Sashe 10
Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Inna Ade tace "Baban biyu yau ba zaka fita bane ba? Naga ka dauko radiyo" yace "zan fita, labarai dai nake so inji ko zanji sanarwar sunayen wadanda aka dauka aikin nan da muka je nema jiya" Sumayya tayi dariya tace "Baba jiya fa kuka yi interview din, daga jiya zuwa yau har a sanar da wadanda suka ci?" Yace "ahau, ba aikin kamfani bane ba, ai su basu da bata lokaci sha yanzu ne magani yanzu ba kamar aikin gwamnati ba da za'a yi ta fama kamar cin kwan makauniya. Su kuwa wadannan tunda sunyi mana intabiyu shikenan" yaran duk suka kwashe da dariyar yadda yayi pronouncing interview din, yayi musu dakuwa yace "ku ungo ku raba, ni kuke wa dariya" Ruqayyah tace "Baba interview ake cewa ba intabiyu ba" yace "ko ma inta uku ne ku kuka sani,ni dai abinda na sani shine a bani aiki kawai, kunga inna samu aikin gadin nan sai innar ku take yi min abin siyarwa ina tafiya dashi ina siyar mata a bakin gate" Zunnur yace "baba ni zan taya ka dauka" Baba yace "makarantar kuma fa?" Sumayya tace "Baba ni zan daukar maka tunda kaga mu mun kusa gamawa, kafin ka fara aikin mun gama sai in ke kai maka" yayi murmushi yace "Husaina in dai har ina da rai kuma ina da lafiya ai ba zaki yi talla ba. Har kar neman kudin da zaki yi idan ba sana'a a gidan mijinki ba to sai dai aikin office" Inna Ade tace "allahumma ameen Baban biyu, Allah ya nuna mana wannan rana ya Allah" yace "ameen. Kinga yaron da yayi mana intabiyu din nan, wallahi ya burge ni sosai yaron nan, sai naji ya kwanta min a rai ina kallon sa nace Allah ameen, Allah ka muna min Suleiman dina watarana kamar haka. Dan saurayi dashi fa wai amma shine mai gurin gabaki daya" Suleiman yace "Baba ba H & H ba? Ai yanzu su suke tashen kudi a garin nan, wannan kamfanin da za'a bude na goma kenan fa kuma ance ogan ko aure bai yi ba" Ruqayyah tace "kai Suleiman banda kari, yanzu har sunyi goma?" Sai kuma ta langwabe kai gefe tace "sunji dadin su, wasu mutanen da sa'ar su suke zuwa duniya" Baba yana kallonta yace "Hassana ni banji kin ce zaki tayani daukan kayan abinci mu siyar a bakin gate ba" ta sunkuyar da kanta tana zuba kunu a cup tace "Baba in nace ma cewa zakayi a'a shi yasa ban ce ba" ya dauke kansa yana maida hankalinsa kan tuwon da Inna Ade ta ajiye masa a gabansa yace "insha Allahu ina samun aikin nan zan fara tara kudin da zan biya muku kudin jami'a. Insha Allahu ba zan kasa biya muku ba kamar yadda na kasa biya muku kudin wannan jarabawar".
Kasa kasa Ruqayyah tace "hmmm. Allah yasa. Necon ma dam gwamnati ce take biya da cewa za'a yi ita ma mu hakura babu kudi" Inna Ade tace "me kike cewa ne Ruqayyah?" Ta dago kai tace "cewa nayi Allah yasa, Allah yayi jagora" duk suka amsa da ameen.
A bangaren su Aunty kuwa da safe, Aunty ta sauko daga samanta idanun ta akan dining table tana lura da cewa ba'a taba abincin gurin ba, tasan kuma Hassan kullum shine na farkon tashi a gidan dan kusan kullum akan dining take samunsa. Ta karaso tana bude warmers din taga babu alamar an taba abincin. Ta ja kujera tana kwalla wa Safiyyah kira amma maimakon taji ta amsa daga san su sai taji ta tana amsawa daga bakin kofa, da alama daga waje take, Aunty tabi fuskarta da kallo har tazo ta zauna a kusa da ita tace "wai har yanzu baki samu number din Hassan ba?" Safiyyah ta ce "ban samu ba Aunty. Da daddare wayar tana shiga amma yanzu da safe a kashe take" Aunty tace "je ki duba mim dakinsa, tashi da sauri" Safiyyah bata motsa ba fuskarta kamar zata yi kuka tace "daga can nake aunty. Yaya Hassan bai kwana a gidan nan ba, motar daya fita da ita ma bata nan. Tun daya fita kafin magriba mai gadi yace bai dawo ba".
Aunty tayi shiru tana kallon gefe daya, sannan kuma sai tayi saurin dauko wayarta tana kiran Hassan, switch off taji, ta katse kiran ta ajiye wayar tana jin yunwar data sauko da ita tana guduwa tana barinta. "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun" ta ringa fada tana maimaita wa "ina yaron nan ya tafi? A ina ya kwana?" Tunda take da Hassan bai taba kwana ba'a gida basao lokacin da yana makaranta kuma shima dan a hostel ya zauna. Ta juya tana kallon Safiyyah wadda idanunta suka cicciko da kwalla tace mata "maza ki kirawo min Jabir" Jabir shine babban abokin Hassan wanda kuma za'a iya cewa shine kadai abokin sa bayan Hussain, shine kuma saurayin Safiyyah.
Ta dauko wayarta ta nemo number din Jabir da kyar saboda hawayen da ya lullube mata idanunta ya rage mata gani. Ta kira ta saka a handsfree, yana dauka tace "yaya Jabir ina kwana? Aunty ce take tambayar ko kuna tare da yaya Hassan, bai kwana gida ba" shirun da Jabir din yayi shi ya tabbatar musu da amsar sa, basa tare, Safiyyah ta fara kuka sosai, Aunty ta karbi wayar daga hannunta tace "Jabir ba kwa tare ko?" Ya danyi gyaran murya yana kokarin boye tashin hankalin sa yace "bama tare Aunty, tun jiya da safe dana raka shi yayi interviewing kananan ma'aikatan kamfanin su ban kuma ganin sa ba, na kira wayarsa dai da daddare bai dauka ba sai nayi tunanin ko har yayi bacci lokacin, da wacce motar ya fita?" Aunty ta gaya masa sai yace " bara in zo gidan, amma ku kwantar da hankalin ku, bara in kira Khalid, maybe gidan su ya kwana kuma maybe bashi da charge" ya fada cikin kokarin sa na ganin ya kwantar musu da hankali amma tabbas shi nashi hankalin ya kai kololuwar tashi. Aunty tace "Khalid? In kwana yayi a gidan su Khalid din kuma bashi da charge mai yasa ba zai karbi wayar Khalid din ya kira mu ya gaya mana ba? Wannan ba halin Hassan ba ne ba. Hassan zaiyi tunanin cewa ya kamata ya kira ya fada. In Hussain ne ba zan damu ba" ta danyi shiru sannan ta dora da tambayar "waye ma Khalid din?"
Jabir yayi saurin kashe wayar,shima baisan wani Khalid ba kawai sunan ne ya fado masa kuma yana son kwantar mata da hankali ko da ta hanyar karya ne. Ya zauna a bakin gado yana dafe kai. Tabbas babu lafiya, Hassan ba zai taba tafiya wani gurin ya kwana ba sannan ya kwashe wayarsa. Ko wanka baiyi ba ya fita, duk inda yasan suna zuwa da Hassan ko wanda yasan suna harka da Hassan sai da ya nema amma babu wanda ya gan shi. A karshe dai ta tafi police station ya sanar wa yan sanda ya kuma basu description din Hassan da kuma motar da ya fita da ita. Anan ya bata lokaci da yawa, saboda police suna fahimtar waye Hassan din suka daukaki maganar kuma abinda suka fara kawowa shine kidnapping. Sai wajen azahar sannan yaje gidan Aunty ya same ta ita da yara sunyi kuka har gode Allah. Ya yi musu bayanin duk abinda yayi sannan yace "ku kwantar da hankalin ku dan Allah. Police sun riga sun shiga maganar nan kuma sun bazu gurin nemansa a lunguna da saƙunan jahar nan, an bada cigiya gidajen rediyo da talabijin duk an baza hotunan sa. An aika asibitoci suma da mortuary duk za'a duba" Zulaihat ta saka kuka tace "mortuary kuma Yaya Jabir?" Ya dafe kansa yace "baya can Zulaihat, dubawa kawai za'a yi amma baya can" tace "to in baya can me yasa za'a neme shi a can?"
Yayi kokarin kawar da maganar ta hanyar tambayar "ina Hussain. Aunty ta dago kai daga kallon charbin hannunta tace "Hussain ya tafi China Jabir. Har yanzu kuma bai kira mu yace mana ya sauka lfy ba, shima bamu san halin da yake ciki ba" ta karasa tana goge hawayen idanunta.
Da yamma a gidan Inna Ade. Inna Ade tana yiwa Ruqayyah kitso Sumayya kuma tana tsefe nata kan. Suleiman da Zunnur suna gefe suna dorawa wasu yara karatu sai ga Baba ya fito daga daki fuskarsa dauke da tashin hankali, hannunsa rike da radiyo. "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Maman biyu kinji wai an sace shi. Yanzu shikenan ya bata sai kace ba mutum ba? Sai kace wata jaka?" Inna Ade ta saki kitson da take yi tana dafe kirji tace "wa aka sace baban biyu? Waye ya bata?" yace "yaron nan da na ce miki na jishi a raina kamar Suleiman, yaron da muka je neman aiki gurin sa, mai sabon kamfanin nan, yan zu ake sanarwa a gidan radiyo wai tun jiya ba'a ganshi ba ana tunanin masu garkuwa da mutane ne suka yi garkuwa dashi".
Gabaki daya suka dauki salati. Inna Ade tace " wannan wacce irin rayuwa ce muke ciki a yanzu? Dan adam ba'a bakin komai yake ba, talaka bai tsira ba mai kudin ma bai tsira ba. Ubangiji Allah ka bayyanar dashi, Allah ka hana azzalumai yin zaluncin su a kansa, Allah ka kare shi ka kare mu baki daya. Allah sarki iyayensa, har naji tausayin su wallahi. Allah ka bayyanar musu dashi in kuma ya mutu Allah ka sa su ga gawarsa" gabaki daya suka ce ameen.
Ruqayyah tace "at least dai ya dana jin dadin rayuwa ko yaya ne, bai zo a bati ya koma a alakoro ba" duk suka juya suna kallonta
A ranar da daddare sai Inna Ade ta samu kanta da saka Hassan a cikin addu'ar ta duk kuwa da cewa bata san shi ba amma tayi masa adduoi sosai da fatan alkhairi duniya da lahira.