← Book details Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 134

Sashe 70

Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tace "ah ah. Me kake so ne ince mijina? Ina nufin kamfani nasa ne, gidan nan da muke ciki nasa ne, motar da kake hawa tasa ce, motar da nakr hawa shi ya siya. Komai da muke takama dashi a rayuwa nasa ne" ya ture hannunta daga jikin da ya mike tsaye, idanunsa sunyi ja jijiyoyin kansa sun fito, ya bude bakinsa zaiyi magana amma voice din ya kasa fitowa saboda ciwon da zuciyarsa take masa, da kyar yace "I understand. I now understand everything. Ni da ke Hassana yanayin yadda muke kallon rayuwa ba iri daya bane ba. Rayuwa ni a gurina ba wai tana revolving around yawan kudin da kake dashi bane ba, tana revolving ne around things that are much more important than money, like love, honor, friendship. But you have no idea me wadannan suke nufi do you? Yes, Hussain yana da kudi, but that doesn't mean ni bani da komai. Yes, gidan sa ne wannan shi ya gina da kudin sa but that doesn't mean ni bazan iya gina nawa ba. Na karba na zauna a ciki ne dan in faranta masa tunda burinsa shine mu zauna tare mu da iyalin mu, saboda yana so na, nima kuma na karba saboda ina son sa. Na fasa gina mana namu gidan ne saboda in siya wa Baba gida, saboda naga yafi mu bukata, saboda ina ganin sa kamar family na ne shima"

"Ruqayyah bayan rai da lafiya da imani da Allah ya bani sai ya bani family, Aunty da siblings dina, masu sona sosai yadda na tabbatar ko da bani da komai zasu kula dani, ko d abana duniya zasu kula da bayana. Sannan ina da aikin yi ba zaman banza nake yi ba, wahalar da nake yi a aikin nan shi kansa Hussain yasan cewa ko shi baya yiwa kamfanin nan wahalar da nake yi masa. Ke kinfi kowa sanin cewa albashi na can more than sustain me, you and ko yaya nawa zamu haifa. And I have these...." Ya fada yana nuna babies din da suke bacci abin su "I have abinda babu wanda ya isa ya samar wa kansa sai Allah ya bashi. Do you know that last week Fatima ta matsawa Hussain sun fara zuwa ganin fertility doctor? Suna nema but mu Allah ya bamu gida biyu" ya tsaya yana kallon ta da jajayen idanuwan sa yace "I tot I also have a pious wife. Ashe I was wrong" ya bude toilet ya shige ya rufo kofa. He just can't stand the sight of her.

Ta mike tsaye tana kallon kofar toilet din, tunda taaure shi tasan baya son nonsense shi yasa kullum in suna magana take jinta kamar mai tafiya akan tight rope kamar slight mistake in tayi zata fada ramin da ba zata iya fitowa daga ciki ba. And yau ta tabbatar da haka.

Ta mike itama ta fice daga dakin ta koma nata dakin, tasan dama dole watarana sai haka ta faru a tsakanin su amma bata dauka hakan zata faru da wuri ba, plan dinta shine ta haifa masa as many yaya as possible yadda babu yadda zai yi da ita. Ta tsaya tana kallon sticker din data lika a jikin mirror dinta

"Have you taken your pills today?"

Sai ta saka hannu ta cire ta ta yar. Ta jawo drawer din da birth control pills dinta suke ta kwashe su gabaki daya taje ta zuba a waste bin. In yasan wata ai bai san wata ba. Ta kashe fitilar dakin ta kwanta, tana jin haushin sa a ranta, har da gori ma yayi mata wai ya siya wa baban ta gida.

Tana jinsa ya shigo dakin, ya jera mata yayan ta a kan gado, yayi musu addu'a ya shafa musu sannan ya tashi ya fita. Ta juyo tana kallon yaran, sai kuma tayi murmushi, dolen sa yayan ta ne yaya kuma dole sai uwarsu.

And yes. Hussain da Fatima sunje sunga fertility doctor a Washington DC. Doctor din yana kallonsu yana murmushi yace "one year you said?" Hussain ya daga kafada yana kallon Fatima da take twisting hannunta yace "she insisted sai munzo" doctor din ya juya yana kallon ta yace "am sure babu wani abu madam, but zamuyi running some tests dan mu tabbatar babu komai din. Pregnancy takes longer to get in some couples than in others ba tare da wani dalili ba".

Daga nan aka fara yi musu tests, a dauki jini a dauki fitsari, vaginal swab, sperm samples da sauransu. Kwanan su biyu ana ta faman abu daya, Hussain dai yana zuwa ne saboda ya farantawa Fatima amma shi a ransa yasan babu mai bashi haihuwa sai Allah. A week after aka kira su karbar result, suka zauna kamar yadda suka zauna last week, Fatima looking very nervous while Hussain is relaxed yana ta tsokanar ta. Doctor din shima ya dan tsokane ta kadan sannan yace "results dinku gasu nan sun fito gabaki daya, amma babu wani problem da muka gani, gabaki dayan ku lafiya lau kuke kuma zaku iya samun haihuwa a kowanne lokaci. Abinda zamu iya yi muku na taimako kawai shine zamu baku magunguna da zasu yi boosting fertility dinku sannan zamu baku shawarwarin da zasu taimaka muku sosai da kuma diet din da shima zai taimaka wajen boosting fertility din. Most importantly kuma ke Madam dole kiyi relaxing ki kwantar da hankalin ki saboda anxiety, rashin kwanciyar hankali, yawan tunani da damuwa duk suna affecting fertility din mace" Hussain ya juya yana kallon Fatima tare da kama kunnensa daya yace "kina dai ji ko? To babu ruwa na" tayi murmushi.

Aka gama yi musu bayanin duk da za'a yi musu, aka basu drugs dinsu aka sallame su. A hanya Hussain ya tasa Fatima da tsokana. "Sai kin shirya fa, tunda dai kinji sunce yawan yin abin nan yana kara chances, to double za'a ke yi yanzu" ta harare shi "to ayi double din ma mana, kasan dai ai bana jin tsoro ko?" Yace "kar ki cika baki fa? Sai kuma anzo gurin kuma ki fara neman a tausaya miki. To babu tausayi yanzu yarinya in....." Ta rufe ido "ka daina dan Allah kunyar ka nake ji fa" yayi dariya "to zamu karasa maganar a turaka".

Washegari da safe karar wayarsa ce ta tashe shi, ya daga cikin muryar bacci yana cewa "Hello. Who is on the line please?" Daga can aka yi masa bayanin cewa doctor din daya gansu ne yake son ya dawo shi kadai, akwai maganar da za'a yi masa. Ya ajiye wayar yana danyin tsaki, ya koma ya kwanta yana kara jawo Fatima jikinsa sai kuma ya mike, ya sake tsaki sannan ya shiga toilet. Mintuna kadan har ya fito, motsinsa ya tashe ta ta dago kai tana kallonsa "ina zaka je?" Yana daura agogo yace "zan dan fita, ki koma baccin ki yanzu zan dawo. Zan yi musu magana su kawo miki breakfast" ta tura baki "bayan ka hana ni bacci da dare ba dole in rama ba yanzu? Ba sai sun kawo ba dan ni banga ranar tashi na daga wannan baccin ba. In ka dawo ka taho mana da shi" yayi murmushi, "better eat something Madam, kar in dawo kuma kice ke ga zance ga magana. Cos da nayi niyyar mu koma Nigeria gobe but yesterday night ta saka na chanja shawara, sai next week zamu koma. Anan za'a yi making baby din" ta dauki pillow ta jefa masa, sannan ta rufe fuskarta da wani pillown.

Direct gurin doctor din ya koma, zuciyarsa tana ta yi masa sake sake iri iri. Doctor ya kalle shi da murmushi yace "kar ka damu da wannan kiran, I hope bamu tayar maka da hankali ba" Hussain yace "it is okay. What's up?" Doctor yace "result din da aka baku still stands, babu wani chanji. But a cikin gwaje gwajen da muka yi muku munga something da muke tunanin ya kamata ka sani kuma kayi taking action akai. It is just a suspicion Sir, we are not sure. Sai dai in ka yarda zamu tura ka gurin doctor din da zai sake maka wasu tests din for confirmation" Hussain ya gyara zaman sa yace "menene wai doctor, just say it" doctor ya gyara zama yace "we suspect that you have a column cancer"

Yana shiga hotel room din ya bude labulen da sauri, haske ya shigo ya haske dakin. Fatima ta daga kanta tana kifta ido tana adjusting to light din sannan tace cikin muryar bacci "har ka dawo? Ka taho da abincin?" Yace "tashi ki shirya, we are taking the next flight back to Nigeria" ta mike zaune tace "What? Why?" Yace "I said we are taking the next flight back to Nigeria" yanayin muryarsa ya sa ta san da gaske yake, ta san kuma something has happened.

Wannan littafin na siyarwa ne, idan kin ganshi a wani guri na sata ne, in kina so ki karanta halaliyar ki ki yi min magana through WhatsApp ta wannan number din 08067081020*The Brothers*

Cikin mimtuna kadan suka gama hada kayansu, ita dai duk bata yarda da yanayin sa ba tace "wai me ya faru a Nigeria ne? Ko wani ne ya mutu aka gaya maka?" Ya kalle ta yana kokarin kirkirar murmushi yace "babu wanda ya mutu fa, kawai ji nayi ina missing Hassan" ta kalle shi kawai amma a ranta bata yarda da uzurinsa ba tace "Hassan din da kuna haduwa zaku fara rigima? A waya ma ina jin ku kuna yi" yace "mun daina daga yau, daga yau ba zan sake fada da Hassan ba ko ya neme ni da fadan ma cewa zanyi ni bana fada" tayi dariya, shima yayi, at least ta dan ji dadin ganin yayi dariya hakan yana nuna mata ba mutuwar akayi ba, but something is definitely up.
Chapter 70 · 0% Book details