← Book details Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 134

Sashe 36

Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun da yamma Inna Ade ta aika aka kirawo Hassana zuwa dakin Baba, suka tafi tare da Sumayya, tun kafin suje Ruqayyah ta riga tasan dalilin kiran, tasan fada ne za'a yi mata a kan zaman aure ita kuma tana ganin kamar bata lokacin su zasu yi su kuma bata bakin su, su fa irin zaman auren talakawa suka sani dan haka akan irinsa zasuyi ma ta fada, wannan kuwa aure na na masu abin hannunsu wadanda basu dawata sauran damuwa a duniya sai dai suci mai kyau su sha mai kyau su kuma kwanta a mai kyau. Ita tuntuni ta gama yiwa kanta fada akan yadda zata yi wannan zaman auren, ta riga ta kama bakin zaren Hassan ta fahimci cewa ba zata iya yi masa musu ba saboda yayi mata kwarjini dayawa amma zata iya cigaba da lullube kanta da hijabin daga riga ya santa dashi sannan tana jan zaren sa a hankali ta karkashin kasa kamar yadda tayi masa a lokacin karbar kudin hidimar biki. Let someone else take the fall, someone else, in dai har ba ita bace ba. Anyone.

Suna shiga dakin sai taji Baba ya fara tsokanar ta, abinda ta jima bata ji yayi ba, da alama shima yana alhinin rabuwa da yar tasa ne. Sai da ya saka su duk yi dariya gabaki dayan su sannan ya fara magana.

"To Hassana, alhamdulillah, gashi kamar yau Allah ya bamu ku keda yaruwarki amma gashi cikin kudirarsa yau zaki bar gidan nan zuwa gidan mijin ki. Babu abinda zamu cewa Allah sai dai godiya tunda munsan kudirarsa ce kawai ta hada ku keda Hassan sannan ta saka soyayyar ki a zuciyar Hassan din. Dan girman Allah Ruqayyah kar ki bamu kunya, ina tsananin ganin girman yaron nan wallahi kuma in da zaki bi ta ta shi na tabbatar ba karamin zaman lafiya zaku yi ba tunda yana son ki sosai. Da farko shi aure bautar ubangiji ne, ita kuma bauta ita ce abinda ake yi dan a samu shiga aljanna, ita ce kuma abinda idan an ƙi yi sai a halaka a fada wuta Allah ya kiyaye, wannan kadai ya nuna miki darajar abinda kika yi, aure. Aure sunna ne, amma abinda ake yi a cikinsa farilla ne, dole ne ki bi mijinki Ruqayyah indai kina son lahirar ki tayi kyau, dole ki sauke wannan bakar zuciyar taki da wannan saurin fushin naki kiyi masa biyayya Hassana idan ba haka ba ina tausaya miki, ina tausayawa duniyar ki da lahirar ki baki daya"

Baba ya jima yana ta yiwa Ruqayyah fada, fadan daya saka Sumayya kuka amma ba Ruqayyah ba. Bayan ya gama yayi mata adduoi na fatan zaman lafiya a gidan mijinta sannan yayi musu sallama ya fita.

Bayan ya fita ne Inna da yanuwanta da suka zo daga zamfara suka dora da nasu, suka yi mata doguwar nasiha akan zaman aure da kuma hanyoyin da za'a kyautatawa miji ta hanyar magana mai dadi, godiya, ladabi da biyayya, nuna soyayya da kulawa "ki mayar da duk abinda ya shafe shi ya zama top priority dinki, yan uwansa su zama naki, shimfidar ki ta zama abinda kullum yake muradin komawa ga, abincin ki ya zamanto shi kadai yake iya ci yaji dadi, wadannan sune manyan abinda namiji yake bukata. In dai har kin rike wadannan to kuwa ba kya bukatar boka ko Malam akan mijinki. Zaki juya kayan ki yadda kika ga dama musamman idan yana sonki" Daga nan kuma sai suka dauko nata tsarabar da suka taho mata da ita suka fara bata, dake dake ne da kulle kulle iri iri, wasu a leda wasu a robobi da kwalabe ko wanne an rubuta yadda za'a yi amfani dashi. Gwoggo Habibah tace "bamu baki su bane ba saboda bamu san kalar halittar ki ba kema kuma baki san ta mijin ki ba, dan haka sai kinje gidan kin kwana biyu kin fara gane yadda abin yake sannan zan kira ki in kara miki bayanin abinda kike bukata da kuma yadda zaki yi amfani da shi sosai. Ko wacce mace da irin halittar ta haka suma mazan, in akaje akayi ta bawa yarinya abubuwan da suka fi karfinta sai azo a zamu matsala kuma. "

Bayan sun gama nasu sannan sauran yanuwa kowa yazo ya dora da nasa, hakuri, biyayya, girmama wa, soyayya, su akayi ta maimaita wa Ruqayyah har sai data ji ta haddace kalaman tsaf a kwakwalwar ta. Abinda Ya rage mata shine yin amfani na kalmomin.

Bayan magrib akazo daukan amarya. Aunty ce da kanta tare da hajiyan Kano, kanwar baban su Hassan su suka jagoranci sauran mata zuwa dauko Ruqayyah, Ruqayyah har tayi wankan ta ta shirya cikin wata green atamfa mai adon pink wadda tayi matukar karbar ta, dinkin yayi kyau sosai a jikin ta, sai a lokacin taga Sumayya tana kuka sannan nata jikin ya fara sanyi, sannan ta fara tunanin zata yi missing Sumayya da sauran yan gidansu, sai kuma tayi saurin kawar da maganar ta hanyar gayawa kanta cewa ai zata ke yawan zuwa tana ganinsu, suma kuma haka musamman in suka je gidan nata suka ga daular da taje ciki. Kuma zata saka Hassan yazo ya roki Baba ya bar Sumayya ta koma can da zama.

Sai a lokacin taga ana fito kayan gararta, ita bata san ma cewa anyi mata garar ba kuma bata da idea a inda Baba ya samo kudin yin garar. Ta daiji Aunty tana cewa "haba malama Sa'adatu, dan me zaku takura kanku kuce lallai sai kunyi gara? Ai da kun barta kawai" Inna Ade tace "aa auntyn yara, ai babu wani takura kai wallahi, kayan dakin ma dan dai an saka lokacin ne gajere Amma da babansu duk zaiyi dai dai iyawarsa".

Bayan anyi duk abubuwan da akeyi na al'ada cikin barkwanci da wasa da dariya tsakanin bangarorin biyu sai aka bayar da Ruqayyah Aunty ta rungumo ta ta fito da ita ta saka ta a motar da tazo a cikinta ita da hajiyan kano da gwoggo Habibah sauran motocin da suka zo daukan yan uwan amarya suka mara musu baya.

Sumayya ta tambayi inna ta hada yan kayanta a karamar jaka, tana so zata raka Ruqayyah kano, so take sai an gama bikin gaba-daya sannan zata dawo gida. Tun da ta fito kofar gidan ta samu gefe daya ta tsaya hannunta rike da jakarta tana ta sharar hawayen ta tana bin mutanen da suke ta turereniyar shiga motoci da kallo, sai kuma taji tana jin haushin kanta na damuwar da tayi, ita me auren ma ko a jikinta dan ko digon kwalla bata gani a idanuwan ta ba amma ita har nata idanuwan sun kumbura saboda kuka.

Tana tsaye taji mutum a kusa da ita, ta gefen idonta ta gane namiji ne dan haka ta yi saurin juyowa side dinsa a tsorace, ya jefe ta da best smile dinsa, ta ji half of damuwarta ta tafi amma sai ta kara bata rai "har da kai aka zo za'a dauke min yar uwa ta ko Adam?" Yayi dariya "mu menene laifin mu? Gidan miji fa zamu kaita, at least ai yanzu zata daina runton kudin mota" Sumayya ta harare shi "be careful, matar ogan ka ce dai yanzu, or else you get fired" ya saka hannu ya kama bakinsa ya ce nayi shiru, ba zan kara cewa komai ba" Sumayya ta nuna shi tace "you better, kasan Hassan baya wasa da yara" yace "yeah, ba sai kin tuna min ba na sani, Hussain ne mai wasa da dariya, dadinta kuma shi na ke yiwa aiki ba Hassan ba" tace "amma Hassan din ne ya dauke ka aikin kuma he can fire you" yace "to mai mijin sister, naji, can we go now" yayi kasa kasa da murya yace "daga ni sai ke, na boye motar da nazo da ita" ya kashe mata ido.

Yayi gaba, da kamar ba zata bishi ba sai kuma ta juya tana waige waige sai data tabbatar babu wanda hankalin sa yake kanta sannan ta bishi inda taga yayi, tana zuwa ya zagayo ya bude mata kofar front seat ta zauna ya rufe sannan ya zagaya ya shiga gurin driver ya tayar da motar. Sai kuma ta juyo tana kallonsa da budaddun idanunta tace "gidan amaryar zaka kaini ai ko?" Bai kalle ta ba yace "yeah, sure" ta kuma cewa "ba wani gurin zaka kaini ba ko?" Ya juyo yana kallonta da guntun murmushi a bakinsa yace "babu inda zan kaiki, daga nan straight zuwa gidan oga Hassan" tace "ka rantse" yace "I cross my heart and hope to die" ta bata rai tace "da Allah ai nace ka rantse" seriously yace "na rantse da Allah ba sace ki zanyi ba. Can we go now?"

Dogon convoy aka hada ana ta sharara gudu akan titinan garin Kaduna, manyan mata suna ta rangada guda yayinda samari da yammata kuma suke kara volume din kida suna rausaya a cikin motoci, amarya kuwa motarta na tsakiya tana jinta kamar a cikin gajimare take tafiya ba wai a cikin mota ba. Ta lullube fuskarta da mayafinta amma da yake ba mai duhu bane ba tana hango gabanta, a haka har suka isa low cost, har suka shiga jerin gidajen da a cikin films da kuma social media ne kawai take ganin irin su. Ta bude ido sosai zuciyarta tana bugawa da karfi tana son ganin wanne ne nata a ciki, a haka taga anzo kofar gidan tun daga wajensa zata iya cewa kaf jerin gidajen babu wanda ya kaishi kyau da tsari. Aka bude gate, mutane da yawa a ciki mata suna ta guda, wannan ya tabbatar mata da cewa wannan shine gidan nata, sai da motar taje gaban gidan sannan ta lura gidajen guda biyu ne a jere amma ko kusa basu yi kama da junan su ba, na farkon yayi ukun na biyun, tayi murmushi a ranta, maybe na biyun na Hussain ne, ko daga nan wannan so call gimbiyar zata gane tayi mata zarra.
Chapter 36 · 0% Book details