← Book details Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 117 OF 134

Sashe 117

Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da safe Hassan ya shiga gaishe da Aunty kamar yadda ya saba yi kullum kafin ya fita, ya tarar da ita a dakin ta bata fito ba, ya zauna a kasa yana gaisheta tayi hamma tace "har zaka fita Hassan? Ni kaga gajiya ta hana ni saukowa daga kan gado har yanzu" yayi murmushi, "nima akwai ciwon jikin fa, akwai wasu tenants ne da aka hada ni dasu jiya, to munyi dasu zamu hadu a can yu da karfe goma na safe zasu ga gidan. Bana so suje ni banje ba" Aunty ta gyada kai tace "hakan dai dai ne, Allah ya bada Sa'a. Ka sauka kasa kaci abinci amma kafin ka fita, kar kaje ka fadi a hanya" ya mike yana cewa "faduwa kuma Aunty sai kace wani tsoho? Da saura na fa" tace "to waye tsohon? Kasan dai in muka yi tsere dai sai na wuce ka" baice komai ba sai yayi kamar zai fita sai tace "yauwa Hassan? Jiya ya kukayi da Sumayya kuwa?" Ya dawo yana kallon agogon sa yace "ya muka yi kuwa Aunty? Kince in kaita gida kuma n kaita, and that is all" ta mike zaune tana kallonsa tace "jiya Sa'adatu take gaya min maganar da kuka yi da Yusuf a kan Sumayya, me yasa ni baka gaya min kunyi haka dashi ba?" Ya zauna akan side table yana kallon ta, ya marairaice murya "Aunty, magana ce yayi min wadda take close to impossible, to menene kuma amfanin ayi ta jan maganar" tace "gwara da kace "close to impossible" ba impossible ba. Kag hakan yana nufin it is possible kenan. Ni da ta gaya min maganar dadi naji wallahi, sai naji hankali na ya karkata a wannan bangaren. Ko ba dan komai ba ko dan yaran nan guda uku da Allah ya bamu" ya girgiza kai yace "Aunty don't get like that please, yara ko a hannun wa suke zasu rayu, kuma yanzu they got you and they are doing just fine. Kar azo ayi abu for the wrong reason kuma azo ana dana sani daga baya" tace "eh yara yanzu suna dani, amma daga ni har kai bamu san kwana nawa yarage min a duniya ba" ya sake mikewa kamar an mintsine shi yana cewa "mu bar maganar nan haka please, babu wanda yasan gawar fari sai Allah, maybe ma ita Sumayyan ta riga ki tafiya Allah ne kadai ya sani" bata bar maganar ba tace "haushin Ruqayyah suke so su huce maka da Sumayya, baka ganin kin karbar kamar watsa musu kasa ne a ido? Ina laifin wanda ya nuna ya damu da damuwarka?" Ya dafe kansa yace "Aunty, yarinyar nan bata sona, akwai wanda take so daban, kuma tasan nasan alakar ta da wancan din kusan nine ma na hada su, idan na karbi tayin Baba b akya ganin kamar na zubar da girmana a gurin su ita da saurayin nata?" Tace "bansan wannan ba, abinda nasani kawai shine matar mutum kamar kabarinsa take, in matarsa ce ba zaka taba auren ta ba" Yusuf ya bude kofar dakin ya shigo, sai ya dane kafafuwan babansa yana murna sannan ya je ya kama hannun Aunty yana janta, "Aunty ki tashi daga baccin nan ki zo muje muci abinci" Hassan ya hade rai yace "kai! Fita ka bamu guri" yaron yayi kamar zaiyi kuka amma sai ya juya zai fita, Aunty ta kira shi ta dauko wayarta ta nemo wani hoto da Sumayya suka dauka tare da Zulaihat da Nafisa ta nuna masa tace "Yusufa wacece wannan?" Ya karba ya gani sannan cikin murna yace "mommy!" Sai ya fita da gudu gurin yan'uwansa.

Aunty ta kalli Hassan ta daga kafada tace "a gurin su mommy ce, ba step mom ba, duk matar da zaka aura will be their step mom not their mom. Kamar yadda nake a matsayin uwa a gare ku not a matsayin kushiyar uwa Sai kayi lissafin abinda zai iya faruwa da ku idan da ace iyayen mu basu yi tunanin hada aure na dana mahaifin ku ba. Maybe da bamu samu kan mu a matsayin da muke kai a yanzu ba. Wannan kadai ya ishe ka misali" ya sake cewa "aunty, this is a different case, na gaya miki yarinyar nan bata sona, in anyi abin nan zai zamanto kamar an tilasta mata ne" Aunty tace "nima sanda aka aura min babanku bana yi masa soyayyar aure, amma a yanzu da za'a dawo min da rayuwata baya ace in sake zabar miji da shi zan sake zaba over and over again"

Sai ya kama kofa ya bude zai fita ba tare da yace mata komai ba, tace "Hassan" ya juyo yanab kallon ta amma bai amsa ba sai tace "misali idan Sumayya ta yarda zata aure ka, zaka amince?" Yace "bata so na Aunty, ba zata yarda ta aure ni ba" ta sake cewa "misali nace ai, in ta yarda, zaka yarda kaima?" A rufe idonsa ya bude, sai kuma ya gyada kai yace "yes, zan yarda, but only in ta yarda, in ba tilasta mata akayi ba".

Wannan kenan.........

Bara mu leka muga yadda rayuwa ta kasancewa Ruqayyah a cikin wannan shekarar...........

A ranar data farka ta tarar ana katange gidan da take ciki, a ranar ne kuma yan aikin gidan kaf dinsu, wadanda suka yi aiki a karkashin fatima suka hada kayan su kaf suka zo yi mata sallama "zamu tafi, Allah ya sada mu da alkharinsa" Ruqayyah ta bude baki "ba gane zasu tafi ba, ni na sallame ku ne? Ni da iya kacin saninaba sallami kowa a cikin ku ba, ko akwai wata matsala ne wadda ban san daita ba?" Babbar cikinsu tace "babu wata matsala, kawai da bazamu iya cigaba da aiki a gidan nan ba alhalin masu gidan basa cikinsa" Ruqayyah tafara kufula, "ban gane masu gida basa ciki ba, ni nice mai gidan, wadanne masu gidan kumakuke magana akai?" Tace "gimbiya Fatima itace uwargidan mu, mutuniyar kirki da sanin ya kamata, tunda akayi auren ku ita muke yiwa aiki da haka yanzu lokaci daya ba zamu iya cigaba da aiki a cikin gidan nan sannan kuma ba a karkashin taba. Gwara mu tafi mu nemi wani aikin a wani gurin daban" Ruqayyah mamaki ya kamata, me suke nufi? Zasu iya yiwa Fatima aiki ammaita ba zasu iya yi mata ba? Dame Fatima ta fita?

Ta fara lallashin su da nuna musu cewa duk abinda Fatima take musu itama zata dora akai amma suka tubure suka ki zama. Har sun mike tace "zanyi muku doubling salaries dinku in kuka zauna" ita tana ganin wannan wani abu ne da ba zasu taba iya turning down ba amma sai taji daga daga cikin su tace "it is not about the money, it is about loyalty" daga nan suka fita suka barta a zaune.

Takaicin duniya ya ishe ta, ita bata san inda ake samo yan aiki ba dan tunda akayi bikin su Aunty ce take samo mata yan aiki har da mai girki duk ita take samo mata ita da Fatima, gashi yanzu na Fatima sun gudu saura nata kuma aikin yayi wa nata yawa dan gidan ba irin nata bane ba, duk kuwa da cewa bangaren Hussain a rufe yake.

Sai taji gida yayi mata shiru sosai, taji wani irin kadaici kamar ita kadai ta rage a duniya, wannan yasa ta kira zuwaira a waya, kawarta ce da Minal ta hada su kuma tana cikin kawayen ta da suka tsaya mata a wajen bikin su ta gaya mata problem dinta "ban sani ba ko kin san yadda zanyi in samo yan aiki? Kamar gida biyu haka masu hankali" babu bata lokaci zuwaira tace zata samo mata sannan kuma suka jajanta labarin batan Minal, zuwaira tace "ance man ke ce mutum ta karshe da kika ganta ko?" Ruqayyah tace "inji wanne munafikin? Inji wanne makaryacin?" Zuwaira tace "a'a, ni da mijinta ne yake gayamin kuma yace mijinki ne yagaya masa, ba san waye munafikin ba a cikin su ba kuma san wate makaryacin ba" Ruqayyah tayi kokarin chanja maganar "okay ban san sunyi maganar ba ai. Ki gayyato duk kawaye ku zo kuga sabon gidana" sai ta bata labarin tarewar da tayi a gida Hussain. Tun a wayar taji excitement a muryar ta, kafin a jima kuwa wajan mutum biyar a kawayen su sun kira ta aka maganar, shi kenan aka bar maganar batan Minal aka cigaba da lissafa yadda za'a ci duniya.

Wannan yasa Ruqayyah taji kadaicin taya dan ragu, sai dai tayi ta kiran wayar Sumayya amma bata shiga, taso ko ma menene zata yi Sumayya takasance a hannun damanta kamar yadda suka shirya tun suna yara amma abin ya gagara, daga dukkan alamu Sumayya tayi fushidaita amma tasan zata sauko tunda ita ba iya fushi tayi ba, dawani ma ballantana da ita yaruwarta Ruqayyah.

Sai ta bata lokaci da niyyar ta huce, kafin nan suma su Inna da Baba sun huce sai taje har gida tayi musu bayanin cewa Hassan da kansa ya dauki kudin nan ya bata ba takura masa tayi ba, wata kila ma daga nan su yarda su biyo tasu dawo gidan da zama gabaki daya. Wata kila idan sunzo ta samu nutsuwar zuciya har ta iya bacci, dan yanzu sam bata bacci sai ta sha maganin bacci shima idan ta sha a wahale take yin baccin. Wannan kukan jaririn ne yake damunta a kunnuwan ta, ko ta cire hearing aid dinta bata daina jin sa dan kamar a cikin kanta yake ba wai ta kunnen ta kukan yake shiga ba. Da zarar ta rufe idonta kuma gawar Minal take gani, bata yo mata magana sai idanuwa da take tsare ta dasu, idanuwa masu ban tsoro, in kuma ta samu tayi baccin to kuwa sai Hussain ya ziyarce ta a cikin baccin ta, kullum mafarkin kusan guda daya ne cewa jaririn data ajiye a kofar orphanage ya girma ya rikide ya zama Hussain ita kuma ta koma jaririn, so defenseless so vulnerable and so scared, shi kuma sai yazo yasa kafa ya tatsile ta, kullum mafarkin iri daya ne amma kuma kullum sai ya bata tsoro tamkar ranar ta fara yinsa.
Chapter 117 · 0% Book details