← Book details Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 125 OF 134

Sashe 125

Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sumayya ta saka Zulaihat ta nuna mata dakin yara a saman, ta nuna mata sannan ta nuna mata nata. Ta shiga tana kallon tsarin dakin, sam baiyi kama da na Ruqayyah ba, kayan Ruqayyah sunfi tsada amma ita a idonta sai taga nata kayan sunfi kyau kuma sun dace da ita sosai. Ta kwantar da Hussain akan gado ta sannan ta koma da niyyar tahowa da Aminu da Yusuf sai Zulaihat tace mata "a ina kike tunanin zasu kwana? Wannan din ma ba lallai Aunty ta bar miki shi ba. Sai kin gama cin amarci tukunna za'a kawo miki shi" ta fada da sigar tsokana.

Sumayya ta marairaice "dan Allah kinga yayi bacci, kar a tashe shi kansa yayi ciwo ki tafi dasu Aminu kawai, a barshi shi yayi baccin sa anan" Zulaihat tace "ni dai babu ruwana, zan tafi dasu amma in aunty ta lura baya can na san zata aiko a dauke shi" Sumayya tace "ba zata lura ba ma" a haka sukayi sallama Zulaihat ta kama hannun twins suna ta bacin rai su a gurin mommy zasu kwana, suka tafi.

Ta koma sama dakinta ta shiga ta zauna a kan gado ta saka Hussain a gaba tana kallon sa, amma ba wai shi take kalla ba zuciyar ta tana saka mata urin rayuwar da zata yi a gidan nan tare da Ruqayyah a matsayin makociyarta, da kuma rayuwar da zasu yi da Hassan a matsayin miji da mata.

Bata an kara ba taji an bude kodar dakin an shigo, ta dago kai tana kallon Hassan shima daya tsata yana kallon ta, ta sunkuyar da kanta kasa tana shafa kan Hussain daya sauke ajjiyar zuciya ya cigaba da baccin sa, Hassan yace "ina kawayen naki?" Tace "sun tafi. Kai ina abokan ka?" Yace "sun tafi" sai ya karaso ya zauna akan side drawer yana kallon ta, ita kuma bata kalle shi ba sai kirjinta da yake dukan tara tara.

Ya kalli Hussain yace "shi wannan me yake yi anan?" Ta kara jawo Hussain jikinta tace "yayi bacci ne, shine nace a bar min shi ya kwana anan" ya girgiza kai, "ki ce in koma in bude kofar gida kenan, dan na tabbatar Aunty sai ta aiko an dauke shi" Sumayya tace "ba zata lura ba, dan Allah ka barshi ya kwana anan dan Allah" ya bita da kallo, a tsorace take sosai, sai kara kankame Hussain take a jikinta kamar zata tsaga kirjinta ta saka shi a ciki.

Sai ya mike tsaye yana kallonta yace "shikenan, in kwanan nasa anan zai faranta miki" ya danyi faking hamma yace "sai da safe"

Wannan littafin na siyarwa ne idan kika ganshi a wani guri na sata ne, in kina son ki sayi halaliyar ki ki yi min magana ta wannan number din through WhatsApp 08067081020*The Sixth Wave*

Kanta yana kasa tace "Allah ya bamu alkhairi" tana jin sa har ya fita ya rufo mata kofa sannan ta dago kai tare da sauke ajjiyar zuciyar da take ta rikewa. Ta tashi tayi locking kofar sannan ta dawo ta dauki Hussain ta kaishi toilet sannan ta dawo dashi ta kwantar dashi itama tayi shirin kwanciya duk da tasan ba bacci zata iya yi ba, kukan Ruqayyah dazu ya taba ta, ta tina rabon da ta ganta tun ranar da Hassan ya sake ta and she ca only imagine abinda Ruqayyah take ji a zuciyarta yanzu. Duk da tasan ba son Hassan Ruqayyah taje yi da gaske ba amma still dole auren su da Hassan sai ta taba zuciyarta sosai.

Ta kwanta tana tuna Adam, sai kuma ta daina tausayin Ruqayyah dan ita ta jawo komai, idan da Adam yana nan da babu yadda za'a yi Baba ya hana shi ita ya bawa Hassan dan tasan Baba yana son Adam kamar yadda yake son Hassan. Ruqayyah ce tayi sanadiyar rabuwarsu dan haka this will be her price to pay.

Ta dauko wayarta tana going through hotunan su kamar yadda take yi kullum, sai data gama gani sai kuma ta koma farko tayi marking all sannan ta danne delete tana jin zafin abin a ranta amma tasan hakan shine dai dai hakan shine zai kara taimaka mata gurin cire shi daga zuciyarta. Bayan ta gama gode hotunan sai ta koma kan messages dinsa da take ta ajjiyar su suma ta goge su sannan ta shiga contact ta goge number dinsa, tasan ko zai dawo ma he won't be using that same number again.

Sai data gama sannan ta tashi tahe ta dauro alwala tazo ta tayar da sallah, tana gayawa ubangijin ta bukatar ta, and for the first time tun bayan rabuwar su da Ruqayyah sai ta samu kanta da yi mata addu'a tana neman Allah ya shiga lamarin ta ya huce zuciyarta ya daidaita tsakanin su.

Sai da taji bacci yayi mata nauyi har bata iya bude idonta sannan ta kwanta, saboda bata son ta kwanta tayi ta tunani, tana kwanciya kuwa tayi bacci abinta.

Da assuba ta tashi tayi sallah sannan tayi wanka sai ta koma ta cigaba da baccin ta dan sai yanzu gajiyar bikin ta ke sauko mata, duk da dai ba wani dogon biki tayi ba. Motsin Hussain ne ya tashe ta, ta farka ta ganshi ya kafe ta da ido yana ta murna wai yau sun kwana tare, daga nan sai ya saka ta a gaba da zance a dole ta mike duk da baccin ba isarta yayi ba ta ja shi xuwa toilet tayi masa wanka yana tayi mata hira "mommy wai yanzu kim dawo gidan daddyn mu ne? Anan zaki ringa kwana ko? Kin daina kwana a gidan Inna?" Tace "eh" yayi tsalle yana bata toilet din da kumfa "nima na daina kwana a gidan Aunty ko? Tare zamu ke kwana anan da su Aminu ko? To ina suke? Ko a dakin mu suka kwana? Daddy ya kawo mu jibi ya nuna mana dakin mu ya saka mana gado a ciki kowa da nasa yace banda fada. Kinga Daddy shi fada yake yi mana idan munyi fitina, Aunty kuma sai ta bamu sweet tace mu fita backyard muyi ball. Ni ban iya ball ba faduwa nake yi......"

Haka yayi ta zuba kamar fanfon daya lalace ita dai tana tayi masa dariya har ta gama masa wankan tayi masa brush da alwala ya fito ita kuma ta tsaya ta gyara toilet din sannan ta biyo bayansa ta tarar ya jawo drawers din dakin wai yana neman kayansa. Ta goge masa jikinsa sannan ta mayar masa da kayan da ta cire masa saboda bashi da wasu sannan ta saka shi yayi sallah, ya duddungura abarsa duk rabi wasa, ita kuma ta shirya cikin riga da skirt na atamfa da suka karbi jikinta sosai, ta gyara fuskarta dai dai gwargwado sannan ta gyara dakin shima ta dauki Hussain suka fito yana ta yi mata complain din yunwa yake ji "a gidan Aunty ina tashi aunty take bani tea nake sha ba ta yi min wanka sai nasha tea" suka fito tana lakuce masa hanci "ninkuma a gidana sai mutum yayi sallah yayi wanka sannan zai sha tea, in luma mutum bainyi abinda nace ba to zan mayar dashi gidan Aunty" ya kankame ta yana kwabe fuska "ni nafi son gidan nan, nafi son mommy na da Daddy na" ta rike fuskarsa a hannunta tana murmushi tace "nima ina sonka sosai sweetie pie"

Sai taji gyaran muryar Hassan a bayanta, suka juya da sauri, Hussain ya zame daga jikinta ya ruga gurinsa "daddy yau akan gadon mommy na kwana kuma banyi mata fitsarin kwance ba kuma tace a nan gidan zata ke kwana kuma bata bani tea nasha ba sai tayi min wanka" Hassan yayi dariya yana shafa kansa yace "kai, da kai da parrot ban san wanda yafibwani surutu ba. To gaya min gadon mommy da dadi?" Hussain yace "da dadi mana, wankan ta ma da dadi, dama tana yi min wanka in naje gidan Inna shi kuma Baba ya siyo min Mango"

Sumayya tace "Hussain baka gaishe da Daddy ba fa kake masa zance haka" Hussain yace "lah na manta, daddy good morning. Zaka bani tea insha?" Hassan ya dauke shi yace "zan baka, amma sai kayi shiru ka barni mun gaisa da mommyn ka tukunna"

Ya juya yana kallon Sumayya sai taji babu dadi, sai taji Kamar bata kyauta ba data fito babu hijab dan bata jin ta taba tsayawa a gabansa babu hijab. Ta dan rage tsaho ta gaishe shi ya amsa yana studying fuskarta "anya kuwa kinyi bacci sosai? Ko bakunta ce?" Ta danyi murmushi tace "nayi bacci fa" yace "amma ba sosai ba ko?" Tayi shiru, yace "kar ki damu, babu dodo a gidan nan" Hussain daya kwantar da kansa a kafadar Hassan yace "Daddy akwai dodo a gidan aunty, yana nan acikin closet aunty Zulaihat tace duk wanda ya kuma shiga ciki ya buya sai dodon ya kama shi kuma tace yana da manyan hakora da zai cinye mutum dasu kamar haka" ya fada yana kokarin demonstrating a wuyan Hassan, Hassan ya sauke shi yana cewa "a'a kar a fara cinyewa ta kaina a cuci amarya ta" Sumayya ta danyi dariya tace "ban san lokacin da bakin yaron nan ya bude haka ba, maganar sa tafi shekarun sa yawa, biyu da rabi yake yanzu fa" Hassan yace "sai next month ma zai yi two and a half years. Yawo be dashi da surutu da kirinki irin na mai sunan shi. Dama kamar su daya" Sumayya tabi Hussain daua fara tsalle tsallen sa a corridor din da suke tsaye tana tuno late Hussain tace "Allah yasa yayi halinsa" Hassan yace "banda iyayin" tayi dariya, sai ya bi ta da kallo yana jingina da jikin bango, ta hadiye sauran dariyarta tana kokarin kamo hannun Hussain yace "kinyi kyau sosai" Hussain ya juyo yace "yes mommy kinyi kyau, amma na jiki kyau" ta juyo tana kallon Hassan sai ya girgiza kansa yace "too late, har iyayin ya dauko".
Chapter 125 · 0% Book details