← Book details Nida Kishiyoyina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 71

Sashe 55

Nida Kishiyoyina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Idan kinje lahiran sai ki tona min asirin shegiya tsinanniya" Luba tace tana kara hankada Asabe dake wani irin makyarkyata jini na zuba a cikinta. Zagi ta cigaba da auna mata har sai da taga Asabe ta daina motsi ta baro bandakin tare da rufe kofar ko dar bataji ba balle nadama tayi wajen drawer Asabe ta hau hargitsa mata kaya sai da ta kwashe duka gwalagwalanta da kayanta masu tsada. zuba su a akwatin da ba komai a ciki ta cigaba da hargitsa d'akin har sai da ta samu kudade a karkashin gado shima ta zuba su a cikin akwatin. Ta rufe akwatin ta Kara lek'a bandakin ta Kai hannunta hancin Asabe da tayi shame shame a cikin jini taji bata numfashi ta fito daga bandakin tayi hanyar waje tana Jan akwatin sai da ta kara bincike d'akin mijin Asabe ta samu kudade a ciki ta kwashe duka ta saka a akwatin ta zauna palon tana tunanin garin da zata koma dan barin garin zata yi dadin da taji Yusuf bai San tana gidan ba sai maigadi,ta karanci Mai gadin Yana da ibada da fita massallaci Yana tafiya massallaci zata bar gidan. Haka ta zauna a palon tana kissime kissime da akwatin a gabanta har sai da ta ji kiran sallah Asuba. Ta mik'e a hankali ta nufi wajen window tana leka maigadin. Tana kallon lokacin daya fito Yana hamma da butarsa a hannu sai da taga ya fita tare da rufe kofar tayi sauri ta fito tana Jan akwatin dan hijabi tasaka har kasa,sai da ta fito daga gidan hankalinta ya kwanta. Sauri kawai take zubawa ko a yanzu batasan Inda zata dosa ba tafiyar kawai take a kafa ba ma abin hawa balle ta hau ya kaita tasha dan garin Lagos taji a ranta zata tafi dan ba yanda za'ayi a iya biyota har can Lagos tasan ma da wuya asirinta ya tonu a gane ita ta kashe Asabe tunda ba wanda yasan tana gidan mai gadi ma tasan ba lailai ya zargeta ba yanda ta Kara hargitsa ko'ina na gidan tasan zasu zargi Yan fashine suka shigo gidan suka kasheta. Ta tuno yanda ta bar Asabe a cikin jini taja tsaki a fili tana "Ke Kika jawowa kanki da ace kin bani kudina cikin ruwan sanyi da ban aika ki lahira ba Kya je ki hadu da kishiyarki lami da kika kashe haba sai dukan yamin yawa ga rashin kudi ga rashin miji da wane zanji" Kamar dai mahaukaciya haka taringa tafiya tana surutai haka ta ringa tafiya har sai da gari ya fara haske masu abin hawa suka fara dan wucewa ta tsayar da wani tace ya kaita tasha. Koda suka isa Tasha wajen da ake lodin Lagos tayi,irin zungureren motar nan masu kwasar fasinjoji da yawa ta samu sai da ta samu awa wajen uku kafin ya cika su dau hanyar Lagos da bata tab'a zuwa ba sai wanan karon. Salis Duk yanda yake d'aukar abin zai zo da sauki sai da suka rik'e shi akan sai sun tura shi station zasu cigaba da gudanar da bincikensu hankalinsa idan yayi dubu sai da ya tashi bai ga alamar kudin cin hanci zaiyi aiki a wajen su ba. Wai a haka ma dan Yana da kudi suka dan daga Masa kafa. Koda suka je station din aka mika case din wajen Dpo akan zaa cigaba da gudanar da bincike akan sa. Alhaji Salis fadar tashin hankali da yake ciki b'ata bakine baiso sanar wa da kowa halin da yake ciki ba dan gani yake abin kunya ne ma wani yaji labarin wai zargin da ake masa,a ba yanda zaiyi da cin hanci suka bashi wayarsa ya nemi Ashraf a waya akan yazo ya same shi a station Hajiya fauza ma an kulleta duk da itama ta kafe akan taimakawa yaran suke ba wani manufa da suke dashi na kai yaran waje. Minti sha biyar da Kiran ASHRAF sai gashi yazo station din sai da ya gwada musu I'd card dinsa kafin suka barshi yaga Salis da ya kara zabgewa sabida tashin hankali. "Abba mai yasa Suka kawo ka nan Abba kaga abinda nake gudu ko" "Ashraf yanzu kayi yanda zakayi a bada belina muje daga gida tukunna zan gaya maka komai" Ashraf sai da yayi dagaske Suka bada belin Salis sabida yaje musu a matsayin lawyer Salis. Koda suka d'auko hanyar gida ba Wanda yacewa wani komai Salis kuwa rufe idonsa kawai yayi Yana Jin inama duk abinan dake faruwa a mafarki ne,a lokaci guda duk asirinsa ya tonu. Yanda zai bawa Ashraf labari kawai take tunani yanda zai samu ya wanke kansa daga zargin da ake masa kawai yake dan sauran dan mutuncin nasa daya rage idan har labarin zargin da ake masa ya fita yasan zub'ewa zaiyi a idon kowa har gwara.masa ma fyaden muhasim da wanan abun kunya da Allah wadai dake neman samunsa. Dana sani keya ce Allah yasan yayi matukar nadamar halin daya jefa kansa zai iya cewa san zuciya ya kai shi tunda Yana dan samun na rufin asiri ta harkar Ngo din da yake zainab da dage ta ringa kwadaita masa har sai da ya tsunduma harka Yama fita zakewa a harkar. Koda suka isa gida d'akinsa ya shige sai yaji Yana Jin kunyar Ashraf Mai yasa bai tab'a tunanin irin wanan lokacin na zuwa da asirinsa zai tonu yaji kunyar mutane da na yayansa. Sallah kawai yayi ya kwanta baisan Kuma binciken da za'ayi iya wajen da zai tsaya ba,baisan ya akayi har aka gano su ba. Shigowar Ashraf d'akin yasa yayi saurin maida idonsa ya rufe Yana jinsa har ya zauna yasan kallonsa yake tsawon mintuna biyar a tsakani Ashraf ya fara magana yana "Abba inaso ka bani labarin sirrin da kake boyewa da har ta Kai da asirn ka ya tonu da tun farko ka fadamin da kila na samu maka hanyar da asirinka zai rufu Abba lokacin boye boye ya wuce ka fadamin kawai iya gaskiyar ka ni lawyer ne zanyi iya k'ok'arina domin na kareka duk da nayi rantsuwa akan goyon bayan gaskiya duk runtsi duk wuya amma babu yanda zanyi tunda rufin asirinka rufin asirin mu ne gabad'aya" Ajiyar zuciya Salis ya sauke kafin ya bud'e idonsa ya sauke akan Ashraf cikin wani irin murya ya fara bashi labari Waiwaye Da Zainab kawai yake muamalla a lokacin dayaje waje karatu,hasali ma zai iya cewa ita ta makale mishi duk da kana ganinta kasan kudi ya zauna mata a matsayinsa na dalibi haka take kashe masa kudi,kamar bata san ciwon kudin ba har yakan yi mamakin yanda take samun kudin,dan a labarin da ta bashi Iyayenta sun rasu ba kuma samari yake ganinta dasu ba ballantana ya zargi ko su ke.kashe mata kudi,abinda ya kara daure masa kai ba iya shi kadai take kashewa kudin ba duk wayanda take mu'amalla dasu suna morarta,abinda ke dan daure masa kai bai wuce yanda take muamalla da mata da yawa a wata Kuma zatayi tafi kasar Dubai sai ta kwana biyu kafin ta dawo. A lokacin da tayi tafiya salis Kuma ke samun damar da zaiyi nashi tsalle tsallen dan a gidanta ma yake zaune.ita ta sabar masa da wani irin rayuwa na san Mata. A irin wanan lokacin ta dawo daga tafiya Yana makaranta yana dawowa ya tarar da ta dawo. Da niki nikin akwati sai da suka samu nutsuwa da juna suna hira yake tsokanarta da Ina tsarabar da ta yo mishi dariya ta saka masa tana ba ta kawo.masa wani tsaraba ba shi kuwa ya mike yana bata isa ba baiyi wata wata ba yayi wajen akwatin nata ya fara k'ok'arin bud'e k'aramin. Kafin ta taso har ya bud'e akwatin A tsorace ya mike tsaye Yana gwalo idonsa waje dan.tunda yake bai tab'a kudi mai yawa haka ba,ita kuwa ta karaso ta rufe akwatin tana dariya yanda ya zaro ido. A ranar ya kasa hakuri har sai da ya tambayeta da Ina take samun kudi haka? Tace mishi ya bata lokaci zai fada mata idan shima yanaso ya zama mai kudin duk zata nuna masa hanya. Haka ya ringa naci Yana binta dan ta fada masa Inda take samun kudin amma tana kakaucewa a karshe da ta gaji da nacinsa ta masa alkawarin tafiya dashi. A haka watarana ya shirya yabi Zainab zuwa dubai,a nan ya gano kazamin rayuwar da Zainab take kudi ke shigo Mata,ita ke nemo wa larabawan masu kudi Yan mata da suke muamalla dasu,muamallan ma irinta da dabobbi su Kuma su biyata ita Kuma ta biya yan matan. Larabawan basu dauki bakakken fatan a bakin komai ba dan ba iya amfani suke dasu ta baya ba har idan zasuyi ba haya ko wani abu a jikin matan sukeyi da suka zabi neman kudi ta karfin tuwo zainab bata tsaya iya nan ba ta hada da muamalla da miyagun kwayoyi. A ranar salis bai iya bacci ba sabida tashin hankali ya kasa yarda da irin rayuwar da yaga masu kudin nayi da yan matansu bak'akk'en fata wani ma bashi ke amfani da macen ba karensa zai samowa mace lafiyaye shi ma yaci dadinsa da mutum. Har suka dawo zainab bata gane kansa ba dan shi dai abinda ya gani ya daga masa hankali daga labarin da Zainab ke bashi tana safarar Yan mata da kwayoyi ta kaiwa larabawan nan su bata kudi,tana nunawa Yan matan taimakon su zatayi da hanyar nema musu aiki ko wani abu basa sanin ainihin aikin da zasuyi sai idan ta Kai su. Ta Kara da "sabida kaunar da nake ma na gwada maka hanyar da nake samun kudi,aikin likita ko wani abu ba inda zai Kai ka idan dai har kana so kayi mugun kudi sai ka hada da wanan sana'ar da nake da ke shigo min da kudi kafara da safarar cocaine sannu a hankali idan ka koma kudi sun zauna maka sai ka fara hadawa da wanan da shi yafi shigomin da kudi" "Zainab bazan tab'a iya wanan sana'ar ba har yanzu da nake zaune Ina ta mamakin abinda na gani wanan wane irin rayuwa ne sai kace ta dabobbi Ina ma zan samo mutane Kai bazan iya ba harkar cocaine dinan akwai hatsari" Murmushi zainab ta masa a ranar ta Masa kyautar
Chapter 55 · 0% Book details