← Book details Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 134

Sashe 30

Tagwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sama sama Hassan yaje hira da kannen Ruqayyah, lokaci zuwa lokaci kuma yana juyo wa ya kalle ta yayi mata murmushi itama ta mayar masa, shi shirun ta da nutsuwarta suna burge shi sosai, wannan yana nuna cewa bata da hayaniya kamar yadda yake so sannan kuma bata da mita.

A kofar gidan ya tsaya, duk suka juya suna kallon gidan with different thought a zuciyoyin su.
Ruqayyah "wait! What? Ba dai nanne gidan da zamu zauna din ba"
Sumayya "kai!!!, Ji wani gida mai kyau"
Sulaiman "duk sanda na tashi yin gidana irin wannan kofar zan saka"
Zunnur "me muke yi anan?"

Hassan ya bude motar yana cewa "okay, we are here, kowa ya fito" suka fara fitowa daya bayan daya duk idon su akan gidan, Ruqayyah trying so hard not to scream. Ya dauko key ya bude gidan fuskarsa cike da farin ciki yace "ku shigo, kowa ya zagaya ya gaya min view dinsa akan gidan nan".

Ruqayyah a tsakar gida ta tsaya tana jin kamar kafafuwanta ba zasu iya kaita double door din da taga sun shiga ba, sai da Sumayya ta dawo da sauri ta ja hannun ta. "Zo ki gani, Ruqayyah, har furnitures an saka" Ruqayyah bata ce komai ba ta dai bita a baya kirjinta yana bugawa.

Ɗakunan guda uku duk an saka musu set din gado masu kyau da labulaye, falon ma an saka set din kujeru irin wadanda ita kanta Ruqayyah ta san cewa bata taba hawa irin wannan kujerar ba amma duk da haka ji tayi sam basu yi mata ba, sam basu dace da ceo na H and H ba. Ga set din kayan kallo, plasma tv ce amma Ruqayyah a idonta sai taga it is not big enough, ita katuwa ta ke so.

Hassan sai murmushi yake yi yadda yaga yaran suna zagaya gidan cikin murna, ko bai tambaya ba yasan cewa gidan yayi musu. Yaga Ruqayyah a tsaye a falo tana daddanna wayarta sai ya saka hannu ya karbe wayar yana cewa "I am here, ba sai kin kalli hotuna na ba" ta dan yi murmushi tace "to ai baka tsaya na kalle ka ba, kana ta zagaye" yace "ke ma ba sai ki zo muyi zagayen ba?"

Tace "bana jin dadi ne, kafafuwana suke ciwo" taga yanayinsa ya chanja, ya durkusa a gabanta yana kallon kafafuwanta da suke sanye da takalmi tace "subhanallah. Wacce ce daga ciki take yin ciwon?" ta kara jan skirt dinta kasa tana kuma rufe kafafuwanta tace "ba nan bane ai yake ciwon" ya dago kai yana kallon ta yace "ina ne yake ciwon?" Ta juya masa baya tana jin zuciyarta tana zafi, kamar zata yi kuka take ji.

A lokacin ne su Sumayya suka fito daga dakin da suka shiga na karshe, suka dawo palo, Zunnur yace "kai! Wannan tv da girma take, zata yi dadin kallon ball" Hassan yayi dariya yace "you like it?" Duk suka amsa da yes banda Ruqayyah data juya musu baya tana kokarin rike hawayen ta. Sumayya tace masa "nan ne gidan ka? Anan zaku zauna da Rukee?" Yace "yaya Ruqayyah, yaya Ruqayyah zaki ke ce mata ba Rukee ba, and no, ba gida na bane ba kuma ba anan zamu zauna ba" Ruqayyah ta juyo tana jin kamar an yaye mata wani abu a kirjinta. Yace " wannan sabon gidan ku ne dana siya muku , nan nake so ku dawo tare da Baba da Inna ku cigaba da rayuwar ku anan".

Yaran suka dauki sowa gaba ki daya, Ruqayyah ma ta rufe bakinta tana dariya, wannan ce dariya ta farko data yi tunda suka shigo gidan, Hassan yace da samarin "ga naku dakin can a soro, akwai tvn ku a ciki da zaku yi ta kallon ku a ciki. Ku zo muje in nuna muku" suka bishi a baya da sauri suna hada hanya.

Sai a lokacin Sumayya ta zagaya da Ruqayyah ta ga gidan, sai a lokacin taga kayan sunyi mata kyau amma da duk dusu dusu ta gan su. Sai a lokacin ta lura da cewa toilets din modern ne. Suka fito suka yi joining sauran a dakin soro inda aka yi masa tsarin samari da toilet dinsu. Sai da suka gama sannan suka fito, ya rufe gidan suka shiga mota suka juya suna barin gurin. Ruqayyah ta juya tana kallon gidan, sai taga baiyi mata kama da gidan su matar mamallakin H and H ba.

A hanya ne yake ce musu. "Ya kuka ga gidan? Yayi muku? Suka yi dariya, Sumayya tace "yayi mana, sosai ma kuwa. Mungode mungode Allah ya saka muka da alkhairi Allah ya biya ka da aljanna" yace "ameen na gode nima da addu'a. Yanzu abu daya nake nema daga gurinku shine ku taimaka ku lallaba min Baba ya yarda ya karbi gidan nan. Ku hada kanku ku nuna masa kuna so ya karba. Kunji"

Duk suka amince, ya juya yana kallon Ruqayyah da take ta zabga murmushi yace a hankali "do you like it" tace "sooo much. Yayi kyau sosai. Mungode Allah ya saka da alkhairi" yace "bana hana ki yi min godiya ba? Duk abinda nake dashi naki ne, to menene in mutum yayi amfani da abinsa?" Taji wani irin dadi a ranta, duk abinsa nata ne, tabbas bata da sauran wata damuwa a duniya.

Bayan ya ajiye su ne yace musu, "bayan gida kuma, akwai Napep da Hussain ya bashi shima saboda transport da kuma ko zai kezagayawa dashi, na san Baba baya son zaman banza" ya karasa maganar yana fadada murmushin sa. Sumayya ta taya shi murmushin "lallai kasan Baba. Ai kuwa Hussain ya kyauta sosai ayiwa Baba Godiya"

Sama sama Ruqayyah take jinsu. Tunda kalmar Napep ta shiga kunnuwan ta taji kunnen ya toshe. what? Baban nata ne zaike yin hayar Napep bayan ya taso daga aikin gadi? Ta juya ba tare da tace da kowa komai ba ta shige gida. Hassan yana sallama da yaran vai lura da shigar ta ba sai daya waigo yaga bata nan. Ya ji babu dadi, ya so su dan taba hira kadan amma kuma sai ya bata uzuri da maybe ta gaji ne, gashi kuma dama tace kafarta tana ciwo.
.
Ruqayyah tana shiga gida ta fara masifa "Napep fa yace, wannan wanne irin cin mutunci ne da cin fuska. Me nayi wa Hassan da zai ke wulakanta ni irin haka? Wannan ce sakayyar da zai yi wa taimakon da nayi masa?" Sumayya data biyo bayan ta tace " ke baiwar Allah! Yanzu menene laifin Napep din? Menene laifin wanda yaso mahaifin ki da arziki?" Tace "arziki? Ina arzikin yake? Napep din ne arziki? Mutumin da na tseratar da rayuwar sa shine zai jefi ubana da keke Napep? Ji nake a sanadiya ta ne ya samu ransa, kuma ya samu dukiyar sa daga hannun wadanda suka sace shi. Ji nake naira billion daya aka xe an karba daga hannun barayin kuma an bashi kayarsa? Me ya bani a ciki? Me ya taba bani? Sim card din?"

Sumayya tace "wannan ra'ayin sa ne ya baki ko ya hana ki, ganin damarsa ce. Amma ya kamata ace abinda kika samu daga gare shi ki gode Allah. Yaushe rabon da kinkwana da yunwa? Yaushe rabon da kici mai da yaji? Ji nake duk a dalilin haduwarki dashi ne? Yanzu kayan da suke jikinki ta dalilin wa kika samu. Ina laifi? Ina laifin wanda ya bawa mahaifinki aiki ya daina leburanci da turin baro? Ina laifin wanda ya bawa mahaifinki Napep yace yayi sana'a dashi? Gidan daya siya mana kuma fa? Mai tilesda ac da ban dakin water system? Shima duk bai kyauta ba?"

Ruqayyah tace "wannan kuturun gidan kike magana akai? Ai wannan gidan is nothing in aka duba irin dukiyar sa, wannan gidan ai bai kai gidan da a za'a nuna ace ga gidan surukan mutumin daya mallaki kamfanoni ba. Ban taba lissafin cewa zan auri mai kudi ba sai da na hadu dashi, ban kuma san cewa marowacin mai kudi zan aura ba sai yau. Wallahi yayi da yar halak, ba dai za'a yi bikin ba? Ba dai zan shiga gidan sa a matsayin matarsa ba, wallahi sai na chanza masa takunsa tunda dai ace duk motocin da yake ta shiga yana fita dasu ya rasa wadda zai bawa mahaifina sai ya bashi Napep. Wallahi har wannan gidan sai ya chanza in dai yana son zaman lafiya"

Ta wuce Sumayya kamar kububuwa. Duk maganganun su Inna Ade tana tsaye akan baranda tana jinsu. Sai da Ruqayyah ta zo zata wuce ta sannan tace "zo nan Hassana" ta dakata da tafiyar da take yi amma bata juyo ba ballantana Inna Ade ta saka ran amsawa. Inna Ade tace "yanzu rashin godiyar Allahn naki har ya kai haka Ruqayyah?" Ruqayyah tayi magana kasa kasa sannan ta juya zata shige daki. Inna ta saka hannun ta na hagu ta finciko ta baya sannan ta saka na dama ta wanke ta da mari tace "watakila wannan ya dawo dake cikin hayyacin ki".

Hussain yana ta shirye shiryen sa. Gida ya kammala, an gama finishing touches da komai. Takanas aka yo masa yawa daga masarautar kano akan cewa kar ya saka wa Fatima komai a dakunan ta. Bai so haka ba, amma sai ya bar musu ya fara zuba kaya a nasa dakunan, the best of the latest of komai yake sakawa. Hassan ya fada tuntuni cewa shi zai yiwa da Ruqayyah kayan daki. Amma kuma Hussain ya ga shiru, kullum in yayi masa magana ko kuma yayi masa tayin wani design na kaya sai yace ai zaiyi ne "tunda nace maka zanyi ka bar ni mana, ina ta planning irin wadanda zan saka da wanda zan saka mata, ba lallai ta so irin naka ba kasan taste dinta ba irin na gimbiya bane ba" Hussain yace "ka tambaye ta ne kaji wanne taste ne da ita? Ko kuma dan sunan ta Hassana sai ya zamanto tana da ra'ayi irin na Hassan?"
Chapter 30 · 0% Book details