Sashe 45
Nida Kishiyoyina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Aisha "Yaya Salisu bai cancanci rufin asirin mu ba Yaya idan har zai iya Mana wanan cin amanar ya Rasa wacce zai nema sai muhasim yaya bai tsaya iya nan ba ya hada da karkata mata baki sabida Kar ta tona masa asiri zaluncin yayi yawa karka ce zaka yi hakuri sabida ni idan kayi haka bazan ji dadi ba muhasim itama 'yace Kamar kowa ka bari mu kwatar mata hakkin ta karka ce wai sabida ni baka so ayi karar sa mutuncinsa ya zub'e, Yaya mutuncinsa ya riga da ya zub'e a lokacin da Luba ta tona masa asiri a gaban yayansa,Yaya kila ba iya Muhasim Salisu ya tab'a yiwa irin wanan zaluncin ba kila ya dade yanayi gwara ayi kararsa asirinsa ya tonu sabida a a ceto wayanda zasu Kara fadawa tarkonsa Yaya idan har Salis zai iya neman maza bai cancanci a rufa masa asiri ba Luba duk ta tona masa asiri a wajena ban tab'a sanin mugu nake aure ba wlh irin su Salis a cikin Al umma masifa ne gwara kawai muyi kararsa a kwatar mata hakkin ta" ido Yaya mustapha ya zuba mata har ta idda magana yana "Kina nufin Luba ce tace miki Salis ne yayi wa Muhasim fyade Kuma har ya karkata mata wuya Yana neman maza Kuma"? "Itace ta tona masa asiri Yaya" "Kuma ya amsa da bakin sa shi yayi wa muhasim fyade"? "Eee Yaya yace Nana yarsa ce da bakinsa ya amsa haka" Sai da yaya mustapha ya d'au tsawon lokaci kafin ya mik'e Yana " idan har da gaske shi ya amsa da bakin sa shine mahaifin Nana zan yarda amma banaso ayi abin da zamu zo daga baya Muna Jin kunya dan wanan Luba tun daga lokacin daya aureta nake ce miki ban yarda da ita ba,a yanda nasan tsanar da ya mata har Yana fadamin lokaci daya naji labarin auren sa da ita nasan akwai boyayyen Al amari da Allah kawai ya barwa kansa sani ki nutsu muyi bincike mai kyau nayi mamaki da ya iya aikata irin wanan mumunan abin da nake ganin da hankalinsa bazai tab'a aikatawa ba kila Kuma San zuciya ya Kai shi da aikata haka" "Yaya ka daina k'ok'arin kare shi ya riga ya amsa da bakin sa shine mahaifin Nana Kuma wlh Yaya shi ya karkata mata baki sabida kar ta samu bakin da zata tona masa asiri" "Ya akayi toh luba ce tasan sirrin nashi"? "Ba Wanda yasan wanan sirrin sai ita kenan?akwai abinda nake san kema ki hango da kanki amma a yanzu lafiyar muhasim shine a gabana shine burina koma menene Allah ya bayyana mana gaskiya bazaki yi kararsa ba ki tambaya min shi kawai idan dai Yana da sa hannu karkacewar wuyan muhasim dan gani nake idan har ya amsa shine mahaifin Nana idan shine zai iya fada ya ce sabida rufin asirinsa yayi haka a lamarin nan ya Kamata ace bincike akayi mai zurfi Aisha batun tona masa asiri bai taso ba ko dan su Ashraf nima bazan so mutuncin babansu ya zub'e ba" Yaya wlh " "Ya isa Aisha ban yarda ayi kararsa ba zan nemi Ashraf muyi magana dan idan nace yazo kunya bazai bari yazo ki bar maganar kai shi karan nan kawai" Daga haka ya fice daga d'akin Aisha ta bishi da kallon mamaki dan bata tab'a tunanin zai hanata Kai shi kara ba har bayan wanan cutar da ya musu ace a barshi ba sai an kai shi Kara ba,duk abinan tasan sabida baya so mutuncin Salis ya zub'e ne Salis bai cancanci wani rufin asiri ba tunda har ya iya cin amanar yayanta. Kiran da ke ta shigowa wayarta ya katse mata tunanin da ta tafi. Koda ta d'auko wayar Salis ke kiranta Katse Kiran tayi tare da jan dogon tsaki sai a lokacin taga alamar ya tura mata sako kamar zata goge dan ko kadan batasan wani abu daya dangance shi, sai Kuma ta fasa ta bud'e message din "Aisha ki rufamin asiri karki gayawa Yaya dan Allah karki fada masa Aisha wlh sharrin shaidan ne ni kaina bansan ya akayi na nemi muhasim ba idan kin tuna a shekarun baya da na ringa kasancewa cikin tsananin bukata har lokacin muke mamakin yanda akayi na koma haka,a lokacin ne wanan kaddara ya fada min a ranar da kikaje asibiti idan Zaki iya tunawa abin ya motsa min kamar zan fice a hayyacina na dawo gida ban tarar dake ba na kasa dannewa bansan mai ya hau kaina ya jani nayi wa muhasim fyade sai da na dawo daidai na gane abinda na aikata wlh wlh ba da gangan na nemeta ba kimin adalci ki tuno yanayin da nake Shiga Kamar zan mutu idan ban samu nutsuwa ba ki tuna Aisha da ace ni mazinaci ne da zaki tab'a Kamani Ina neman mata da a lokacin bazan addabeki ba zan na zuwa wajen wasu su magance mun matsalata ne amma haka nake dawowa gida,da ace a ranar nasan bazan same ki ba bazan dawo gida ba da ace nasan ranar bazan same ki a gida ba wlh na gwammace na nemi koma wacce da na nemi muhasim,daga lokacin da abinan ya faru ban Kara samun nutsuwa ba kema kin Sha tashi ki gani a zaune Ina tunani,amma ki yarda dani bayin Kai na bane Kuma wlh Allah bani da hannu a karkatawar bakinta idan har nine tunda asirina ya riga da ya tonu zan fito na fada miki" Aisha tsaki tayi ta goge message din tare da danna masa blocking dan ta riga da tasan tsara zancensa yayi karya yake yi,daga lokacin da ya auri Luba ta daina yarda dashi,ba abinda zai yi a idonta taga farinsa tariga da tasan zaiyi duk yanda zaiyi dan.ya wanke kansa bata yarda bashi ya karkata wa muhasim baki ba. Sallamar Afrah da ummi da taji a Palo yasa ta zubawa k'ofar ido har suka turo k'ofar suka shigo,da ganin Afrah taci kuka ta gode Allah. "Hajiya umma dan Allah kiyi hakuri mu koma gida" Cewar ummi ta zauna a gefen gadon Afrah Kuma ta zauna a kasa ta tankwashe kafarta tana "Hajiya umma Abba ne ya turo mu akan mu baki hakuri dan Allah hajiya umma ki dan saurareshi yanzu haka mun baro shi bashida lafiya" "Bazan goyi bayan zalunci ba Afrah ke ba yarinya bace kingane duk abinda ke faruwa ki koma ki fada masa ya gaya miki abinda yayi wa muhasim wuyanta ya karkace idan har bai fada ba dole nayi karar sa ya fada a kotu,duk da Yaya ya dage amma bazan biyeshi ba,sabida muhasim bata cancanci haka daga wajen mu ba itama ya ce kamar kowa zan tsaya na kwato mata hakkin ta shekara Sha biyar sai dai a kwantar a tayar sa'ointa daga masu Yara uku sai biyu wlh bazan yafe masa wanan zalincin da ya mata ba" Ta karashe tana fashewa da kukan dake dankare a zuciyarta na tausayin muhasim a baya bata ji tausayin ta haka ba sai da ta gano Salis ne yayi wa muhasim fyade. Yaya mustapha yana fita daga d'akin ya fita can waje ya zauna ya zauna akan benci Yana kara nazartar maganganun Aisha baisan mai yasa ya kasa yarda da duk Salis ne ya aikata wa muhasim wanan zaluncin ba banda Aisha tace ya amsa da bakinsa akan shine mahaifin Nana da ya karyata,akwai abubuwa a baya da yake kara tunawa game da Salisu,ya sha zargin asiri Luba tayi masa ya aureta,idan ya tuna yanda yake fada masa. ya tsani Luba tashi daya yaji labarin wai ya aureta, anya Luba ba burinta taga ta raba Aisha da salisu ba yasa ta biyo ta haka akwai Abubuwan da yake so Salis ya warware Masa da kansa. Wayarsa ya d'auko a Aljihu ya nemo lambar Salis yayi dailing. Sai dai har ya masa kira uku bai d'auka ba sai text din sa daya shigo da "Bazan iya d'aukar wayar ka ba Yaya kunyar ka nakeji bansan mai zance ma dan Allah dan Annabi ka yafe min" Yaya mustapha mayar da wayarsa yayi cikin Aljihu ya shiga ciki ya d'auko mukullin motar sa ya tayar ya nufi gidansu Salis. Luba Da mugun sauri ta damko Asabe ta shaketa tana "Kinyi kad'an Asabe kinyi kad'an ki wulakanta ni,bazan baki ko sisina ba Kuma bazan miki wanke wanke ba wlh kin Dade baki tona min asiri ba ai bani kadai keda asirin da zaa rufa ba kema kina da sirrin da zan tona miki ko kin manta mu taru mu tonawa juna asiri mu ji kunyar gabad'aya har ni zaki ce nazo na ringa miki wanke wanke kinyi kad'an na miki wanke wanke ki tona min asiri na tona miki naki kudina Kuma da kikaci wlh sai ma kin biyani" Asabe murmushi ta saki tana "Luba na wuce duk yanda kike tunani zan baki mamaki wlh sai na tona miki asirin,asirina da kike cewa zaki tona ba na kashe kishiyata bane na saka mata guba a shayi ta sha ta mutu,wa zakije ki fadawa ya yarda? Wajen Wanda zaki tona min asirin kinsan kamun da na masa? An gaya miki bansan zakice zaki iya tona min asiri ba lailai yanzu na Kara yarda ke dakikiya ce tunda har kince bazaki min wanke wanke ko ki ringa biyana dubu hamsin ba a yau zan tona miki asiri kina fita Zan dau mayafina wlh duk sai na bankada sirrinki kije ki bankada nawa" Luba a hankali ta saki rigar Asabe hawaye na gudu a fuskarta tace "zan ringa biyan ki dubu hamsin din amma kiyi hakuri na samu a yanzu banida hanyar samun kudi ko biyar bana magani kudadena na wajenki sauran kudina da kaddarata Kuma salis ya hanani" "Wanke wanken ne dai bazaki iya min ba"? "Zabi kika bani na gwammace na ringa biyan naki" "Ina nan Ina jiranki wlh naji shiru kinsan halina na daga miki kafa a watan nan karshen wata naji dumus" Luba bata iya ce mata komai ba ta juya tayi hanyar waje tana Jin Asabe na mata dariya Tana fita ta fashe da kuka sai da taci kukan ta ta gode Allah kafin ta tsayar da abin hawa ta nufi gidan Salis tana Addu'a Allah yasa baya gidan dan so take