← Book details Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 134

Sashe 45

Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yace "amma kunyi magana dasu akan aikina?" Ta daga kai tace "sun tambayeni aikin ka nace ban sani ba, amma sai na basu labarin daukan Baba aiki da kayi a H and H. Ina jin daga nan suka samu kalmar CEA din" yayi dariya yana girgiza kansa yace "CEO ake cewa. It means Chief Executive Officer, wanda shine matsayin da yafi Kowane matsayi girma a Company, shi yake da final say a duk decision making, wani ceo din kuma shine mamallakin Company, shine founder, shine kuma sole share holder" ta dago idanu tana kallonsa tace "and are you?" Ya girgiza kansa yace "noo, am not" taji dan sauran hope din da take dashi yana bin iska. Ta sunkuyar da kanta kasa, Ya sa hannu ya kuma dago da fuskar tata suna kallon juna yace "Hussain shine CEO kuma owner na H and H bani ba. Ni ko share ma bani da ita a cikin Companyn. Duk group of companies din nasa ne shi kadai. Ni maaikaci ne a karkashin sa nake aiki. Matsayina shine chief of staff, duk wani maaikaci na kamfanin a karkashi na yake, ni nake daukan su kuma Ni nake kula dasu. Nima Hussain albashi yake bani kamar yadda yake biyan sauran ma'aikata albashi. Gidajen nan guda biyu duk nasa ne, shi ya gina su, duk motar da kika gani a gidan nan da kuma gidan Aunty to Hussain ne ya siye ta, yana da passion for mota shi yasa yake chanjata kamar yadda yake chanja sutura. Duk abinda kika gani a gidan nan tun daga kan gadon da kika kwana akai zuwa chokalin da zamu ci abinci dashi Hussain ne ya siya" ta sunkuyar da kanta kasa tana fighting kukan da yake taho mata. Dama abinda ta aura kenan? Solobiyon miji wanda zai zauna kaninsa yayi masa komai? Shi me yake yi a lokacin da Hussain yake neman kudin? Ta rabu da Baba ta dawo hannun Hassan. Ita dai bata da Sa'a a rayuwa.

Ya sake dago kanta da hannunsa yana cewa "do you have a problem with that?" Ta girgiza kanta da sauri tace "babu matsala, kayansa ai kamar kayan ka ne. Kuma wata rana Allah zai hore mana namu mu tasar masa daga gida" yace "yes, da banyi niyyar zama anan ba, gida nayi niyyar in gina mana da kudin da nake ta tarawa. But ganin Baba ya fi mu bukatar gidan shi yasa na siya masa sauran kudin kuma nayi amfani dasu a biki, yanzu zan sake tara wasu kafin nan kafin mu tara zuri'a sai muyi ginin mu, shi yasa ban bari Hussain yayi mana gini irin nasa ba, saboda ba lallai bane mu gina irin nasa, kuma bana so in mun zo tashi muga kamar munci baya ne gwara muji cewa munci gaba. Kin fahimta?"

Ta juya tana kallon side din gidan Hussain, ta nuna da hannu tace " you mean....... Irin wancan zai gina mana......sai ka hana shi kasa ya gina irin wannan........?" Yayi murmushi ganin irin tarin mamakin da yake kwance a fuskarta yace "eh mana. Har fushi yayi ya kaini kara gurin aunty" wasu hawayen takaici masu zafi suka zubo mata, wannan wanne irin rashin rabo ne da Hassan? Ya saka dan yatsa ya gogi hawayen yace "kuka? Kukan me kike yi kuma?" Sauran kukan ya kwace mata gaba daya, tace "kukan godiya nake yi ga Allah, wanda ya bani miji mai gudun duniya da hangen nesa kamar ka" ya zauna sosai yana kwanto da ita jikinsa yace "it is okay. Ki bar kuka, you have cried a lot a cikin kwanakin nan. Murna zamuyi muyi godiya ga Allah kinji" ta gyada kai tana tashi daga jikinsa. Ya mike yana mikar da ita itama. "Ki tashi muje to muyi sallah mu gode masa, in mun gode masa sai ya karo mana. Haka yace da kansa" ta mike tana goge idonta da bayan hannunta.

Sai da ya kai ta har dakin ta sannan ya fita, har yanzu bai debo kayansa daga tsohon dakin sa ba, yan kayan da zai bukata kawai ya dauko ya dawo gidan. Ya kai kayan dakinsa sannan ya koma dakinta ya tarar tana toilet har yanzu. Ya koma dakin sa ya shiga wanka shima.

Sai da ta yi kuka mai isarta a toilet sannan tayi wanka tayi alwala ta fito ta saka doguwar riga tayi sallar ishai da bata yi ba. Tana tashi yana shigowa da basket a hannunsa ya ajiye akan side table yace "kar dai har kinyi sallah kin barni" tace "sallar ishai nayi ai" yace "ohhh okay" sannan yazo ya shiga gabanta suka gabatar d sallar sunna da annabi ya umarci ma'aurata suyi. Bayan sun idar Hassan ya yi musu adduoin neman albarka a auren su, neman samun dacewa a duniya da kuma a lahira.

Suka shafa ya juyo yana kallonta ya dan hade rai yace "idonki, kamar ya kumbura, duk kukan ne?" Ta sunkuyar da kai tace "da rashin bacci ma, kasan in mutum yazo bakon guri baya iya yin bacci" yana murmushi yace "kar ki damu, yau zakiyi bacci har da munshari" ta mike tana jin wani iri a jikinta, sai yanzu take tunanin yama akayi ta yadda tayi aure yanzu ne? Ita yar karamar ta ina zata kai wannan mutumin? So take tayi tunanin ta yadda zata zille masa amma kwakwalwar ta ta toshe ta kasa aikin tunanin yadda zata yi dashi dan ita sam yau bakar rana take gani kar yazo ya kara wa ranar ta duhu dan bakikkirin take ganin sa.

Ta mike tana kokarin shiga closet taji hannunsa ya rufe kofar sannan ya murda key, ta juyo da sauri sai gata a kirjinsa, ya saka hannunsa a dayan side din ta yadda ta kasance a tsakiyar hannayensa. Ta fara yayyarfe hannu sauran kukan da bata karasa dazu ba yana dawowa. Yayi dariya yace "cry cry baby, tunda kin zama baby let me treat you as a baby" ba tare daya jira amsarta ba ya daga ta chalak kamar baby, ya zauna akan gado yana dora ta a cinyarsa, ya lura da yadda jikinta yake rawa kadan kadan, ta boye fuskarta a jikinsa. Yace "bafa wani abu zanyi miki ba, look at me, look at me precious" ta dan dago kai tana kallon serious face dinsa yace "nace ba wani abu zanyi miki ba, I just want to feed you that's all. Na ga dazu baki ci abinci a gurin dinner ba, am sure da rana ma ba ci kika yi ba" tace "to ka sauke ni, zan ci da kaina" yace "to zan sauke ki, amma sai kin gaya min a fruits me kika fi so?" Tace "ni banason komai, ni bana shan fruits ma" ya dauko ayaba yana barewa yace "in dai kika cinye wannan to zan sauke ki kuma ba zan yi miki komai ba" ya fada yana kaiwa bakin ta, ta girgiza kai sai ya mayar nasa bakin yace "to shikenan, bara in cinye abata amma kuma duk abinda ya biyo baya ke kika siya da kudin ki" tayi saurin dawo da hannunsa baya tana saka ayabar a bakinta tana ci a hankali idonta a cikin nasa har ta gama cinyewa sannan tace "na cinye to" ya dauko cinyar kaza yace "saura wannan" tayi kamar zata yi kuka "ni ayaba kawai kace min ai" yace "ai ba rantsewa nayi ba". A haka sai data ci kazar, shima kuma yaci. Tace "to na koshi, ka sake ni to" yana murmushi yace "ai ba rantse wa nayi ba" sannan ya juyo da fuskarta zuwa gare shi, ta rufe idonta, ya dora bakin sa akan nata.

A part din Hussain, a cikin Bedroom dinsa. Fatima tsaye a gaban mirror tana cire ear rings dinta. Hussain yana zaune a kujera yana amsa waya yana ta dariya, tana kallonsa ta mirror fuskarsa tana reflecting farin cikin da yake zuciyarsa. Tayi murmushi itama tana jin zuciyarta wasai. Bata da wani tension bata da pressure din komai sai farin ciki da annashuwar cikar burinta na zama matar Hussain. Rabin ranta. Ya ajiye wayar yana cewa "Time to switch off the phone, duk wanda bai kira ba yayi missing, duk kuma wanda bai zo ba shina yayi missing" ya karaso bayan Fatima ya tsaya yana tayata cire sarkar wuyanta yace "duk wanda bai ga kyalliyar Fatima ta yau ba yayi missing" tayi murmushi tana juyowa suna facing juna sannan ta mika masa hannunta yana cire mata awarwarayen ta tace "wanne mai missing din ne ya kira ka? Nasan duk wanda ya bar gidan nan yanzu ba zai kira ka ba" ya kamo yatsunta yana cire zobuna guda biyu da suke yatsun yana ajiye su a gefe yace "Sadiq ne, dan banza, bayan yaki zuwa bikin kuma shine zai kira ni yana min dadin baki" tayi murmushi tace "the prince of Abuja kenan. Shalelen Sarki Abdallah. Ina zai iya tahowa daga america ya bar his Arabian girlfriend?" Hussain yayi dariya yace "sai na gaya masa kina tsokanar sa" ta durkusa tana cire masa socks din kafarsa, sai ya kamota ya dago da ita yana kallon fuskarta yace "kinsan me yace min" ta girgiza kanta idonta a kasa, ya jawo ta zuwa jikin sa sannan ya kai bakinsa dai dai kunnen ta yace "yace wai insha strawberries before I kiss you, so that I will taste like a strawberry to you" ta danyi dariya tana sunne fuskarta a kirjinsa. Yace "kinsan amsar dana bashi?" Ta girgiza kanta ba tare data kalle shi ba, ya saka hannu ya dago fuskarta amma sai ta rufe idonta sai dai ta kasa daina murmushin da take yi, yace "nace masa ba zan sha din ba, cos when I kiss you, I want you to taste me, to taste Hussain not strawberry".

Nasan ba yawa, ayi hakuri

Hassan ya danyi dariya yace "CEO na H and H? A ina kika samu wannan tatsuniyar?"
Chapter 45 · 0% Book details