← Book details Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 134

Sashe 41

Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da aka kwashe kayan gara sannan su kuma dangin ango suka shigo da lefe, tun Ruqayyah tana lissafa akwatunan har taji kanta ya fara ciwo ta kwanta a jikin kujera ta rufe idonta, bata son ma ganin kayan ciki tunda ance kazantar da baka gani ba tsafta ce. Sumayya ta kama hannayenta, ta juyo ta kalle ta sai tayi mata murmushin kwarin guiwa, sai taji har Sumayyan ma haushi take bata. Gabaki daya mutanen gurin haushi suke bata, ranta zafi yake yi, zuciyarta ciwo take yi. Ta mike da sauri tana daukan jakarta. Aunty ta riko hannun ta "ina zakije Ruqayyah?" Ruqayyah ta langwabe kai "Aunty kaina yake ciwo wallahi, zuwa zanyi in dan kwanta kafin a gama" Aunty tayi murmushi "Akwai ciwon kai kam, nima kaina ciwon yakeyi, amma zaki iya gane hanya kuwa" Ruqayyah tayi shiru, ita wadannan sorayen da suka wuce ina zata iya gane su? Aunty ta waiga ta kira wata a cikin wadanda ta lura bayin gidan ne tace "dan Allah raka su inda aka sauke mu".

Suna zuwa can Ruqayyah ko ta kan Sumayya bata bi ba tayi kwanciyar ta, taji karar wayarta ta dauko ta taga ten missed calls daga Hassan, hayaniya ce ta hana ta ji. Tayi tsaki ta mayar da wayar cikin jakarta sayi kwanciyar ta.

Sumayya ta bita da kallo sannan ta tabe baki tace "kin dorawa kanki aiki. Babban aiki ma kuwa" a kara gyara fuskarta Sannan ta juya ta koma gurin taron. Ita ba zata iya zama tayi tagumi ba bayan ga shagali can ana yi.

Wannan littafin na siyarwa ne, idan kina so kiyi min magana ta WhatsApp ta wannan number 08067081020Sai magrib aka tashi daga taron, daga nan duk aka dawo masauki aka yi Sallah masu son yin wanka suka yi sannan aka fara shirin tafiya dinner, sai a lokacin Ruqayyah ta tashi tayi sallah sannan itama ta shiga tayi wanka, suka zo suka fara shiryawa, kayan ta data zubo a jakar Sumayya ta dauko, daya daga cikin kayan da aunty ta siya mata ne na fitar biki, tayi kwalliyar ta tsaf ta shirya duk da cewa bata cika make up da yawa ba amma tayi kyau sosai. Sumayya ma tayi wanka ta chanja kaya, suka yi sallar isha i sannan suka fita suka tafi inda sauran mutane suke, ana ta yin make up da daurin dankwali, Aunty ta tambayi Ruqayyah ko tanaso ayi mata amma tace a'a, sai daurin dankwalin ta kawai aka gyara mata. Zuwa karfe takwas aka ce su fito za'a tafi. Sai a lokacin ta dauko wayarta ta kira Hassan, har ya gaji da kira ya hakura. Ring daya ya dauka. "Har na dauka ko an sace min amaryata" ta danyi dariya, "sace wa kuma sai kace kai" yace "ohh abin harda tsokana? To zan rama ne nima zan zo in sace ki kinga munyi one one" tace "ai ni bani na sace ka ba" yace "yeah, ke kika dawo dani gida, and I am never going to forget that" tace "me too". Yace "nayi ta kiranki ne dazu dan in gaya miki mun karaso muma, an kaimu masauki tare dasu Hussain and I was lonely nace bari in kira matata tayi min hira" tace "muna gurin taron can, and the place was so noisy shi yasa banji ka ba, sai yanzu dana dauko wayar sannan na gani. Sorry" yace "it is okay dear. Gamu nan muna shirya wa yanzu zamu tafi dinner" tace "muma haka" yace "okay, I will see you there angel"

Tayi murmushi tana kashe wayar. Sai yanzu taji dadin zuwansa garin, ita sam bata son zuwa gurin dinner din nan dan bata ga abinda zata je ta gani a can ba. Sai yanzu kuma take kara gode wa Allah da Sumayya tayi dabarar sallamar kawayenta da sun biyo ta kano ai da ansha abin kunya. A cikin palace din za'a yi dinner amma sai da aka dauke su a motoci aka kaisu gurin saboda girman palace din, kamar wata duniya suka je.

Suna shiga suka tarar da gurin already da mutane, taji ana zancen harda governor da matarsa ne zasu je gurin. Yanayin tsarin gurin kadai ya isa yasa mutum kamar Ruqayyah ciwon kai. Sumayya sai kalle kalle take tana daukan hotunan yadda akayi arranging tables din gurin da kuma kujerun amarya da ango, ta dauki hoton high table, wannan lallai sai ta nuna wa Inna Ade dasu Sulaiman, wannan lallai sai ta nuna wa Adam.

Ruqayyah ta ja Sumayya zuwa can extreme end din hall din suka zauna, Sumayya tace "nan ai ba gani zamu ke yi ba, Please ki tashi mu koma gaba" Ruqayyah tace "ke da kika zo gani kenan, ni kuma zuwa nayi a ganni and I really don't want to be looked at, dan haka nan zanyi zamana. Ke ma kuma sai ki zaba, gurina kika zo ko gurin bikin gimbiya? The choice is yours" Sumayya tayi ajjiyar zuciya ta zauna tana ta daga kai, sai daga baya ta lura a gefen su ma akwai katon screen da kake iya hango can gaba kamar a gabanka akeyi, just like kana kallon TV. Shikenan Sumayya ta gyara zaman ta da niyyar shan kallo tana yi tana recording as much as she can. Basu jima da zama ba guri ya cika, sai ga Hassan yana kiran Ruqayyah, "kuna ina ne? Ga guri an tanadar mana" ta yamutsa fuska "mun samu guri mun zauna ma, kuyi zamanku kawai" yace "noo, ni ba zan iya zama ni kadai babu ke ba, common ki na ina inzo in taho dake inda nake" ta kwantar da murya "ni ba zan iya zama a can ba, dan Allah ka bar ni inyi zamana anan" yayi ajjiyar zuciya, he thought as much, yaso a rabu da yarinyar nan tayi zamanta a gida aunty tace lallai sai an taho da ita, ita bata saba da irin wadannan abubuwan ba dan haka dole zata jita a takure. Yace "kina ina? Ni sai inzo inda kike" ta gaya masa. Mintuna kadan sai gashi nan yazo, yaci kwalliya kamar babu gobe dan ita kanta tasan yayi kyau. Tayi masa murmushi shima ya mayar mata yana jan kujerar kusa da ita ya zauna. Sumayya ta gaishe shi yace "su Sumayya an samu abinda ake so ko? Biki dai ayi ta hidima dai" tayi dariya tace "eh mana, biki ai lokaci daya ake yinsa daga an gama shikenan" yace "Allah ya kaimu baki bikin to, mu sha shagali har mu gode Allah" ta sunkuyar da kanta tana murmushi. Yace da Ruqayyah "muna shigowa ai Hussain ya kira ni wai gimbiyar sa tana ta nemanki, tana so wai ko zaki shiga cikin friends dinta and I said no, baki san su ba ba zaki ita zama a cikin su ba" Ruqayyah bata ce komai ba sai kira ya shigo wayarsa ya dauka yayi magana sannan ya mike "excuse me ladies, zan je zamu shigo da Hussain. Reserve my seat please dan anan zan zauna"

Bayan fitarsa da kadan sai akayi sanarwar amarya da ango zasu shigo, kowa ya mike tsaye kamar wani president ne zai shigo, suka shigo suna taku dai dai abokan ango da kawayen amarya suna take musu baya, camera tana daukan su ta kowanne angle ana turo hotunan a manyan screens din da suke a gurin saboda wadanda ba zasu iya gano wa ba. Mai video yana dauka tun daga kan takalman gimbiya har zuwa kan sarka da dan kunnen ta, haka shima Hussain aka dauko shi, ba kuma wai shigarsu ko kuma kyawun surar sune abin burgewa ba, a'a, soyayyar junan su da take kwance akan fuskokin su. Kowa ya gansu ya san a cikin farin ciki suke. Ruqayyah ta kifa kanta a jikin table din gabanta tana rufe idonta kamar mai bacci, wannan abin shine abinda tayi ta mafarki zata samu a bikinta tun lokacin data hadu da Hassan. Mutane irin wadannan, governor, ita da mijinta su shigo kowa yana kallon su cike da sha'awa, amma ita nata mijin ma cewa yayi ba zai je kowanne event dinta ba, in dai bai je ba kuwa mutanen sa ba zasu je ba, shi yasa bata yi komai ba saboda baya ga amfanin yin ba tunda so take yayi introducing dinta ga mutanensa a matsayin matarsa ita kuma tayi a matsayin mijinta kuma ceo of h and h group of companies. Now she is just a guess a bikin ceo na H and H group of companies. Jama'ar amarya da ango suna wucewa ta mike ba tare da tace komai ba ta bar cikin hall din ta fita waje, a can gefe taga wata doguwar veranda da kujeru a ciki sai ta tafi can ta ja kujera daya ta zauna sannan ta zubawa bishiyoyin gurin ido tana kallon su tana lissafo rayuwar da take gabanta.

Bakin ciki dai kam tasan zata sha shi har sai ta godewa Allah. Abu daya ne zai saka ba zata fasa auren Hassan ba shine saboda tasan in ta rabu dashi ko a mafarki ba zata samu mijin da ya kai ko da rabin sa bane ba, ceo or not ceo tasan cewa Hassan ba sa'an aurenta bane ba kaddara ce kawai ta hada ta da shi har kuma ta kulla aure a tsakanin su, ta kuma san cewa yana son ta da gasken gaske, dan haka zata yi amfani son da yake yi mata gurin samun cikar burinta. Burinta na auren ceo, bata san yadda hakan zai faru ba bata san ta inda zata fara ba amma tasan abinda take so kenan, abinda ta hango wa kanta kenan. Wannan gidan, wannan valcony din na can sama shi take so. Title din matar ceo na H and H shi take so.
Chapter 41 · 0% Book details