Sashe 103
Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tayi kokarin tambaya "me muke yi anan? Ina ne nan?" Amma sai taji bata jin maganar tata. Sai ta tuna da abinda ya faru da ita a jirgi, the pain, the blood, sai ta saka hannayenta biyu tana dukan kunnuwan ta dasu "menene ya samu kunne na? Wayyo Allah na na shiga uku, menene a kunne na? Hassan, mijina ka taimaka min wani abu ya shigar min kunne na" Hassan ya fara kokarin kamata, yana yi mata magana, tana ganin bakinsa yana motsawa amma sam bata jin abinda yake fada, tana ganin Sumayya tana kuka tana magana amma ita ma bata jin abinda take fada. Ta kara rikicewa, ta mirgino ta fado daga kan gadon, ta fara kokarin tashi amma kafa taki cooperating. Hassan yayi sauri ya daga ta yana kokarin rungume ta ya lallashe ta amma taki barin shi, kuka take yi tana magana da karfi tamkar zata tsaga masa nasa dodon kunnen, babu shiri Sumayya ta kwantar da Hussain shima da hayaniyar uwar ta sa ta tashe shi ya fara kuka ta fita waje da sauri ta samo nurse, haka suka hadu da kyar suka rirrike Ruqayyah sannan suka sake yi mata wata allurar baccin ta koma.
Kafin dare labari ya iske gida, Aunty ta hada Nafisa da Zulaihat sannan suka biya suka dauko Inna da sassafe suka taho Abuja, lokacin da suka isa har an shiga da Ruqayyah dakin da za'a yi mata aiki dan haka sai suka hadu da Sumayya suka zauna zaman jira kawai da addu'a a bakin ta na samun nasarar yin aikin. Nafisa tace "ni ban taba ji ba, ko a labarai ban taba jin wanda ya samu irin wannan problem din ba kawai dan ya hau jirgi. Kuma jirgin nan ba yau ta fara hawansa ba da duk bai sa mata ciwon ba sai yau?" Sumayya tace "doctor din yace ana samu but it is very very rear. Amma yana saka ran success a surgery din sai dai kuma babu sake shiga jirgi a gun Ruqayyah" Zulaihat tace "to wa yake ta shiga jirgi kuma? Ana maganar lafiya? Fatan mu dai kawai ta samu lafiya dan itace tafi komai muhimmanci yanzu a gare ta" Sumayya ta gyada kai, amma a ranta tasan maganar shiga jirgin nan ba karamin taba zuciyar Ruqayyah zata yi ba. She is not going to like the news.
Alhamdulillah anyi aiki lafiya an kuma gama lafiya, aka turo Ruqayyah aka fito da ita yan uwanta suna ta bin ta da addu'a kowa yana cikin alhini da tausayin ta. Inna kuma ta na tayi mata addu'ar Allah ya bata karfin zuciyar da zata karbi kaddarar ta da hannu bibbiyu. A haka har ta farka, ta gansu a zagaye da ita suna kallon ta, Sumayya ido ya kumbura saboda kuka, still tana jin wannan feeling din marar dadi a kunnenta. Ta saka hannu da niyyar bubbuga kunnen wai ko zai bude amma sai ta ji su a nannade da bandage, sai a lokacin tunani yazo mata, tunanin irin azabar da taji a kunnenta lokacin da jirgin su ya tashi da kuma yaddata taba taji jini yana fitowa daga kunnen. Bata bukatar tambaya tasan ta samu matsala a kunnenta, bata bukatar tambaya tasan tafiyarta zuwa Germany ganin likitan kafa bata yi ba, sai ta fara kuka a hankali ba irin na jiya ba, tana kallon yadda bakunan su suke motsawa tasan sannu suke yi mata da kuma kokarin bata hakuri amma sai ta mayar da idonta ta rufe tana cigaba da kukan ta dan ba jin abinda suke cewa take yi ba. Wannan wacce irin mummunar kaddara ce? Ita Ruqayyan ita ce ta kurumce bayan kuma kafar ta da har yanzu aka kasa gane menene matsalar ta?
Babu wanda bai tausayawa halin da Ruqayyah take ciki ba musanman Hassan wanda bayan ta tashi ya fahimci bata jin abinda suke cewa sai ya koma gurin doctor da complain, amma sai doctor din yace masa ai ba yanzu ne zata ji din ba sai aikin yayi healing an kunce bandage din. Sai nan da sati biyu masu zuwa tukunna sannan za'a tabbatar da success din surgery din ko akasin haka.
A cikin sati biyun nan Hassan da Sumayya sun kasance tare da Ruqayyah, supporting her, encouraging her tayi accepting duk abinda result din ya nuna amma ita ta tubure so take yi su bar asibitin, su bar Nigeria gabaki daya su tafi kasar waje tunda ita a ganinta acan ne zata samu lafiya, gani take nan kawai karasa lalata mata kunnen zasu yi ga kuma kafarta da take getting worst everyday. Sai dai har yanzu Hassan ya kasa samun courage din gaya mata abinda likita yace, tausayinta yake ji, ya kasa samun right time da zai ganta cikin mood mai kyau yayi mata bayani, kullum cikin kuka take, kullum cikin mita take. Ga magana da karfi in ya nuna mata ta rage Muryar ta sai ta fara kuka tana ganin kamar yana mocking dinta ne. In zasuyi mata magana a takarda suke rubuta mata, in zata basu amsa kuma sai ta fada, da karfi kamar zata tsaga dakin. Ta zama very edgy, abu kadan sai fada sai kuka shi har tsoron shiga dakin yake yi gurinta shi yasa yake jinjinawa kokarin Sumayya dan tunda suka zo tana tare da Ruqayyah ko nan da can bata zuwa tana ta hidima da Hussain ga kuma nata ciwon da yake cin zuciyarta na rashin sanin inda Adam yake. Amma bai taba jin tayi complain ba ko sau daya. Wannan yasa ya karbi Hussain daga hannunta ya mayar dashi Kaduna gurin Inna aka cigaba da bashi madara dan ga uwar tasa nan amma ba samun shan nonon yake yi ba madarar ake bashi.
Ranar da sati biyun suka cika a ranar ne aka budewa Ruqayyah bandage din kunnen ta, doctor din ya kunce tare da wanke kunnen a gaban Hassan da Sumayya sannan ya gwada yiwa Ruqayyah magana "Hajiya Ruqayyah, can you hear me?" Ta juyo tana kallon sa, tana ganin bakin sa yana motsawa sannan tana jiyo Maganar sa can nesa kamar irin ana hira a makota din nan. Bata fahimtar abinda yake cewa sai data tattara dukkan hankalin ta a guri daya sannan ta fahimce shi, ta rufe idonta hawaye yana zuba, tace "ina jin ka, amma bana fahimtar ka, maganar bata clear" sai doctor din yayi murmushi cikin jin dadi yace "alhamdulillah. An samu nasara kenan" duk suka kalle shi cikin mamaki, Hassan yace "an samu nasara fa kace, bayan kana jin tace bata fahimta? Menene amfanin ji idan ba'a fahimta?" Doctor din yace "jin shine babbar nasarar da muka samu, ear drum din ya gyaru kenan ya fara receiving sound. Clearing sound din kuma sai anyi mata taimako da hearing aid. Zai kara enhancing ya kuma kara clearing din sounds yadda weak ear drums dinta zasu karbe shi sosai"
Ruqayyah dai tana kallonsu suna ta magana, bata jin mai suke cewa tana dai jin mixed voices dinsu kamar masu rada da juna tace "me kuke cewa ne wai? Ai kin bai yi ba ko? Na gaya maka ai mijina, aikin nan ba kyau zaiyi ba kazo mu tafi Germany din, a warkar min da kafata shima kunnen ayi min aikinsa acan, anan babu abinda za'a samu sai wahala. Dan Allah Hassan kar ka bari na kurmance" ta karasa tana kuka. Doctor din ya kalle shi yace "baka gaya mata ba?" Ga mamakin ta sai taji taji wannan tas, ta juyo tace "menene za'a gaya min" yace "cewa ba zaki kuma hawa jirgin sama ba ballantana har kije wata kasar. Likitocin dai da suke Nigeria damu zaki yi hakuri ki lallaba har zuwa karshen rayuwarki" ta zaro ido tana kallonsa sannan ta kalli Hassan tace "he is lying" likitan ya dauki takardun sa yace "in baki yarda ba akwai hanyar tabbatar wa, ki tafi airport yanzu ki hau jirgi ki gani. Ina tabbatar miki dan guntun jin da kika fara samu zaki rasa shi gabaki daya".
Daga haka ya fice ya bar su da rigima. Yasan bai kyauta ba yadda yayi breaking news din amma kuma shima haushinta dama yake ji yadda take ta nuna wa cewa basu iya aiki ba da sauransu, wai ita matar mai kudi. Yanzu sai yaga amfanin da kudin nata zaiyi mata.
Washegari suka bar asibitin dan Ruqayyah cewa tayi ba zata iya cigaba da zama ba. Hassan yayo mata order hearing aid din da zata ke amfani dashi, yaso kuma ace gida zasu koma amma taki komawa tace ita sai dai a chanja mata wani asibitin inda wani likitan zai sake duba kafarta tunda tana tsoron daring likitan kunne da yayi warning kar ta kuma shiga jirgi.
Wani private asibitin kashi ta tafi anan Kaduna, doctor din yayi mata alkawarin zai warkar mata da kafarta tana zuwa yayi admitting dinta ya fara karbar kudade yana sakawa a aljihunsa, tana asibitin aka kawo mata hearing aid dinta ta fara amfani dashi kuma alhamdulillah jinta ya dawo tana ji tas amma sai da shi, in ta cire sai dai taji kadan kadan kuma shima sai tayi stressing kunnenta tukunna. Daga baya ta fahimci cewa likitan bashi da clue akan abinda yake damunta dan haka ta nemi sallama kuma ya bata sai ta hada kaya sai Kano, AKTH, tana zuwa nan ma suka hau kanta da gwaje gwaje da hotuna da magunguna amma bayan shafe wata guda cur a cikin asibitin sai suka tabbatar mata da cewa su basu da idea me yake damun kafarta. A guri daya kuma kafar sai kara motsewa take yi kamar ta mai ciwon shan Inna, yanzu har kankancewar tata ya zama ana gani ake ganewa dan kana gani zaka gane daya kafar tafi dayar girma. A karshe sai likitoci suka yi mata cast, tun daga hips dinta har zuwa tafin kafarta dan ya taimaka mata wajen motsa kafar, daga nan suka ce babu abinda zasu kuma iya yi mata.
Ta zama mai kafa daya kamar yadda ta zama kurma.