Sashe 8
Nida Kishiyoyina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
masu mutunci Kuma wlh daga yau Kar na sake na sake ganin ta a gidanan tunda tace ban isa na rabaku ba sai nagani ta tsaya a matsayinta na bazawara ta nemo zawara Yan uwanta ta cigaba da hulda dasu tana aron kayansu" "Salisu yau ni kake wa cin mutunci sabida nazo gidanka"? "Anyi miki cin mutunci idan kin zuciya ki rabu da Aisha Kar na sake ganin kafarki a gidanan dan tunda har ta fara d'aukar kayanta masu tsada tana baki nasan zata iya Jin maganarki ki mata hudubar tsiya" "Salis dan Allah ka bari haka da kakeyi bai dace ba daga aron kayana bai dace ka mata irin wanan cin mutuncin ba haba salis ka manta wacce Luba ne"? "Wacce ita wato dan Kinga ban tuje kayan daga jikinta ba ko wlh kafin na fita waje na dawo ta tabbata ta cire kayan nan ta Kuma bar gidanan idan Kuma kin zabe ta a kaina sai ki bita ku tafi amma matsawar a karkashina kike wlh sai kin rabu da ita" Ya juya fuuu y ayi waje. Luba ta bishi da ido hawaye na gudu a fuskarta na Mik'e tsaye Ina k'ok'arin Magana ta daga min hannu ta Shiga d'akin yarana na bita Ina bata hakuri. Ta fashe da kuka tare da zuge zip din rigar ta cire rigar ta cire sarka da dan kunnen duk abinda take kuka take sosai nima na fara kukan Ina cigaba da bata hakuri wlh a rayuwata bana san wulakanci Salis ya wulakanta Luba bai kyauta ba tana gama cirewa ta d'auko zanin wanka dake rataye a kan k'ofar bandaki ta daura duk abinan bata cemin komai ba ta d'auko hijabin dake kan gado tayi hanyar waje tana cigaba da shesheka "Dan Allah Luba kiyi hakuri dan girman Allah wlh ban taba tunanin Salis zai iya min haka ba wlh ko da Wasa ban tab'a fada masa kina aron kayana ba" Ta juyo da jajjayen idonta ta fara nuna kanta "har ni Salis zai yiwa irin wanan cin mutuncin dan na ari kayanki duk a tunanina yanda na d'auke ki haka Kika d'aukeni wlh ban daukeki kawa ba tamkar Yar uwata nake jinki a raina yau akan abun duniya salis ya murza idonsa yamin cin mutuncin nan ba komai Aisha insha Allahu bazai Kara ganin kafata a gidansa ba wlh ba'ayi namijin daya Isa ya rabani dake ba amma tunda shi ya rabamu shikenan idan naje gida Zan aiko miki sauran kayanki da wanan hijabin nagode" Tayi waje da sauri tana toshe bakinta. Na zube a kasa ma fashe da kuka a lokacin wlh har wani daci nake ji a bakina sabida b'acin rai bansan mai ya hau Kan salis yayi mata irin wanan cin mutunci ba Ina laifi ma ya bari ta tafi inyaso duk sai yamin gargadin da zaimin amma irin Wanan cin mutunci Kamar Mai jiran kiris. A haka ya shigo d'akin ya Sameni Ina kuka "Kinsan wlh kina bani mamaki Aisha yanzu ke kinyimin adalci kenan na siya miki Kaya Mai tsada ki dauka ki bawa yarinyar da bata San mutuncin kanta ba ta kashe aurenta dan kawai mijinta bashida kudi dan na koreta kike wanan kukan Kamar tare aka haifoki da ita ko idan kun rabu rayuwarki ta tsaya"? "Haba salis wlh baka kyauta ba dan Adam ba'a abin wulakantawa bane har akan abin duniya ka wulakanta Luba haka Haba Salis ka manta irin hidimar da Luba tayi dani a bikina da yan uwanta tsakani da Allah dan ta nemi aron abu a wajena na bata shine zaka mata haka Salis bansan ka da rowa ba wlh baka kyauta ba arzikin nan naga Allah ne ya baka abaya baka dashi sai yanzu dan Allah ya ma niima baka San wasu su mora wlh baka kyauta min ba" Tunda na fara magana kallona kawai yake Koda na gama sai cewa yayi "toh yanzu so kike naje gidansu na bata hakuri na maida mata kayan? "Ni ba haka nace ba wulakanci da ka mata ne banji dadi ba" "Allah ya kyauta" Yace tare da mik'ewa ya bar d'akin. A ranar ban Kara walwala ba dan wlh abinda Salis ya yiwa Luba ya dameni. Gashi ba waya a lokacin ballantana na kirata na sake bata hakuri kwana uku a tsakani da yamma sai ga wani karamin kanin luba ya shigo da niki nikin leda wai inji Luba tace a kawomin. Salis na zaune a palo yace masa ya kawo ya gani bakinsa sake cikin mamaki. Nidai ban motsa ba Salis ya fara fito da duka kayana da Luba ta tab'a ara a wajena Yana ikon Allah "Ai bansan ku biyu nake siyawa Kaya ba Aisha dama kayan duk da nake siya miki Luba kike bawa ni Ina iya k'ok'arina dan naga na faranta miki amma kina bawa kawarki dan baki san zafin kudi ba toh yayi kyau" "Kai mayar mata da kayan kace ba'aso" Yacewa kanin Luba ya kuwa dauka ya juya ya fita nikuwa hawaye ya hau wanke min fuska. A takaice sai da muka tafi sati biyu Salis ya kasa gane kaina daga baya san damuwata nasani tuni ya damu ya hau Kuma rarrashina Yana cemin abinda nayi bai dace ba nace Masa ni a rayuwa bazan iya wulakanci ba bazaa iya tambayata abu nace babu ba wlh ban iya Kuma banaso ya rabani da luba dan banaso taga dan dagasken da na samu niima nida mijina muka wulakanta ta. Ya saki murmushi Yana toh shikenan bazai kara shiga tsakanina da Luba ba amma shi dai Luba alakata da ita bai ga alheri ba. Baa san ransa ba ya kawo ido ya zuba min yamin Allah ya isa idan na sake bata kayan daya siya da kudinsa sai dai na siya da kudina na Bata. Nidai ban damu ba tunda na samu bai datse kawancen mu ba,da kaina na shirya naje gidansu ban sameta ba haka na zauna na jirata ko da ta dawo ta gani sai ta hade rai "ke da mijinki yace ki rabu dani mai Kika zo nema"? "Dan Allah komai ya wuce Luba kiyi hakuri da abunda ya faru shima yace kiyi hakuri" Hmm kawai tace bata Kara cemin komai ba nidai nayita janta da hira tana bani amsa sama sama da nazo tafiya ta rakani na bata kyautar kudi. A yanda na sake dawo da Luba rayuwata kenan. Amma ta daina aron kayana sai dai ta tambayeni kudi na bata a haka cikina ya isa haihuwa na haifi da namiji aka sa Masa Aliyu arziki Kamar karawa Salis ake yi dan dagaske bansani ba ko lokacin banida wasu burika ne Rabin kudina Luba nake bawa burina ta sake samun miji tayi aure, dan Hamza yayi aurensa Salis ya bashi jari ya bud'e shago a lokacin kafin yayi Aure ma Salis ya sakoni gaba akan na tsara Luba ta koma dakinta wlh zai bata jari da kuwa nayiwa luba maganar kamar ta dakeni akan ko a lahira taga Hamza guduwa zatayi. A haka muka fara shirye shiryen komawa sabon gidan da aka kwashi shekara uku ana ginawa wlh a lokacin babu Kamar gidan a unguwarmu gida ne Salis ya narka masa mugun kudi,daidai da kayan cikin gidan duk na waje ne. Duk tsofafin kayana da Suma da kyaunsu haka yace na bada su na kuwa loda a mota aka kaiwa mahaifiyata ba abinda muka dauka a gidan komai sabone. Har Kaya duk sababi ya mana Salis ne ma ya dan hada Walimar tariya nima na danyi gaya Luba kuwa itace Kan gaba tace har mafarkin gidana take sabida haduwarsa kullum maganarta a Ina zata samo miji Mai kudi irin Salis ai ita tama Raina kudin wanan Alhaji da yake santa. A ranar da muka tare da yawa Yan uwa sun zo sun Kuma kwana dan duk Wanda yazo sai yaji kamar bazai tafi ba a ranar itama Luba ta kwana a gidan dayake gidan sama da kasa ne sama ne bangaren Salis kasan kuwa duk nawane ba wanda ya hau sama duk muka baje kolinmu a kasa dan wlh Ina balain san mutane yaran yayana suma duk a gidan suka kwana sai saintyn gidan suke Ina dariya Khadija da muhasim suma Suka ce ba abinda zai Mai dasu gidansu sun samu gida. Wlh banki ma duk Yaya ya barmin su ba amma nasan bazai tab'a barinsu ba yace idan sunyi hutu zasu ringa zuwar min hutu wanan kenan. Shekara daya a tsakani wani mugun iftilai ya fada mana da bazamu taba mantawa ba muhasim aka Kai gida bakinta a karkace wuyanta baya tsayawa Koda aka zo aka gayamin hankalina a balain tashe nayi gidan yayana Ina zuwa naga gidan a cike taf. Koda na ratsa mutane na shiga ciki a kwance na tarar da muhasim a tsakiyar kafet aunty Mami idonta yayi luhu luhu Yaya mustapha kuwa jikinsa rawa kawai yake. Na zube agaban muhasim da bakinta ke dalalan yawu tana binmu da Ido wuyanta shima a karkace. Cikin tashin hankali nace "Yaya Mai ya sameta haka"? "Wlh bamu sani ba daga makarantarsu aka kawo Mana ita akan an ganta a yashe a bakin gate. "Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun" "Mu kaita asibiti mana mai ya sameta haka" Duk hankalinsu bai Kai su kaita asibiti ba sai da na nemo mota muka dunguzuma muka tafi asibiti. Present. Alhaji Salis Tunda ya tafi massallaci bai dawo gidan ba sai da safe har wani zazzabi yaji yana neman rufeshi. Yana shigowa suka hada Ido da luba dake karkada kafa ya d'auke kansa tare da nufar d'akin Aisha Yana Jin Luba tana maganganu kasa kasa ko ta kanta bai bi ba ya tura k'ofar Aisha a hankali sallamar da yayi ta amsa ko dagowa batayi ta kalleshi ba ta maida idonta ta rufe. Ya zauna a gefen gadon ya zuba mata Ido tsawon minti biyar kafin yace "Aisha dan Allah dan annabi ki tashi muyi magana wlh nagaji da irin zaman da muke yi dake Allah fa muna masa laifi ya yafe Mana haba Mana" Sai a lokacin ta bud'e idonta ta tashi zaune tana "Wani abu ne ya faru"? MG'S SKINCARE Dame akafiki yar uwata? Kyan fatar ko iya gyaran fatar? Ina riba g macenda t Maida kanta sauran mata? Shin haryenzu labarinmu kikeji ko kike