← Book details Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 134

Sashe 76

Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai daya tabbatar jikinsa yayi kyau sannan ya kira Fatima video call, suka yi hirar su ya tabbatar mata nan da kwana biyu zasu dawo, dan shi kam ya gaji ko ba'a sallame shi ba guduwa zaiyi.

*Nigeria*

Tun bayan tafiyar su Hassan sai Ruqayyah ta samu sake, a lokacin ne ta samu damar zuwa ta ga dakin Minal. Gidan ta mai kyau kuma mai girma part dinta daban na uwargidan ta daban, shi kuma mijin ya raba kayan sa a tsakanin su tunda akwai dakin sa a kowanne part. Minal ta baje sosai abinta ta na zuba wa uwargida rashin kunya son ranta yayin da shi kuma mijin ya ja bakinsa yayi shiru, yan uwan miji ma sun fara dawowa gurin Minal musamman uwar mijin da shekarun ta suka riga suka ja kuma bata da buri irin taga jikokin ta daga ɓangaren Alhaji Kabiru kuma a yanzu dukkan hopes dinsu yana kan Minal tunda suna ganin cewa rashin haihuwar daga matar ne ba daga mijin ba. Wannan yasa uwargidan mai suna Hajiya Baraka ta ja kofar part dinta ta rufe, bata gani ba ballantana ranta ya baci, babu mai shigar mata sai nata bakin idan sunzo, sai kuma mijinta idan ranar kwanan ta ce.

Ranar wuni suka yi suna hira, farko Minal ta nuna fushin ta akan kin zuwa bikinta da Ruqayyah tayi, daga baya kuma sai ta sauko ta nuna dama ai tasan wannan matsolon mijin na Ruqayyah ne zai hana ta zuwa dan kar ya kashe kudi. "Ni dai Ruqayyah da Allah ya bani miji irin naki gwara in yi ta xama a gida, ya za'a yi ina kallon dukiya kuma ace ba zanyi abinda nake so da ita ba? Kema walllahi da laifin ki, ai wallahi idan ni ce ba ka isa ba, a matsayin na na matar ka sai nasan yadda nayi na lankwasa ka kabi ra'ayi na wallahi" Ruqayyah ta tabe baki tace "kema dai kya fada Minal, ke ni fa duk kwanan nan abubuwa sun cushe min wallahi, ji nake yi ma kamar ba ya sona yanzu. Irin soyayyar da nake gani a idonsa yanzu duk sai inga kamar babu" Minal tace "haba dai! Kuna nufin ki ce min babban makamin naki ya ragu? Soyayyar da yake miki ce fa take rike dake a gidan, wallahi kar ki bari ta tafi, chafdi, ki zo mu koma gurin Malam a juyo miki da hankalin sa kachokan ya dawo kanki. Ke ba ki ga yadda mai gidan nan da yan uwansa suke rawar kafa a kaina ba? Ai ba haka na barsu ba fa".

Ruqayyah ta dauke kai gefe tace "ke raba ni da wannan malamin duban, ki barni kawai zan samar wa kaina mafita dan ni tsoron malaman nan nake yi wallahi, na tabajin ance aikin su gaba yake ci sannan ya dawo ya ci baya, ku barni in lallaba kawai" Minal tace "sai kiyi ta lallabawar ai. Ni kam babu wata lallabawa da zanyi a rayuwa" sai kuma tace "ni bamu yi maganar wannan maganar da Malam yayi a kanki ranar nan ba, na cewa zakiyi kudi. Kinga fa maganar sa ta fara tabbata tunda gashi kin haifi yara biyu kamar yadda yayi alƙawari" Ruqayyah tayi murmushi tace "maganar da nake miki kenan ta lallaba war ai, na sani duk wani kudi da zan saka ran yi to ta hanyar Hassan zai taho, dan haka nake lallaba abuna har zuwa lokacin da zamu ga abinda rayuwa zata zo mana dashi kuma" Minal tayi dariya tana dan dukan Ruqayyah tace "munafuka, ashe dai kim yarda da Malam din tunda kin yarda da maganar sa. Ina tabbatar miki da cewa abinda ya fada zai faru din. Ni dai fatana daya shine Ruqayyah kar ki samu duniya kuma ki manta dani, ko me kika samu ina so na zama a hannun daman ki" Ruqayyah tace "a'a ban yi miki wannan alkawarin ba Minal, za dai ki zauna a hanun hagu na amma Sumayya ita ce a hannun dama na" Minal ta bata rai, "shikenan tunda wariya za'a nuna min, hannun hagun ma ban raina ba".

Sai dare Ruqayyan ta koma gida, bata shiga gurin Aunty ba dan kar tayi mata fadan ina taje ymtayi dare haka sai ta wuce part dinta ta hau sama direct tunda ta riga taci abincin ta a can gidan. Tayi wa yaranta wanka tana ta yi musu wasa suna dariya gabaki daya, tana jin son si sosai a zuciyarta irin son da bata taba yi wa kowa irinsa a duniya ba. Sai dai kuma a ranta tasan bata son su taso a karkashin masu kudi, tafi son su taso a matsayin masu kudi kuma tasan she is going to make the right decision at the right time. Ta dauki wayarta ta kira layin Hassan na india. Kullum kamar lokacin suke yin waya duk da shi a gurinsa cikin dare ne amma ta fahimci kamar baya bacci sosai, ko kuma da rana yake baccin ne oho.

Ring daya ya dauka yace "yanzu nake tunanin kiran ku inji yadda yarana suka wuni" ta bata rai kamar yana kallonta tace "yaranka kadai? Ni ba zaka ji yadda na wuni ba? Allah sarki ni babu mai sona" ya danyi murmushi yace "ni na isa ince haka? Kin san yadda kike hana min bacci kuwa?" Tace "kamar gaske, baya ka fin ku tafin ma wani shashshare ni kake yi" yace "na tuba ai, kwana biyu da babu ke ai jiki na ya gayamin" tace "kai da baka da lafiya? Ko dama ciwon na yan gayu ne" ya danyi dariya, sai taji wani iri, yaushe rabon da taji yayi dariya ko a wayar ne tana iya jiyo rashin nutsuwa a muryarsa, tace "masha Allah, jiki yayi sauki kenan" ya juya ya kalli Hussain da yake ta danne danne a wayarsa, yace "sosai ma, alhamdulillah is all we can say" tace "alhamdulillah. Sai shirin dawowa kenan ko? Kaga ni ina son mijina ya dawo fa" ta fada da shagwaba, ya sake dariya "ki sha kurumin ki yarinya, in nazo har sai kin gaji dani". Suka jima suna hirar su, ko da wasa bata gaya masa taje unguwa ba, ta kara wa yaran wayar duk da basu san me take yi ba amma shi ya jiyo motsinsu kuma yaji dadi a ransa. Tabbas yaya rahama ne dan komai bacin ra sa ko zancen su yaji anyi sai yaji ransa yayi dadi. He can't imagine zuciyar Hussain, bayan wannan ciwon kuma ga babu haihuwa yet.

Washegari ta tashi da gyaran dakinsa tunda taji yace sun kusa dawowa. Duk da dai ba wani datti dakin yayi ba dan fes ya tafi ya barshi kuma tunda ya tafi bata bude dakin ba. Ta dan karkade kura ta gyara abinda yake bukatar gyara sai ta bari da niyyar sai ana gobe zasu dawo sai ta kuma gyarawa ta wanke toilet. Anan taga system dinsa a kan study table dibsa tare da takardu, ita ta dauka da ita ya tafi dan haka bata lura ma da ita a gurin ba, sai kawai ta dauka ta hau kan gado ta bude ta fara dudduba abubuwan ciki, babu komai dan shi ko irin videos din nan ma ba ajjiyewa yake yi ba duk yawancin tarkacen kayan office ne, har tayi kamar zata rufe sai kuma zuciyarta ta raya mata cewa ta duba e-mail dinsa, maybe ta samu something interesting. Ta bude ta fara bin mails din briefly, suma duk tarkacen office ne dan ba ma gane me ake cewa take yi ba. Sai kuma idonta ya sauka akan wani "re_suspected Cancer patient" ta bude ta karanta, ta kuma karantawa tana so ta fahimta, ta dauko wayarta tana duba ma'anar wasu daga cikin kalmomin da akyi amfani dasu, sai da tayi wa e-mail din filla filla sannan ta fahimci cewa wani doctor ne a india ya rubuto yana gayyatar "Hussain Aminu Abdullahi" yaje za'a yi masa gajin cancer. Ta duba date din taga kwanaki kadan kafin tafiyar su, sai kuma taga wani email ne na Hassan wanda ya turawa doctor din akan yana son ganinsa amma kuma info din na Hussain ne.

Ta cigaba da bincike amma takasa samun wani abu da zai kara fahimtar da ita cikakken ma'anar abinda ta karanta din, Cancer, Hussain, India. Haka ta wuni da abin a ranta kuma can kasan zuciyarta tana jin wani excitement yana taso mata. Tana jin maanar abin tana kwanta mata a zuciyarta, Hussain yana fama da cutar cancer, wannan shine dalilin zuwansu India ba wai zazzabin da Hassan yayi ba. Yes, ta samu wannan information din amma me ya kamata tayi dashi? Ta yaya zata yi amfani dashi to her own advantage?

Sai dare sannan ta yanke shawara. Dakin Hassan ta koma ta samu wata newspaper ta zauna tana duba front page din a hankali har taga hotline dinsu, ta dauka a wayarta sannan ta sauka kasa ta aika a ka siyo mata sabon sim card, ta dawo dakinta ta zauna ta saka a wayarta sannan ta nemo waccan number din data yi saving ta tura message.

"Hussain Aminu Abdullahi, the CEO of H and H is suffering from cancer and currently receiving treatment in india"

sai ta rubuta address din asibitin data gane tare da email din ta tura. Sai data tabbatar ya tafi sannan ta zare sim card din ta balla shi ya jefar. Tayi murmushi yana jujjuya wayar a hannunta. "Let's see how Fatima will react to this".

**********. **********. *********

Tun tafiyar su Hussain Fatima bata jin dadi, ji take gabaki daya kamar duniyar tayi mata zafi duk kuwa da cewa kullum suna makale a waya amma empty take jin duniyar ta. Wannan yasa ta roke shi akan zata je kano ta dan zauna kafin ya dawo, bai yi tunanin komai ba ya bar ta ta tafi saboda tunda akayi auren su bata taba zuwa ta zauna a gida ba, on few occasions ne yake barin ta tayi weekend kuma yasan tana missing gidan sosai duk da bata taba yi masa complain ba. Babu bata lokaci ta shirya ta tafi, sai ta dauki Khadijah suka tafi tare dan babu abinda take yi a gida a lokacin.
Chapter 76 · 0% Book details