Sashe 68
Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A take maganganu suka fara wayo "wannan waye haka?"
"Ai shine mai kamfanin nan na H and H"
"au ba mijin Ruqayyah bane ba dama mai H and H din ba?"
"Aa, wannan ne, mijin Ruqayyah dan uwansa ne"
"kun ga matarsa kuwa?"
"Ai Yar yar sarkin kano ce"
maganganu dai iri iri, a take marokan da Ruqayyah ta saka aka dauko mata hayar su dan suzo su koda ta a gaya wa mutane wanne irin suna akeyi sai suka juya kan Fatima suna yi mata kirari, ita kuma ta bude bakin jaka tayi ta musu barin kudi. Wannan ya saka Ruqayyah ta zare jikinta ta koma daki ta cire gwagwgwaron ta yi kwanciyar ta, sai ga Fatima ta shigo dakin ta tsaya tana kallonta tace "lafiya Ruqayyah kika kwanta ana tsakiyar taron sunan ki?" Ruqayyah ta juyo tana kallon ta tana yamutsa fuska tace "wallahi stitches din nan ne suke min ciwo, sun takura min. Kin san azabar zafi ne dasu. Ko da yake ashe fa ke baki sani ba ko?" Ta juya ta cigaba da kwanciyar ta.
Bayan Fatima ta koma gida tun da ta shiga babu labarin da take yi irin na taron sunan Ruqayyah. "Ruqayyah tayi kyau, twins din nan sunyi kyau sosai, sooo cute. Kamar in sako su a jaka ta in taho dasu in kawo mana su gida" Hussain yayi dariya "kar ki damu, in duka dawo gida zamu ke dauko su suna yi mana wuni anan" ya sunkuyar da kansa yace "kafin mu samu namu muma" sai tayi shiru tana breaking knuckles dinta, ya tsaya yana kallonta dan yasan wata magana take son fada, sai tace "Mi Amour, nace ko zamu fara zuwa asibiti ne?" Ya girgiza kansa da sauri yana rike hannunta yace "ko wata goma fa ba'a yi ba da bikin mu, let's not be inpatient please, mu jira ikon ubangiji kinji Princess. Our time will surely come kinji?" Ta gyada kai a hankali, ya jawo ta jikinta yace "nima ina so Fatima, ina son naga jinina a duniya ko ba biyu ba ko daya, ko mace ko namiji, ina so nima. But nasan cewa what ever will be will be".
Ta kwantar da kanta a kirjinsa tana sauraron bugun zuciyarsa, sun jima a haka sai wayar sa ta fara ruri ya dauko ta ya daga kiran ya saka a kunne. "Manya manya maganin kanana kanana. Ya akayi? Ya garin? Nayi fushi ai in dai har ka kuma barin kasar nan ba ka zo kaga gidana ba to nasan matsayi na" ya danyi shiru sannan yace "ai na gaya maka tun ranar nan da muka yi Magana, in har baka gwada ba babu ta yadda zaka yi ka tabbatar cewa zasu baka auren yarinyar nan ko kuma ba zasu baka ba? Fargaba fa asarar namiji ce" yayi dariya "ka sami takawan kawai ka gaya masa halin da ake ciki, shi zai tura a nemar maka auren ta" "oh haka yace? To shawara ta rage naka kuma, amma ni dai personally bana giving up without trying, ka shirya kaje Riyad din da kanka ka nemi auren yarinyar nan in an baka you come and thank me in ba'a baka ba kuma to kar kace ni na baka shawara" yayi dariya, "gata nan a kirjina. Kai dai tsaya wasa sai da kaga munayi" ya cire wayar daga kunnensa yana dariya, ya juya yana kallon Fatima "mutumin ki dai ya kusa zuwa karshen katanga. Babansa ya ki zuwa nema masa auren balarabiyar nan" ta gyara kwanciyar ta a kirjinsa tace "shine kai kuma kake zuga shi ya tafi shi kadai ko? Ba zasu bashi ita ba ko me zaiyi. Am sure" yayi ajjiyar zuciya yace "I know. But there is no harm in trying, right?"
A daddafe Ruqayyah tayi sati uku a gidan su, sai kawai ta shirya plan ta gaya wa Inna Ade cewa Hassan yace ta shirya zai zo ya dauke ta su koma gida, sai kuma ta gaya wa Hassan tace Baba yace yazo ya dauke ta su tafi. Shi bai san me ta shirya ba yayi ta murna ya gaya wa Aunty, ita kuma ta saka aka gyarawa Ruqayyah part dinta duk dan ta faranta mata. Ita kuma Ruqayyah ta dawo da niyyar in Fatima ta taba mata ya'ya ta gurza mata amma sai ta tarar Fatiman ma bata kasar gaba ki daya. Wannan ya kona mata rai, ita gani take yi wannan tafiye tafiyen kamar dan a kona mata rai ake yin su. Farkon dawowarta tare da Sumayya suka dawo, Sumayyan ce kuma tayi mata register da online catering classes da yawa inda take koyon girke girke da sauran kitchen tips kuma suna gwadawa tare a kitchen dinta, sannan suka koyi yadda ake amfani da kitchen appliances din da suke kitchen din nata. Anan ne Sumayya ta gwada tambayar ta ko tana da niyyar komawa karatu? Tayi dariya Tace "karatu kuma? Ni dama tun farko ai kin san ina karatu ne saboda in yi kudi, yanzu already ina da kudin da ko aikin nake yi ba lallai in samu albashin da zai bani wannan rayuwar ba so why should I bother myself?" Sumayya tace "shi karatu fa ai ba dan ayi aiki ko dan ayi kudi ake yinsa ba ko? Nima da nake karatun ba lallai ne inyi aiki ba musamman in na samu mijin da baya son matarsa tayi aiki ai kinga dole in hakura ko ? Tunda dai ai auren yafi aikin" Ruqayyah tace "say what you may, ni dai ba wata school da zan koma".
A haka rayuwa ta cigaba da tafiya, bakar zuciyar Ruqayyah tana nan a kirjinta amma har yanzu dafinta bai bayyana ga Hassan ba. A haka akayi bikin Minal da alhajin ta lokacin su Yusuf suna da watanni uku a duniya. Ruqayyah tana tsananin son yayanta a zuciyarta amma being the Ruqayyah that she is, bata iya nuna soyayya ba dan haka sai ya zamanto yaran sunfi sabawa da Abban su, sai uncle dinsu wanda in dai yana gari to kullum suna tare har ya iya hada musu madara yayi feeding dinsu. Daga nan sai Aunty wadda dama daga sun dami Ruqayyah zata hada su da mai renon su su tafi gidan aunty, ita kuma ta dauki wayarta ta cigaba da daukan darasin mallakar miji.
A lokacin bikin Minal ne kuma Minal din da kawayenta suka zo gidan Ruqayyah da niyyar zasuyi bridal shower dinsu anan. Sai dai suk ayi rashin Sa'a suka tarar Hassan yana gida kuma Ruqayyah bata gaya masa za'a yi event din ba. Ya shigo yana kallon su, yana lura da yanayin shigarsu da kuma yadda babu wadda ta gaishe shi a cikin su. Sai ya sunkuya ya dauki yaransa y ahau sama da su, Ruqayyah ta bishi a baya.
Tana shiga dakin sa taga ya ajiye yaran akan gado yana musu wasa suna bangala masa dariya, ta tsaya a bakin kofa tana murmushi, bai kulata ba tace "dama bikin Minal dana gaya maka an fara, shine kawayen mu suka zo zasu dan yanka cake su kuma yi hotunan" ya juyo yana kallonta yace "kawayen ku? I thought you said kawayen Sumayya ne da na Minal? Ina ita Sumayyan take? Ko bata zo ba sai kawayenta?" Ruqayyah ta dauke kai gefe tana juya ido yadda ba zai ganta ba sannan ta karasa shiga dakin, ta dora kanta a bayansa tace "to yanzu menene dan nace musu kawayena? Ina laifin wanda ya kula ka? Ka manta su suka tsaya min da bikin mu?" Ya juyo yana kallonta yace "ina fa zan manta? Har duk rashin kunyar da suka yi min ina sane da kowacce kalma. I thought daga ranar ba zaki kara kula su ba saboda marar tarbiyya ne kadai zai riki wadannan a matsayin kawaye, baki san masu magana sunce 'nuna min abokin ka Ni kuma in gaya maka halayen ka ba?" Ta daga shi tana jin ranta yana fara baci tace "ni banga abin daga hankali a wannan maganar ba, ko ma menene sukayi ko suka ce ai ya wuce ko? Idan da kai wani ne yanzu da ba sai dai inji kace ka dauki nauyin duk abinda za'a yi a gidan ba, ko kuma inga ka fita ka siyo mana duk abubuwan da muke bukata ba? At least haka akeyi a gidajen arziki, at least da Hussain ne da hakan zai yi ba wai ya zauna yana mitar abinda akayi shekara guda data wuce ba"
Wannan littafin na siyarwa ne, idan kin ganshi a wani gurin na sata ne, in kuna son ki sayi halaliyar ki ki neme ni ta wannan number din through WhatsApp 08067081020*Unveiled 2*
Farko daskarewa yayi a zaunen da yake, sai kuma yayi blinking idonsa dan ya tabbatar cewa ba wai mafarki yake yi ba, sai kuma ya saka hannu yana bubbuga kunnuwansa ko sune suke yi masa karya sannan ya juyo yana kallonta, bakinsa da idonsa a bude amma kalma daya ta kasa fita daga bakin nasa, so yake ya tabbatar ita ta fadi wadannan maganganun, har da waigawa yayi dan ya tabbatar su kadai ne a dakin ba wata ce ta shigo ta fada ba, sai dai yana yin daya gani a fuskarta kadai ya isa ya tabbatar masa da cewa ita ta fada din. Rashin gaskiya kiri kiri a rubuce a fuskarta. Ta tosa kanta da sauri tana nin gabaki daya jikinta ya dauki kaikayi, sai kuma ta juya da sauri zata bar dakin. Tana son ta kasance ita kadai tayi bitar abinda tace din ta kuma shirya abinda zata ce ta rufe maganar tata.
Charaf ya rike hannunta,bata juyo ba sai idonta data rufe, ya mike daga kan gadon ya zagayo gabanta sannan ya saka cika hannun nata ya rike fuskar ta da hannayensa biyu. "Hassana?" Ta kwace fuskarta ta na kokarin juya masa baya ya sake rike ta, jikinsa har rawa yake yi "Hassana me kika ce min? Me kike cewa? Wacce magana kike gayamin Hassana? Are You okay?" A ransa ya fara tunanin anya ba aljanu suka taba Precious wife dinsa ba?