← Book details Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 134

Sashe 77

Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Satin ta daya a gida, kullum sai sunyi video call da Hussain sau uku kamar yadda yayi mata alkawari kuma hakan yana debe mata kewa sosai. Sai dai problem dinta daya shine yadda taga kamar yana ramewa, tayi complain sai yace mata ai kewarta ce take damun sa. "To ku dawo mana" ta fada kamar zata yi kuka "bana jin dadi da baka nan, kullum zuciya ta sai in ringa ji kamar wani abin yana faruwa wallahi, ga faduwar gaba, kuma duk dan baka nan ne" yace "ya zanyi in taho in bar Hassan baya bashi da lafiya? Kimga ai ban kyau ta ba ko? Gashi ciwon nasa kamar karuwa yake yi ni duk hankali na a tashe yake, an bamu wasu test da za'a yi da hotuna da za'a tabbatar da me yake damunsa" sai kuma taji babu dadi, kamar ba ta kyauta ba da take cewa Hussain ya bar dan uwansa ya dawo gurinta. Tace "to maybe ma damuwar hakan ce ta saka nake ganin kamar ka rame, ka daina damuwa sosai kaji Mi Amour? Zai samu sauki kaji?" Yace "insha Allah. Amma duk da haka a zamu dade ba nan gaba, in anyi test din zamu taho in results ya fito ma dawo" tace "noo, ku tsaya kawai a bashi kulawa sosai. In abun zai dauki lokaci sai in dauko Ruqayyah muntaho tare kawai, na tabbatar shima zai bukaci matarsa a kusa dashi" Hussain yace "yeah right. Nima kuma ina bukatar matata a kusa dani."

A hankali take lura da yadda nayayin sa yake cigaba da kalacewa, kullum kuma sai tayi masa complain, hakan yasa ana gobe za'a yi masa aikin yace mata wayarsa ta lalace ba zata yi video call ba sai dai suyi voice. Wannan yasa ta sake tabbatarwa da cewa something is definitely wrong, tasan cewa karya yake yi mata amma sai ta kasa karyata shi din. Babu yadda za'ayi Hussain ya zauna da lalatacciyar waya, wayar da bata yi komai bama Hussain yana chanjata zuwa sabuwar yayi ballantana ace wayar da tayi lalacewar da zata hana shi ganin ta? He is definitely hiding something.

Wannan yasa ta tattara ta dauki Khadijah suka koma Kaduna, ta samu Aunty ta zayyana mata abinda suka yi da Hussain ita ma kuma auntyn ta tabbatar da maganar Fatima sai dai sun kasa gane dalilinsa na yin hakan, sai Aunty kawai ta bawa Fatima shawarar su yi ta addua, dan Hussain ba mutum ne mai boye boye ba tunda har ya boye to abu ne mai muhimmanci a gurinsa, ta tabbatar duk abinda yake boyewa in ya dawo a hankali zasu sani.

Sai dai hakan bai sa baccin Fatima ya dawo gare ta ba, sai dai ta dauki shawarar Aunty bata nuna masa ta fahimci yana boye wani abu ba kuma ta dage dayi masa addu'a da fatan alkhairi aduk abinda yake gabansa......

Sai dai sati daya bayan dawowar ta, sai gashi ya kuma kiranta video call, kuma sai taga yana looking much better than ganinsa da tayi na karshe sai dai shadow din da yake kwance a kasan idonsa. Tace "you look so handsome" yai murmushi yana saka hannu tare da kara gyara gashin kansa yana kashe mata ido yace "Hussain ne fa, Hussain will always look handsome" tayi dariya "kai ka fiya son kanka da yawa" sun jima suna hira, yana tabbatar mata da cewa Hassan ya samu sauki sosai kuma nan da kwana biyu zasu dawo gida. A ranar tayi bacci mai dadi sosai.

Sai dai..........
Washegari a morning news ana fadar major headlines na jaridun kasar nan taga katon hoton mijinta ya cika screen din tvn ta, da rubutu a kasa.....

"Hussain Aminu Abdullahi, H and H boss, is suffering from colon cancer and currently receiving treatment in India"

Ta saki kofin tea din hannunta idon ta a cikin na Hussain din da yake murmushin sa da baya rabuwa dashi. Sai news din ya cigaba yana nuno hotunan Hassan dana Hussain, kunnuwan ta basa jin abinda ake cewa, amma daga hotunan ta fahimci a asibiti ne sannan basu sani ba ake daukan su, kuma yanayin hotunan yana nuna Hussain din ne marar lafiyar. Screen din ya tsaya akan hoton Hussain a kwance akan dago, ga naurori a zagaye dashi, ga kuma doctors a tsaye a kansa.

Kwakwalwar ta tayi blacking out, sannan ita ma ta zame ta bi kofin shayin ta zuwa kasa.

Yarinyar ta da abin ya faru a gabanta ce ta saka ihu, sauran jama'ar gidan suka zo tare da Khadijah wadda tun tafiyar Hussain a gurin ta take, ganin halin da take ciki ya saka Khadijah ta kira aunty ta gaya mata sannan tace a samu driver a tafi da ita asibiti, ita Khadijah sam bata ga labaran ba saboda kafin ta futo daga daki an dauke gurin an tafi wani labarin daban.

Adam aka kira cewa ya kawo mota za'a je asibiti, sai dai yanayin da aka tarar dashi shima a rikice yake, dan shima akan idonsa akayi labarin. "Dama oga Hussain bashi da lafiya? Dama tafiyar da suka yi asibiti ya tafi?" A hakan dai ya dauko motar aka saka Fatima, Aunty da Khadijah suka shiga Aunty tana kiran doctor dinsu tana gaya masa gasu nan akan hanya. Sannan dauko robar ruwan data fito dashi a hannunta tana bismillah tana shafawa fatima a fuskarta, tana kuma zuba mata har cikin rigarta. Ta sauke ajjiyar zuciya a hankali tana dan bude idonta ta dora su akan Aunty. Aunty ta fara jera mata sannu, ta juya ta kalli Khadijah tace "ya dawo? Kun kira shi a waya ya taho?" Khadijah tace "waye?" Fatima ta juya tana kallon Aunty tace "Hussain Aunty ashe abinda yake boye mana kenan?" Sai ta rushe da kuka tana tuno fuskarsa a zagaye da doctors. "Na shiga uku ni Fatima Allah ka tashe ni daga wannan mummunan mafarkin. Dan Allah Aunty ki ce min mafarki nake yi Hussain lafiyar sa kalau" Aunty ta rungume ta "Hussain lafiyar sa kalau mafarki kika yi, ban san me kika gani a cikin mafarkin ba amma mafarki kika yi dan Hussain dina lafiyar sa kalau babu abinda ya same shi dan dazu ma munyi waya dasu" ta rike fuskar Aunty "ba mafarki nayi ba aunty a tv na gani. A labarai na gani sunce Hussain bashi da lafiya wai cancer ce take damunsa yana asibiti, har da hotuna suka nuna Aunty, Aunty Hussain dina....." Sai ta rufe fuskarta tana kuka mai ratsa zuciya.

Aunty ta fara girgiza kanta "uhm uhm, karya suke yi, makiyane kawai suke yi masa mugun fata, Hussain lafiyar sa kalau, Hassan ma ya warke sun kusa dawowa, karya ne ki daina bata hawayen ki akan karya Fatima. Bara in kira miki shi ya tabbatar miki da cewa karya suke yi. Ko kuma mafarki kika yi Fatima" a haka suka asibitin, sai da suka yi packing sannan Adam ya kira Khadijah gefe ya gaya mata shima yaga labaran da haka ba wai mafarki Fatima tayi ba, nan take Khadijah itama ta rude dan da duk tunanin ta mafarki Fatima tayi dannita tana bacci ne ma taji hayaniya ta tashi. Nan da nan ta bi Aunty a baya cikin asibitin, ta tarar har karbi Fatima daga hannun Aunty, ta ja ta gefe ido a waje ta gaya mata abinda Adam ya gaya mata. Aunty tana girgiza kanta da sauri ta dauko wayarta ta danna number din Hassan ta India

Yau Hussain tunda yayi sallar asuba ya kuma fita yayi exercise din da likitoci suke saka shi yayi dan taimakawa ciwon sa yayi healing da wuri, sai ya dauko diary dinsa kamar kullum ya fara rubutu.

Dear baby

"Na samu sauki sosai, gobe nake shirin guduwa daga asibitin nan saboda naga basu da niyyar sallama ta ni kuma gida nake son komawa gurin mommyn ka, naga ta fara zama frustrated, bana so tayi fushi da yawa kar tayi min bulala. Kaima kabi ta a hankali dan in mayi mata laifi zata ke zane ka but ba wai dan bata sonka ba sai don tana so ka zama yaron kirki, zata so ka sosai na sani amma kuma nasan ba zata yi maka irin son da take yi min ba. Wait, kar kayi kishi, matsayi na daban naka daban"

Hassan ya shigo yana kallon sa yace "an fara rubutun?" Hussain ya rufe diary din yace "hmmm. Duk abinka dai ba zaka gani ba" Hassan yace "ban yi niyyar in gani din ba dai, san da kake sheka uban baccin ka in nayi niyya ai zan dauka in karanta ne" Hussain yace "sata kenan ai" Hassan yace "ni dai ba zanyi fada da kai ba, ni na daina fada da kai" Hussain yayi murmushi yace "makaho ne aka ce masa ga ido yace baya so, saboda yasan ba zai samu ba. So kake muyi fadan kuma ni ba zan kula ka ba" ya rufe littafin yana saka shi a cikin yar karamar jakar da ya siya musamman saboda littafin. Ya sauko daga kan gadon ya zauna a kujera da ke kusa da table din da aka jera musu breakfast, shi dai duk ba dadin wannan abincin yake ji ba, shi babu abincin da yake jin dadinsa kamar na gimbiyar sa.

Bayan sun gama cin abincin ne aka zo aka bawa Hussain magungunan sa yasha, yana ta mita yana cewa ya kusa daina shan magungunan nan dai ya huta, "ko ku sallame ni ko kar ku sallame ni guduwa zanyi" su dai basu ji abinda yake cewa ba, Hassan yana hararar sa sai ya daga kafada yace "ai nayi kokari" a lokacin ne wayar Hassan tayi kara, ya dauka yaga number din Aunty sai yaji hankalin sa bai kwanta ba dan dazu da ya fita waje ita ya kira kuma duk sun gama maganar da zasuyi, tabbas wani abin ne sabo ya taso. Ya dauki wayar ya fita waje yana magana "Aunty" "Hassan duk abinda kuke yi ku bari ku taho gida, makiyan ku suna nan suna yawo a gidajen radiyo suna yada karyar cewa wai Hussain bashi da lafiya, sun ce wai cancar hanji yake fama da ita, sunce wai abinda ya kaiku India kenan" ta karashe maganar cikin muryar kuka.
Chapter 77 · 0% Book details