Sashe 11
Nida Kishiyoyina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
wacce yake da ita a abujan shiyasa ya hana ni zuwa Wlh sai naji kirjina yamin nauyi kamar ta kwada min katon dutse a ka ban tab'a zargin mijina ba nasan Salis ko.ina ne zan. Iya Masa shaida. Sai dai me sai naji maganganunta sunyi balain tasiri a raina dan tabbas da yana da gaskiya bazai tab'a hanani zuwa ba tunda a baya shine me cewa zai ringa tafiya dani idan Yara sunyi hutu. A ranar Sam ban runtsa ba sai naji dama nasan wajen da yake da naje. Kwana biyu na matsawa kaina da tunanin na Kuma yarda ya ajiye mace a gidan da yake tunda har ya hanani zuwa. A irin haka muka yi waya da Luba nace dama nasan wajen da yake Abuja wlh da sai dai ya gani Ina Jin maganarta da kamshin gaskiya ta saki dariya tana baki dai yi niyya ba idan har kinaso ki kamashi ki taho zan bincika asibitin da yake aiki bazaa rasa sanin Inda yake zaune ba. Ai sai naji ba mai kaunata kamar luba sai naji dama yamma batayi ba da na shirya a yau na tafi. Sai na barwa washegari karfe takwas na dau hanyar Abuja dan ta turomin address din gidanta. Akan tunda ranar suna akeyi bayan taron zamu nutsu mu nemo gidan Salis. Tafiyar awa biyar dai sai gani a garin Abuja da na Kira Luba tace na samu taxi na bawa driver ta gaya masa unguwar da zai kawoni. Ban Sha wahalar samun taxi ba na hadashi da Luba da nake ta Jin hayaniya a gidanta bansan dai yanda Suka yi ba yaja taxi din muka tafi nidai kalle kalle kawai nake sai na tsinci kaina cikin mugun faduwar gaba da bansan mai ya hadasa min shi ba sai na danganta hakan da satar fitar da nayi ne. Tafiyar minti Ashirin muka iso wani hadadden gida bashida girma sosai amma ya had'u kafin na sauka na bawa taxi kudinsa na janyo karamin akwatina Ina karewa gidan kallo. Sai na fara k'ok'arin zuge Jakata dan na Kira Luba dan na tabbatar da a gidan aka saukeni. Muryar da naji yasani dago da kaina da sauri kirjina Kamar ya fado.... MG'S SKINCARE Dame akafiki yar uwata? Kyan fatar ko iya gyaran fatar? Ina riba g macenda t Maida kanta sauran mata? Shin haryenzu labarinmu kikeji ko kike bayarwa? Hajiyata miye matsalar? Fatar takice abun se lahaula? Kingwada kingwada harkinsare? Tsakanida Allah yaushe daren yayi balle wayewar garin? Inbakida labarin MG'S wacce tasanki tasansu, Gawurtaccen Kuma shahararren kamfanin gyaran fatane,duk lalacewar jiki,duk hautsinewar fata,duk yenda jikinki yazama abun kunya gareki, Ina tallata maki me gabadaya, Muntarkato,munwarwaro,munqullo duk wani Abu daze maidaki wanke hannu kataba mun qara a cikin kayayyakinmu,muncire,muntsife,munfidda,mun tantance mun hadamaku wasu irin hadaddun lafiyayyun kaya masu masifar goge fata,wallahi duk fitinar fatarki inshallah,kinzo bustop,kisiya kiyikyanda ko mace,kan juyo ta waiwayo ta dubi halittar Allah, Ga product din kamar hka, Sabulu 4500 Mg's beauty kit Karamin kit 12k Body soap Facial soap Body cream Face cream Glow oil Pink lip balm Flawless skin beauty kit Babban kit 20k Body soap Facial soap Body cream Face cream Scrub Glow oil Pink lip balm Note kowanne d kalanshi nd yanayin packaging dinma aren't the same, Tsakanida Allah kigafa Duk wannan garabasar Kuma kinazaune hba taso a dama dake a harkar yar uwata, Ayi hakuri da sauyin farashi komi yatashine muma b hka mukasoba Chat:08062991549,07046881166,07067210195, Call,+2348064532391 *NI DA KISHIYOYINA* *NA SADNAF* *E.W.F* *PAID BOOK* *Page 7* Salis ne rungume da farin showel da wasu maza biyu suna "Allah dai ya raya mana Bintu" Sai a lokacin ya gani nidai lissafi ya kunce min dan bansani ba ko gidansa luba ta saka aka kawoni ba gidanta ba jikina rawa kawai yake dan Luba bata kyauta min ba. Shi kuwa sallati ya saki da k'arfi Yana "Aishaaaa" Sai naga yaja da baya a tsorace hannunsa dai rungume da farin showel Nidai a tsayen da nake wlh banda rawa ba abinda jikina yake Kuma na kasa tunani ko na hasaso mai ke faruwa kamar dai an dasani haka na tsaya ban motsa ba. Ganin ya koma ciki da balain gudu yasa mamaki kasheni mai ke faruwa ne? Sai na tsinci kaina da sallati Ina tunanin dai gidansa luba tasa aka kawoni Kuma da kamshin gaskiya kenan Yana tare da wata sai kirjina ya buga da na tuna maganar maza biyun da na gansu dashi suna Allah ya raya musu Bintu" Ai bansan lokacin da nima na fada cikin gidan aguje ba kirjina na balain faduwa ba dai dagaske Salis yana tare da wata macen ba. Koda na Shiga gidan canopy naga guda biyu an saka a tsakar gidan Mata da maza a azazaune a fararen kujera da alama dai taro ake. Sai dube dube nake banga Salis ba. Sai na doshi cikin gidan a daidai lokacin da wata naga tana k'ok'arin fitowa nayi saurin tareta murya na rawa nace "Baiwar Allah dan Allah waye mai gidanan nazo ne bansani ba ko b'atan hanya nayi" "Gidan Dr Salis ne ai yau ake sunan Yar sa ko sunan Kika zo ai ki Shiga suna ciki shi da matarsa" Sai naji numfashina Yana k'ok'arin d'aukewa maganganunta na maimaituwa a kunne na nidai nasan Dr Salis ake ce mishi idan ba ciwon kunne nake ba kamar cemin tayi yau ake suna matarsa ta haihu ?dama Yana da wata matar ne bayan ni? jikina rawar da yake yasa na kasa motsawa sai sallati nake wlh k'ok'awa ma nake da numfashina. Nafi karfin minti biyar a haka bansan ma Ashe wayata bata hannuna ba Ashe luba da gaske take akwai abinda Salis yake b'oye min shi yasa yak'i barina nazo innalillahi wa Inna ilaihi rajiun. A hankali na taka dan matatakalar na shiga ciki dan madaidaicin Palo ne sai tsirarun mutane da suke cin abinci idona ya sauka akan kanin luba Nura dake ta loma abinci muryar yayar luba ya doki dodon kunnena "Aa Aisha sai yanzu kika iso"? Ban iya magana ba sai ido da na zuba mata dan a yanzu Kuma kwakwalwata ta tsayar da aiki inaso nagane wani abu kannen Luba a gidan Dr Salis mai hakan ke nufi mai take nufi da sai a yanzu nazo" Kallon da nake mata batare da ko kiftawa ba yasa ta ajiye plate din hannunta. Ta nufo wajena tana "Aisha lafiya kuwa"? A daidai lokacin da naji muryar Luba kirjina yayi wani irin bugawa na waiga da sauri. Masifa kawai take tana "Idan bata sani ba yanzu yaushe kake so tasani, salon ka Fadi ka mutu aki yarda cewar na haihu da Kai na gaji da kumbiya kumbiya gwara kawai ta sani a wuce wajen" Sanye take da shadda ruwan toka ya sha aiki har kasa Ina da irin shaddar har kalar dinkin bambancin nawa yafi nata turuwa ta sha kunshi kina ganinta Kinga mai jego had'a idon da muka yi da ita bai sa ta tsayar da maganar da take ba har sai da ta idda ta Kuma had'e rai tana "Aisha kin karaso"? Ban bata amsa ba na cigaba da kallonta inaso kwakwalwata ta bani hadin kai na gane mai Luba takeyi a gidan Salisu mijina ita da Yan uwanta. "Luba lafi ya kuwa ya naga Aisha a hargitse haka Ina salisun yake"? Cewar yayarta ita kuwa tace mata "Yana d'aki yanzu zamu shiga ciki ai" Aisha kizo mu Shiga daga ciki Ta juya tare da komawa d'akin da ta fito. Sai na tsinci kaina da bin bayanta zuwa lokacin nan wlh numfashi jansa nake da k'arfi kaina ma juyamin yake sai inaso nayi tunanin Wai Luba ce matar salis sai na janye tunanin Ina hararo fuskar wata a matsayin matar da Salis ya aura a boye kila matarsa kawar Luba ce shiyasa na gansu a gidan. Ina tura k'ofar naga salis ya kifa kansa a jikin gado ga jaririya a shimfide a Kan gado Luba Kuma tana jingine da wadrobe din d'akin. "Salisu" Na kirashi Kamar an fusgo maganar daga bakina a yanzu tunanina ya bani abinda ke faruwa luba kawata aminiya ta itace Salis ya Aura "Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Aisha kiyi hakuri kiyi hakuri innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Aisha bazan iya dago da kaina na kalleki ba wlh ba a san raina haka ta kasance ba Allah ya hukunta sai na auri Luba tunda ga rabon ya mace a tsakaninmu wlh ba cin amanarki nayi ba innalillahi wa Inna ilaihi rajiun" "Mtssss Wai kai mai hakane ya kake Abu kamar mace auren da muka yi haramune mtsss wlh karka sake cewa baa san ranka ka aureni ba da san ranka sarai ma dan da baka sona bazaka kwanta dani har na haihu ba,da baka sona bazaka kawoni Abuja wajen da kake aiki sabida ma Kar na nisance ka" Ta juyo ta kalleni tana "Kawata Salisu shekara daya kenan da aka daura mana aure dashi bisa yarjajeniyar bazaki tab'a sanin ya aureni ba wai nan gaba zai fada miki ya zabi ya ajiyeni anan sabida wai karki tab'a sanin munyi Aure ya Kuma zabi aurena ne sabida kawancenmu ya Kara k'arfi domin kina kaunata Ina kaunarki cigabanki cigabana ne Yana da kyau Kuma kaso wa dan uwanka abinda kaso wa kanka nasan islamiyya daya muka yi kinsan haka dan na auri Salis ba haramun bane ba Kuma haka zai saka Wai kawancen mu ya ragu ba a ganina hakan zai saka mu hade kanmu dake muci arziki tare ba wani abu bane ba auren Salis da nayi bai zai rage ki da komai ba tunda bai rage kaunarki ba wani abu bai ragu a jikinsa ba,ni a ganina boye mikin da yake shine munafirci amma ni ko lokacin da muka tsayar da magana wlh naso na fada miki ya hanani ko ranar da nazo dinan Kika ringa cewa kamar amarya nake ba karya kikayi ba kwana uku da daura mana auren ko zuwan da nayi wlh nayi niyyar fada miki sai Kuma na fasa dan ya rokeni sosai akan bayaso kisani,ni sai nake ganin da ya gaya miki sanin da na miki wlh bazaki hana ba dan naga kina balain san nayi Aure duk Yan gidanmu sun d'auka da yardarki akayi auren shiyasa kikaji Aunty Walee na tambayata