Sashe 7
Nida Kishiyoyina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
matan nan naka Salisu kanka daya kuwa ai wahala kawai Yar mutane zata zo ta sha a gidanka ko ka manta suwaye matan naka? Ina laifi ma kace babba ka d'auko zaka aura?ai daga lokacin da ka aikata kuskuren auro kawar matarka ka tusa mata bakin cikin da nasan har ta mutu bazata tab'a mantawa ba Kai ma fa ba zaka tab'a samun farin cikin da kake so ka samu a rayuwar aure ba wlh ba baki nake ma ba hakki ba Wasa bane ba ni nasan Aisha cewa kawai take ya wuce amma ba yafe maka tayi ba" "Hajiya Kun kasa ganewa kaddara yasani auren kawar Aisha Kuma rabon Yara uku ko inaso ko bana so tunda Allah ya kaddara da rabo a tsakanin mu sai na aureta bansan mai yasa Aisha ta kasa ganewa ba wlh bata kaini bakin cikin zama da Luba ba duk tsawon shekarun nan hajiya wlh ban tab'a kaunarta ba zaman hakuri kawai nake Hindatu Kuma kema kinsan kaddarar da ta saka na aureta mahaifinta ya kakab'a min aurenta nidai kawai ki cigaba da tayani da Addu'a ayiwa su kawu magana suje su kai kudin auren da sadaki tunda mahaifin yarinyar yace wata biyu za'a saka" "Tom Allah ya bada sa'a Salisu bani wayata na kira kawun naka" Alhaji Salis ya mik'e ya d'auko mata wayar a gaban mudubin d'akin ya Nemo lambar kawun yayi dailing tare da sakawa a handsfree. Koda Hajiyar ta fadawa kawun tambayarta kawai yayi yaushe za'a je dan Alhaji Salisu Kam ba wanda baya san faranta masa sabida hannunsa a bud'e yake har dangi na kauye yana hidimanta musu. Bai bar gidansu ba sai karfe shidda dan ji yayi ma Yana fargabar zuwa gidan bai san mai zai je kuma ya tarar ba idan a tsarine yau d'akin Aisha ya Kamata ya kwana tunda har yayi wa Luba kwana daya amma dan masifa sai ya karasa mata wanan kwana dayan idan ba haka ba kuwa bai Isa ya runtsa ba. Koda ya isa gida da Bismillah ya doshi bangaren da yake na yaran dan part wajen uku ne a gidan masifar Luba yasa duk suka zaune part daya duk da katone na gaske sai daya part din daya hade da nasu sabida yara. Ta k'ofar tsakar gidan ya shiga part din yaran a Palo ya tarar da su duk a zaune Afrah tana Kan doguwar kujera a zaune,Aliyu na gaban tv sai yaran Luba Faisal fawazz da bintu, sai na Hindatu da sune kusan Yara a gidan Mubarak Ummulkhairi sai Ummi. Duk suna ganinsa Suka yi wajensa da gudu banda manyan. Ya saki murmushi yana shafa kansu tare amsa gaisuwar da suke masa. Sai da ya gama amsa gaisuwar su ya samu waje ya zauna dan bama yaso ya Shiga Bangaren iyayen duk da sun san daga tafiya yake hakan bazai Hana su daga Masa hankali ba. Afrah dake k'ok'arin mik'ewa ya kalla Yana "Ina Nana banganta ba"? "Tana wajen hajiya umma wai zata mata kitso Abba bari na d'auko ma ruwa" "Ki barshi kawai daga gidan hajiya nake lokacin sallah yayi ku je kuyi alwala kuyi sallah ko nima bari nayi alwala naje massallaci" Da sauri mazan duk suka kada kansu suka yi waje da Alhaji Salis. Basu Kuma dawo gidan ba sai da aka iddar da Sallah Isha. Alhaji Salis ji yake kamar Kar ya Shiga gidan. A hankali ya doshi bangaren matan gidan hayaniyar da yake ji ya saka shi tsayawa cak ya fara jan sallati muryar Aisha da yaji yasa mamaki Kama shi dan bai tab'a Jin hayaniyarta dasu ba idan dai zasu kwana suna fada bata shiga harkarsu. Da sauri yayi cikin gidan ya tsaya a bakin k'ofar Yana kallon Aisha dake sanye da hijabi har kasa hannunta rik'e da na Nana da bata fi shekara goma sha uku ba tana ta kuka "duk abinda zakiyi Luba kiyi luba ban hanaki ba amma idan har zaki tab'a Nana wlh bazan d'auka ba ki tab'a kowa daga Kan Ashraf zuwa Kan ummi amma karki sake ki yarda ki Kara tab'a Nana kinji na gaya Miki" "Sai na tab'a ta Aisha sai dai kiyi duk abinda zakiyi tunda ba fin kowa tayi a gidanan ba wacce wata Nana da bazaa aiketa ba daurin gindin da ta samu a wajenki yasa take yiwa mutane rashin kunya kamar yarinya nan tace baza'a aiketa ba,tunda har yaran gida ma ake aikensu wacce wata agola da baza'a aiketa ba wa ta fi a gidanan aikuwa indan har na aiketa bata je ba wlh sai na doketa idan na daketa ki dau mataki ko a zuciya a maida ta inda ta fito" "Luba ba fa wai tsoronki nake ji ba duk tsawon lokacin nan kike abinda kika ga dama Ina kyalleki idan shi Salisu asirice shi kikayi ni ba asirceni kikayi ba wuri na baki sabida kiyi duk abinda kikeso kiyi domin hankalina da naki ba daya bane daga lokacin da na fara biye miki mun zama daya dake amma wlh wlh kinji na rantse idan kika kuskura kika Kara tab'a Nana wlh zan baki mamaki" "Ki bani yanzu idan ke Yar halak ce bari na daketa naga mai zakiyi" Luba tace tayi wajen Nana da sauri "Lubaaa ya isheki haka" Alhaji Salis yace cikin wani irin tsawa daya sa suka juya dukansu suka kalli bakin k'ofa. Alhaji Salis ya nufi wajensu cikin wani iirn b'acin rai kafin ya Isa wajensu Aisha ta masa wani irin kallo ta ja hannun Nana tayi dakinta da ita. Luba kuwa ta hau girgiza tana jiran isowar Alhaji Salis "Yana kuwa isa wajenta ya hau masifa "Luba ke wacce irin mata ce ke? A rayuwarki sam bakya san zaman lafiya kinfi san ayita tashin hankali da ke wanan wane irin balai da masifa ne Luba na gaji fa wlh wlh nagaji bazaki kasheni da raina ba har ace nafi samun kwanciyar hankali a waje akan a gidana Kuma duk gidanan ba mai daga min hankali sai ke a wane dalili"? "Akan me toh za'a ce kar na aiki Nana wacce Nana da har za'a ringa gindaya min sharruda a kanta wa tafi a cikin yaran mu haka kawai dan San zuciya zaa ringa fifita ta sabida ta hada jini da Aisha toh wlh bazata tab'a sabuwa ba nima Zan dauko ilham ta dawo gidanan da zama ehe ai ba fina tayi a gidanan ba" "Alhaji kawo jakarka na kai ma d'aki ai yaci ka Saba da halinta kake wani damuwa da abinda tayi ita idan bata San ciwon kanta ba ai Kai kasani haka kawai daga dawowarka zaa saka ma ciwon kai muje ka watsa ruwa kaci abinci na maka tausa" Hindatu tace tana k'ok'arin karbar jakar hannun Alhaji Salis da idonsa ya Kada yayi ja kansa har wani sara Masa yake Wani irin duka Luba ta kaiwa hannun Hindatu dake k'ok'arin karbe jaka tana "toh katuwar kwartuwa kafin kija shi d'aki dan jarraba yau kwana na ne ba ruwanki dashi kwana daya yayi a dakina yayi tafiya sai ya karashe min kwana dayan zai koma hannun uwar gida duk jarrabarki sai ki hakura sai kwananki ya zagayo" "Kefa kwana ya dama da gado Luba tarbar da ya Kamata ki Masa ne bakiyi ba shiyasa nake San na masa, tunda ke din ba abinda Kika sani sama da masifa da gado" Wani irin Ashar Luba ta dura wa Hindatu Suka fara zage zage. Alhaji Salis ya zube akan dogon kujera tare da dafe kansa Yana sallati. Sosai yake ji kamar ya sa hannu aka yayi ta kurma ihu. Magana yake musu amma Ina idonsu ya rufe Shirin dambe ma suke. A hankali ya mik'e hannunsa dafe da kansa yayi d'akin Aisha Yana tura k'ofar ya sameta a gefen gado a zaune tana ta share hawaye gefenta Kuma Nana ce a zaune a kasa. Shigowarsa yasa ta dago da kanta ta zubawa Salis ido. Salis kuwa yaji kirjinsa ya masa wani irin nauyi da ganin Aisha a cikin irin Wanan halin shekara nawa Aisha na zubar hawaye da duk shi ya jefata a cikin wanan halin. "Aishaaaa" Ka fita Salisu dan Allah ka fita a yanzu bana san magana ka fita dan girman Allah karka Kara min ciwo akan Wanda nakeji a zuciyata" Salis a hankali ya juya ya fita daga d'akin Yana hadiyar yawu sabida ji yayi makoshinsa ya bushe har ya koma palon suna masifa akan kujera yayi kwanciyarsa ya runtse idonsa Yana Hindatu idan ban isa da Luba ba ke na isa dake dan Allah ki rabu da ita" "Shikenan Alhaji ni bansan ma mai ya kaini biyeta ba kayi hakuri" Tayi hanyar dakinta tana zabgawa Luba harara "Alhaji tashi mu tafi daki na hada ma ruwan wanka" "Bazan tashi ba" "Bangane bazaka tashi ba kasan dai yau a dakina kake ko"? "Anan zan kwana bazan Shiga d'aki ba" "Idan kwanan Aisha ko Hindatu ne ai ba a Palo kake kwana ba" "Idan kina da k'arfi Zaki iya daukana ki kaini d'akin" "Banida karfin daukar ka amma kasani nima anan din zan kwana nima dan bazan shiga d'aki a ci amanata ba" Alhaji Salis yaja tsaki dan kansa sosai yaji yana neman rabewa biyu ya gaji da Luba ya gaji ya rasa ya zaiyi da ita Aisha ce tsaye a ransa inama zata barshi da ya kwana a dakinta ya kwana Yana bata hakuri hawayen ta daya gani ba karamin daga masa hankali yayi ba. A takaice a ranar a Palo ya kwana Luba itama ta d'auko bargo ta kwanta a kasa ta dora kafarta a kan kujerar wajen kafarsa wai kar ma bacci ya d'auketa ya tashi yaje d'akin Aisha tunda nan yafi zuwa idan bacci ya d'auketa. Past Aisha "Dan Allah Abban Ashraf ka bari ka rabu da ita taje daki ta ciremin" "Wlh sai ta cire kayan nan ba bata da hankali ba" Ganin dagaske Salis yake yasa na zube agabansa tare da kankame kafarsa na saka kuka Ina magiya Luba kuwa wani irin hucci take da alama da tana da k'arfi sai ta kaiwa Salis duka. Salis kuwa nasan wuyanta na fara kuka nasan na gama dashi bayasan kukana ko kad'an. "Dalla sake min kafa wlh sai ta ciremin kayan nan idan bakyaso ni Ina da wayanda zan bawa