sauri. Sai kuma yayi kokarin mikewa zaune yana dan cije lips dinsa amma kuma fuskarsa da murmushi "hey, gidan mijin aure ne fa kake shigo min kai tsaye, ko baka san ni mijin aure bane ba?" Hassan ya share shi ya nufi diary din kamar zai dauka sai Hussain ya riga shi, a tura shi bayan sa yace "sirri ne na gaya maka" Hassan yana kallon sa yana lura da yadda yake iyakacin kokarin sa na ganin yayi keeping straight face sannan yace "why? Me yasa zaka yi mana karya Hussain? Ko zaka yi wa kowa karya ni mai yasa zaka yi min Hussain? Why do you choose to suffer alone bayan ba kai kadai aka haife ka ba tare dani aka haife ka? Me yasa zaka ware ni when you need me the most?" Hussain ya dauke kansa gefe, ya fahimci cewa ya sani, sai ya girgiza kansa yace "what does it matter in na gaya maka din, babu abinda zaka iya yi min, babu abinda kowa zai iya yi min, wanda zai yi min komai na gaya masa na kuma roke shi ya bani lafiya, na saka kun taya ni rokonsa ya bani lafiya, tunda ka ga bai bani ba to lafiyar bat da alkhairi a gurina, shi kadai yasan me yake nufi da ni".

Zuciyar Hassan ta karye ya durkusa a gaban Hussain tare da dafa gwuiwar sa yace "Hussain dan Allah kazo mu koma asibiti, dan girman....." Hussain yayi sauri ya rufe masa baki "mun gama maganar nan Hassan, na roke ka kuma ka amince, kayi min min alkawarin ba zaka sake mayar dani asibiti ba. Hassan likitoci ba zasu hana mala'ikan daukan rai ya dauke ni ba, kudina dukka ko zan karar dasu ba zasu kara min adadin kwanakin da aka kayyade min ba. Dan Allah Hassan kar ka tilasta min komawa asibitin nan, bana so in mutu a zagaye da likitoci da injina,bana son in karasa sauran kwanaki na a asibiti looking at faces din mutanen da basu da muhimmanci a rayuwata. Na fi son in zauna a gida tare da ku, tare da Fatima, nafi son inyi making use of my last days doing abinda zai amfani lahira ta ba wai neman lafiyar da babu wanda zai bani ita ba. Wancan aikin da akayi min na gaya maka na amince ne dan in faranta maka ba wai dan raina yana so ba" Hassan ya sake girgiza kansa "ba dan ni ba, yanzu kayi dan Fatima, dan abinda yake cikin Fatima" Hussain ya dauko diary dinsa yana budewa yana murmushi yace "Allah baya taba barin wani dan wani yaji dadi, ko babu ni nasan abinda yake cikin Fatima yana da uba, nasan ba zai yi kuka maraici ba, zai samu gatan uba a gurinka kuma a bangaren mahaifiyarsa ma ba zaiyi rashin komai ba".

Hassan ya zauna sosai yana kallon Hussain guiwoyin sa sunyi sanyi da suka kasa cigaba da daukan sa, ya runtse idonsa yana fatan hawaye yazo masa ko zaiji sanyi a zuciyarsa. A ransa yana addu'a "Allah in zaka dauki wani a cikin mu Allah ka dauke ni ka bar Hussain, Allah ka dawo da ciwon Hussain kaina shi ka bashi lafiya ya Allah. Allah kar kasa Hussain ya tafi ya barni Allah" ya bude idonsa sai suka hada ido da Hussain yana yi masa murmushi yace "don't cry bro, kar kabada maza mana, everything is going to be okay".

Babu yadda Hassan bai yi ba amma Hussain ya tubure yace shi babu asibitin da zai koma, babu aikin da za'a sake yi masa, kuma ya roke shi Allah da Annabi kar yabari kowa yaji cewa ciwonsa ya dawo. "Bana so inga hawayen su, ga halin da Fatima take ciki bana so in tayar mata da hankali" sai dai Hassan bai hakura ba sai da ya kuma kiran wancan doctor din yayi masa bayanin irin taurin kan Hussain da dagewar da yayi akan ba zai koma ba, sai doctor din yayi referring dinsu to wani oncologist din a nan Nigeria ya kuma bawa Hassan shawarar ya lallaba Hussain ya kaishi can "ko ba za'a yi masa aiki ba sai a bashi drugs din da zasu rage masa radadin ciwo, cos he is in pain right now, ina mamakin ma yadda har kace yan iya harkokin sa har yana boye ciwonsa, he really is strong". Hassan ya gyada kai yace "the strongest man I have ever known".

Likitan da aka hada shi da shi a Abuja yake da private hospital dinsa kuma ya kware sosai a aikinsa. Hassan ne ya shirya yaje asibitin, ya tarar already an aiko da record din Hussain da komai daga can asibitin dan hak kawai takardu ya ciccike sannan ya koma Kaduna ya fara yakin lallaba Hussain akan ya taho yaga wannan likitan. Da kyar ya yarda suka zo, da alkawarin cewa ba kwantar dashi za'a yi ba. Da daddare suka zo secretly saboda gudun sa idon yan media, Doctor din ya duba shi sosai, yayi masa hotuna sannan yayi masa prescribing drugs din da zasu taimaka masa wajen dulling pain din da yake ji. Amma Hassan bai ji yayi promising komai ba. Haka suka karasa kwana a hotel tunda Hussain yaki kwana a asibitin.

Da safe ne da zasu taho yake cewa "da akwai wani abokina Sadiq, dan sarkin Abuja ne ina jin baka san shi ba dan a wani zuwa da nayi London muka hadu dashi kuma bai taba kawo min ziyara ba nima ones na taba zuwa gidan su tunda shi ba mazauni bane ba. Amma we are very close a waya munsan affairs din juna" Hassan yace "to ko zamu shiga ku gaisa?" A ransa yana fatan hakan zai farantawa Hussain rai, Hussain yayi murmushi yace "baya nan, ya bata" Hassan ya danyi dariya, "ya bata fa kace? Ya bata kamar yaya?" Hussain yace "wata yarinya yake so balarabiya, babansa sarkin Abuja yaki zuwa ya nema masa aurenta shine na bashi shawarar yaje ya nema da kansa, he went there kuma suka hana shi. Tun daga nan ba'a kuma jin labarin sa ba yayi cutting off ties da gida gaba ki daya har mu abokan sa babu wanda yasan inda yake. Rumors have it that ya sace yarinyar ne yaje ya aure ta, but babu wanda yasan a wacce kasar suke yanzu" Hassan ya bude baki yana mamakin wannan irin karfin hali na wannan bawan Allah, amma ya sani dole duk inda suka tafi ma watarana da kafafuwan su zasu dawo gida kuma yana guje musu abinda zasu tarar a gidan musamman saboda kasancewar su yan sarauta.

Hussain yaji dadin magungunan sa sosai, dan da suka kare shi da kansa ya kira Doctor din ya sake bashi wasu. Sun rage masa ciwon da yake ji a cikinsa sosai kuma yanzu yakan ita zama yaci abinci ya koshi, yaji dadin hakan dan hakan ya kara taimaka masa wajen kara boyewa Fatima halin da yake ciki. Cikin Fatima yana ta girma abinsa, cikin lafiya ita kuma cikin kwanciyar hankali dan babu abinda yake damunta, ga Hussain yanzu da yake kara makale mata kamar cingam dan office din ma yanzu ba fita yake yi ba in ma ya fita da wuri yake dawowa, yawon kasashen duniyar ma duk ya daina kullum yana tare da ita yana yi wa babyn cikinta hira, haka zai ta bawa cikin labarai yana dariya shi kadai ita kuma tana yi masa dariyar wautar sa "ba fa ta jinka" yace "injiwa? Haka ya gaya miki?" Tace "wai kai wa yace maka namiji ne? Na gaya maka mace ce" yace "ke wa yagaya miki macece? Ni na gaya miki namiji ne" tace "ai a cikina take ko? Muna communicating through placenta" yayi dariya "gori zaki yi min ko? Nima ai muna communicating through you, kuma ya gaya min shi namiji ne" tace "to aje a duba mana, sai a kure musu" yace "anki wayon. Ni bana so a kure ni".
Chapter 86 · 0% Book details