← Book details Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 128 OF 134

Sashe 128

Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da tago kai suka hada ido taga har yanzu ita yake kallo yana murmushi, sai taja hijab dinta ta rufe fuskarta, ita bata san ya akayi yake tsokanar ta har yake murmushi ba bayan ga halin da Ruqayyah take ciki, yana nufin wai shi yanzu bashi da wani concern akan Ruqayyah? Ko babu komai ai sister dinta ce kuma uwar yayan sa. Tace "me Doctor din yace?" Ya dan daga kafada yace "yace zata warke, zai dai duba ta yanzu amma yana tunanin sai an kai ta asibiti sunyi flushing system dinta, in akwai sauran maganin duk zasu fitar mata sannan su saka naya drip sabida ta samu nourishment tunda ta kwana ta wuni bata ci abinci ba sannan kuma a jira sanda zata farka"

Sumayya ta gyada kai hawaye yana tarar mata a idonta tace "me yasa zata yi overdose?" Ya daga kafada yace "Allah masani, maybe ta gaji da duniyar ne" Sumayya ta girgiza kanta da sauri tace "no! She will never do that. Ni nasan Ruqayyah fiye da kowa" yace "really? I don't think so" ya mika mata hannu "ki zo mu tafi gida" sai ta girgiza kai "ina so in zauna a gurinta, in za'a kaita asibitin ma ina son in bisu can din" ganin kallon da yake mata ya saka ta sunkuyar da kanta tace "in ka amince".

Yayi ajjiyar zuciya, tabbas yasan akwai soyayya da shakuwa sosai a tsakanin Sumayya da Ruqayyah, amma shi yanzu Ruqayyah tsoro take bashi, yana gudun kar ta cutar masa da matarsa akan kishin da take iƙrarin tana yi duk da yasan cewa na karya ne, ita da bakinta ta gaya masa bata sonsa, ta aure shine saboda tana tunanin mai kudi ne shi. But, ba zai raba hanta da jini ba sai ya tafi ya zauna akan kujera yace "we will wait together then. Bazan taba barin ku tare daga ke sai ita ba" ta biyo shi itama ta zauna tana kallon sa tace "wai kana tunanin Ruqayyah zata iya cutar dani? She is my twin sister, she will never hurt me" yace "she already did hurt you, not once not twice, wanda na sani ma kenan, Allah ne kadai yasan sau nawa ta cutar da ke, bana fatan ta sake wani. I won't wait har sai ta sake kafin in raba ku"

Tace "nasan akan Adam kake wannan maganar, ita a nata juyayyen tunanin tana ganin kamar taumako na tayi data raba ni da Adam" ya daga mata hannu yace "mu bar maganar Adam please" tayi mamakin yadda ya hade rai, wato kishi yake yi kenan ko mene ne? Amma sai tayi shiru ta bar maganar kamar yadda ya bukata.

Suna zaune sai ta dauko wayarta zata kira Inna ta sanar da ita sai ya hana ta "menene amfanin gaya mata? Hankalin ta ne zai tashi kuma Baba ba zai barta tazo ta ganta ba, ki bari kawai in kin tabbatar ta warke sai ki gaya mata daga baya yadda hankalin ta ba zai tashi ba" ta gyada kai cikin fahimta, tabbas Hassan ya san halin baba kuma yasan cewa in dai har Ruqayyah bata yi abinda yace ba to ba zata shiga gidan sa ba kuma Inna ma ba zata shiga nata gidan ba ballantana shi.

Suna nan zaune doctor din ya fito ya sauka kasa sai gashi ya dawo da kujerar marasa lafiya, Sumayya ta tashi tataimak masa suka dora Ruqayyah akai sannan suka kama shida Hassan suka sauka da ita kasa, doctor din yana cewa "akwai problem gaskiya, I tot zan iya farkar da ita tun anan amma abin ya gagara, dole zamu tafi da ita za'a yi mata some tests.

Nan take hankalin Sumayya ya kuma tashi, a dole Hassan ya dauke ta a mota suka bi baya ambulance din da doctor din yasa Ruqayyah a ciki suka tafi asibiti suna bayar da sakon cewa idan yara sun dawo su tafi gidan Aunty. A asibitin anyi duk abinda za'a yi dan ganin an tashi Ruqayyah daga bacci amma abin ya gagara, suna can suna ta abu daya har yamma har aka yi sallar magrib sannan ta farka tana jinsu suna ta maganganu can nesa, babu hearing aid dinta dan haka bata fahimtar abinda suke cewa, sai ta bude idonta a hankali ta sauke shi akan Sumayya da take tsaye suna magana da wata nurse akan tests din da doctor din ya rubuto wa Ruqayyah, yawancin su akan lafiyar kwakwalwar ta.

Ruqayyah ta mayar da idonta ta rufe sannan da dan karfi tace "me kike yi anan?" Sumayya ta juyo da sauri tana tahowa inda take sai Ruqayyah ta daga mata hannu tana yi mata alamar ta dakata daga inda take "babu ni babu ke. Maci amana. Kamar yadda kika ce babu ke babu ni saboda adam to nima babu ni babu ke saboda Hassan" Sumayya ta tsaya daga inda take ta kasa karaso wa ballantana tayi kokarin kare kanta. Duk da tasan ko tayi maganar ma Ruqayyah ba jinta zata yi ba tunda babu hearing aid a kunnenta.

Ruqayyah ta dafa gado ta mike zaune, tana jin jikinta wani iri sannan kuma kanta yana wani mugun sarawa kamar zai tsage biyu, ga cikinta kamar an yashe duk abinda yake ciki. Idonta da yake cike da tsana akan Sumayya, bata taba tunanin akwai ranar da zata zo wadda a cikin ta zata tsani Sumayya ba amma sai gashi yau ranar tazo. Ta dauke kanta ta daina kallon ta cikin tsawa ta kuma cewa "ki fita daga nan nace. Bana son ganin ki ba tsane ki na tsani kowa na tsani komai, bana bukatar ku babu ni babu ku kar ku sake nema na kar ku sake zuwa inda nake kar ku saje tunanin ma akwai wata alaka a tsakani na da ku"

Sumayya ta karasa da sauri ta kama hannunta sai ta ture ta da karfi, dai dai lokacin da Hassan ya shigo, kallo daya Ruqayyah tayi masa ta juyar da kanta gefe hawaye masu zafi suna zubowa daga idon ta.

Gani tayi yayi mata kyau, irin kyan da bata taba tunanin yana dashi ba, irin kyan dabata taba gani a gurin sa ba sanda yana nata sai yanzu da ya zama ba nata ba tukuna. Sanda yana nata bata kallon sa, wadansu take kalla shi yasa bata taba zama ta yabi surar sa ba, kamar yadda gidan Hussain kafin ya zama nata take ganin sa kamar shine aljannar duniya yanzu kuma daya zama nata sai ya koma mata kamar makabarta, sanda bata da kudi kuma sai ta ke kallon masu kudi a matsayin wadanda basu da wani problem a duniya, yanzu kuma da tayi kudin sai taga a yanzun ne ma problems suka fara mata.

Kaicho....

Hassan yazo da sauri ya rike Sumayya yana janye ta daga kusa da Ruqayyah, ya saka hanu ya goge mata hawayenta a kunnenta ya rada mata "let's go home".

Har sun kai bakin kofa Sumayya ta sake juyowa ta kalli Ruqayyah, sai suka hada ido and she can see the heart break da yaje idon Ruqayyah and her heart went out to her. Har suka je gida basu yi magana da, suna tsayawa sai Sumayya ta roki Hassan ta shiga gidan Ruqayyah ta saka aisha ta hada kayan da ta san Ruqayyah zata bukata a asibiti ta hada da hearing aid dinta sannan ta saka driver ya tafi da ita asibiti ita kuma Ruqayyah ta dawo gida.

Dakinta ta wuce direct tayi alwala tayi sallah sai ta samu kanta da kuka a sujjadar ta tana rokawa Ruqayyah dai-dai to a rayuwarta. Sai data idar sannan ta shiga toilet tayi wanka. Tana fitowa suka hada ido da Hassan a zaune a bakin gadonta, a guje ta juya ta koma bandakin tare da rufo kofa, dariya ta kama Hassan, dama yana sane ya zauna dan yaji motsinta a toilet din yasan kuma zata fito babu kaya. Sai yaja pillow ya kwanta kafafuwan sa a kasa hannayensa a rungume a kirjinsa idonsa akan toilet din. Ya san dole zata fito shi kuma yana nan yana jira.

Ta jima a tsaye tana mayar da numfashi, Inna lillahi, yau ya zata yi? Ta yi ta dube dube babu wani abu da zata rufe jikinta dashi, towel din nan na jikinta shikenan sa dan ko kaya dama bata shigo dasu ba da towel din ta shigo. Ta jingina a jikin kofar tana tunanin abinda zata yi, ta jima a haka sannan ta leka ta ramin key ta hango shi yana nan a kwance akan gado. Ta dafe kanta tana jin ana kiraye kirayen sallar ishai, ga sanyin toilet din ya fara ratsa ta tasan kuma in tayi wasa yanzu zata kama zazzaɓi.

Ta danyi knocking kofar toilet din sannan ta dan bude kadan. "Dan Allah yaya Hassan ka miko min zani da hijab" ya gyara kwanciyar sa yace "saboda me?" Tace "saboda Allah. Wallahi sanyi nake ji, zanyi mura da zazzaɓi" yace "to ki fito mana ki shirya, ni ina ruwa na dake" taji kamar zata yi kuka tace "ba zan iya shiryawa a gaban ka ba, dan Allah ka tafi dakin ka" yace "nan ma dakina ne, dan dakin matata ne" tace "ai Allah nace maka. Kaga ana kiran sallah zaka rasa jam'i" yace "shikenan sai muyi tare, in mukayi tare ma zamu samu ladan jam'i ni dake"

Ta dora goshinta akan kofar idonta a rufe tana jin sanyi yana ratsa ta tace "dan Allah dan Annabi daddyn Hussain ka fita, wallahi sanyi nake ji" ya mike zaune yana kallon toilet din yace "to ke me yasa ba zaki fito ba sai na fita, ni ba mijinki bane ba?" Tace "kunyarka nake ji Allah, ba zan iya fitowa babu kaya a gaban ka ba" yadda tayi maganar kamar zata yi kuka yasa ya ji tausayin ta, ya mike yai kamar zai shiga toilet din, yaga ta rufo kofar da sauri har da murda key sai yayi dariya yace "na fita to. A shirya lafiya, amma zan dawo".
Chapter 128 · 0% Book details