← Book details Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 134

Sashe 63

Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar daga sama taji sallamar Hassan, tayi kokarin kirkirar murmushi dan ta tare shi amma sai ta tuna cewa fada fa suka yi kuma har yanzu basu shirya ba, dan haka ta bata rai ta koma ta zauna tana cika tana batsewa. Taji motsinsa ya shiga dakinta sannan ya dawo palon sannan ya taho dining din, ya tsara yana kallonta ita kuma ta maze tan cigaba da jujjuya abincin gabanta. Ya jawo kujerar kusa da ita ya zauna yana kokarin leka fuskarta sai ta dauke kai gefe, ya danyi murmushi mai sauti "haba my Precious wife, wai fushin ne har yanzu vaki gama ba?" Ya kama hannunta tayi kokarin kwacewa yace "look. Nasan abinda na fada jiya ya bata miki rai, but dole ce ta saka na fada. Kinga munyi aure ne ba tare da mun fahimci halayen junan mu ba, dama nasan dole watannin farkon auren mu a going to be rough on us, tunda a lokacin ne zamu fahimci kanmu, ina son duk abinda nayi miki, ko menene wanda kika ga ba kya so dan Allah ki fada min dan in san cewa ba kya so kinji? Ni ma kuma in kika yi min abinda bana so zan gaya miki kinji? Kamar jiya, na gaya miki bana son jin magana marar dadi akan Hussain saboda bana so din, idan kuma ban gaya miki ba ai ba zaki sani ba ko? I know I was harsh a magana ta but kiyi hakuri raina ne ya baci saboda abinda kike fada kina kara maimaita wa. Na sani Hussain dan Adam ne kamar mu, kowa kuma yana da bangaren sa mai kyau da marar kyau dan haka duk wasu halaye na Hussain na sani bana bukatar ki gaya min su. Kinji?" Ya saka hannu ya juyo da fuskarta da take zubar da hawaye yana kallo sannan ya girgiza mata kai yace "ya isa haka, ko nima so kike inyi kukan?" Ta turo baki "ba kai ne kace baka sona ba wai kafi son Hussain a kaina" yayi dariya "ohh kukan kishi ne ashe kike yi. To bara in gaya miki Hussain side dinsa daban a zuciya ta kema haka. Kin san wani abu? Sai da na aure ki ne fa na zama complete mutum, Hussain yana tare da ni tun a ciki amma ba zai iya completing dina ba sai ke ce kika iya. Kin gane banbancin?" Ya kamo ta yana dawo da ita cinyarsa, ya dora kansa ya wuyanta yace "ga kuma babies zaki bamu, abinda Hussain ba zai taba iyawa ba. Kuma bara kiji, kamar yadda nayi defending Hussain a gabanki haka zanyi defending dinki a gaban Hussain idan ya taba ki because you are my precious wife". Tayi kokarin tashi ya dake riketa, "Please ki ce min kin hakura komai ya wuce kinji? In ba haka ba tuwon nan ba zai iya wucewa cikina ba"

Ta bata rai tana kara kwanciya a jikinsa tace "tuwon ma babu dadi ai" ya jawo plate din yace "me ya same shi?" Tace "har na shiga kitchen din zan fara girkin kuma amai ya hanani, bana son mixed kamshin abubuwan girki, shine na barwa yaran nan suyi kuma gashi bai yi dadi ba" ya ture plate din yana cewa "it is okay, bara in samo mana wani abun ko a gurin aunty ne" tace "aunty kuma? Kar ka takura mata mana" ya mikar da ita tsaye shima yana mikewa yace "no, babu wani takura ai tasan baki da lafiya, daga nan ma sai ce ta samo mana cook mai tsafta sosai tunda dai babies sun hana maman su girki" ya karasa yana tsokanar ta sannan ya fita, ta zauna tana jin kalmar maman babies tana bata mata rai, sai kace ita ce Inna Ade da ake cewa uwar biyu.

Sumayya bayan ta shiga gida su Inna suka yi ta mamakin ganin ta haka da sassafe, sai tace musu kawai tayi kewar gida ne shi yasa ta dawo, amma Inna Ade ta lura da damuwa a fuskarta. Sai data bari ta shiga daki tana gyara kayanta sannan ta bita ta zauna tace "ya kika baro su Ruqayyah? Jiya da dare da muka ganta naga tayi girma sosai, kamar hankalin ta a kwance yake ko? Bata da damuwa ko?" Sumayya ta ajiye kayan hannunta ta dawo kusa da Inna Ade ta zauna tace "bana jin Ruqayyah tana da damuwa Inna, ki kwantar da hankalin ki, mijinta da surukan ta suna da kirki sosai kuma suna son ta sosai" sai kuma ta dan yi shiru idanunta a kasa, Inna Ade tace "sai dai kuma me? Akwai magana a bakin ki ki gaya min mana wani abun ya faru ne?" Sumayya tace "kawai dai ina tsoro ne Inna, kin san halin Ruqayyah tun tana gidan nan, yanzu kuma tayi aure ga kuma irin gidan da tayi auren a ciki, cikin yan kwanakin nan da auren nata har idanunta sun kara budewa sosai, ta kara chanjawa sosai, ina tsoron nan gaba kar ta kauce hanyar da kika dora mu akai Inna, so nake kiyi tayi mata addu'a Inna" Inna Ade tayi ajjiyar zuciya tace "ko sau daya ban taba cire wannan tunanin daga zuciyata ba Sumayya, kullum ina yi muku addu'a gabaki dayan ku kullum dare sai na tashi nayi muku addu'a neman tsari daga shaidan, mutum da kuma aljan. Kuma na tabbatar ubangiji ba zai jiyar da addu'a ta ab saboda yayi alƙawarin amsar addu'ar uwa akan ƴaƴanta. In sha Allah yar uwarki ba zata tabe ba. Xan kara wata addu'ar akan wacce already nake yi kullum.

Sumayya taji dadi kuma taji hankalin ta ya dan kwanta, tasan babu abinda addu'a ta bari dan karfin addu'a yakan iya chanza kaddarar mutum gabaki daya.

Cikin kwana biyu Ruqayyah ta kuma dawo da mijinta gare ta, ta kuma fara shiga cikin yan uwansa kamar yadda Minal ta bata shawara. Idan ya fita itama sai ta shirya ta tafi part din aunty tayi zamanta acan, ba zata dawo ba sai yayi mata waya yace gashi nan zuwa sannan zata debar musu abinci ta tafi can ta kuma shirya tayi masa kwalliya kafin ya dawo. Wannan yasa shima ya wanke zuciyarsa gaba ki daya akan waccan maganar yake enjoying matarsa.

Motocin su da Hussain ya siya musu ita da Fatima sun iso kuma Ruqayyah tayi murna sosai dan bata dauka haka motar ta hadu ba sai da tagan ta kiri kiri sannan ta kuma fahimtarta. Hassan ne yayi suggesting ya kamata ta shirya taje gida ta nuna musu motar dan tun da suka dawo bata je gidan ba. Dan haka ta dauki kayan tsarabarsu sannan shima kuma ya dauki kudi masu kauri ya bata yace ta kai musu, sai ya hada ta da driver yace ya kaita tunda bata fara koyon motar ba tukuna. Dan haka hankalin ta kwance ta tafi a zuciyarta tana plan din daga can zata biya ta gidan su Minal suje gurin malamin nan mai addu'a.

Tana shiga soron gidan taga Adam yana fitowa daga dakin su Sulaiman. Yana shafa kai yace "welcome Madam" ta watsa masa harara tare da jan dogon tsaki ta wuce cikin gidan sai yayi murmushi kawai ya fita. Tana shiga Zunnur yana ta murnar ganinta amma ita da fada tafara "me wancan kedarin yake yi a gidan nan? Duk ya cika masa gida da warin karti" Sumayya da take daki suna waya da Adam yana gaya mata ya gama zai tafi ta fito tana kashe wayar ta nuna ta "kar ki kuma, wallahi Ruqayyah ki fita daga idona na gaya miki" Ruqayyah tace "in na kuma nace sai me? Me zakiyi min? Wallahi sai ya daina zuwa gidan nan ai badan irin su Hassan ya sai gidan ba" Sumayya tace "to maza, yi mana gorin cewa mijinki ne ya siya mana gida, dan ma dai ba rokar sa mukayi ba kuma daya siya din ba ke ya siya wa ba Baba ya siya wa dan haka baki da iko da gidan" Ruqayyah tace "amma dai saboda wa ya siya? Saboda ni ya siya baby girl amma ina da say akan waye zai ke shiga gidan nan yana fita kuma wancan katon kedarin baya daga cikin su"

Inna data rike baki tana kallon su tace "to kuyi dammara ku daku a gaban kannen ku kunji. Akan saurayi zaki yi fada da yar uwarki Sumayya? Ke kuma akan wata akida taki ta daban zaki yiwa yar uwarki damu iyayenki gori cews mijin ki ya siya mana gida? Ruqayyah? Har kin kai haka? Har kin yi girman da zaki yi mana gorin gida Ruqayyah?" Ruqayyah ta zauna taa magana kasa kasa "ni ba gori nake muku ba inna, ni kawai mutumin nan ne bana son yake zuwa gidan nan wallahi. Na tsane shi bana son ganin sa" Sumayya ta bude baki zata yi magana sai kuma ta kalli Inna ta juya ta koma daki tana rufo kofa. Tana ragawa Ruqayyah akan komai amma ta rasa me yasa bata iya raga mata akan Adam. Ko da wasa bata son Adam yaji irin maganganun da Ruqayyah take fada akan sa, babwai dan tana son sa a matsayin saurayi ba sai don tana sonsa a matsayin sa na wanda yayi loosing everything for islam.

Inna ta jima tana yiwa Ruqayyah fadan abinda tayi sannan kuma ta koma yi mata nasiha, daga nan kuma sai suka shiga hira. Su Sulaiman da suka tafi dauko kaya daga mota suka suka dawo suna baje kayan anan tsakiyar palo kowa yana diban nasa. Ruqayyah ta dauko na Baba ta bawa Inna ta ajiye masa sannan ta bata nata itama. Ta ware na Sumayya gefe tace "ita kuma wannan inntaga dama ta fito ta dauka to in kuma tayi fushi in kinyi bakuwa inna ki bayar" Sulaiman yayi dariya yace "babu wanda zai shiga tsakanin ku dan duk wanda ya shiga to kuwa zai ji kunya" duk suka yi dariya amma ita Ruqayyah bata ga abin dariya a cikin fadan su da Sumayya ba, ita bata san me yasa suke daukan lamarin Adam for granted ba. This is very serious issue amma su suna dariya akai.
Chapter 63 · 0% Book details