← Book details Nida Kishiyoyina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 71

Sashe 53

Nida Kishiyoyina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Asabe tasan wata ai batasan wata ba idan takamarta mugunta zata nuna mata ko aji daya batazo ba. Koda suka isa bayan boys quaters Asabe ta kaita tana wani huhura hanci ita a lailai ga ta zata taimaka mata tsabar wulakanci duk girman gidan ta rasa wajen da zata ajiyeta sai d'akin da tarkace ake sawa "Yanzu zan d'auko miki katifa akwai bandaki a ciki nan dai yafi miki babu ko ni fa dan inada zuciya musulunci ma yasa na taimake ki dan ni so nayi wlh na miki rashin mutunci dazu bansan Kuma mai yasa na canja ra'ayina ba ki goge lambar Yusuf yanzu a wayarki Ina kallonki Luba lambar Yusuf ta dubo ta haska mata kafin ta goge,duk da haka Asabe bata yarda ba sai da ta karbi wayar ta shigar da lambar Yusuf taga baya cikin contact dinta tayi blocking lambar tare da goge lambar tana "bari na dubo miki Kaya a cikin tsofaffin kayana ki ringa sawa" Daga haka ta fice daga d'akin. ,duk yanda Luba ta so hadiye bakin cikin wulakanci da Asabe ta mata kasa hadiyewa tayi sai da ta fashe da kukan bakin ciki tana karewa dakin kallo wulakantata kawai dama Asabe ke San yi dan ko d'akin mai gadi yafi wanan girma ko a mafarki akace mata zata tab'a Shiga gararin rayuwa irin wanan karyatawa zatayi rashin hankali da rashin zurfin tunani ya kaita ya baro ta cutar da kanta ta tonawa kanta asiri dan ba Salis ta tonawa asiri ba ta tuna girman dakinta da haduwarsa ko a yanzu kayan da bata dinka ba na kasan akwatinta ya kusa Sha biyar tsadaddu Wai duk yanda take da Asabe yau Asabe ita ke wulakanta ta haka da ace tana da wajen zama wlh ba abinda zai tab'a sakawa ta biyo Asabe,a bata da yanda zatayi ta biyo Asabe minti goma a tsakani sai ga Asabe da Kaya ta rungumo tana zuwa ta watsa a tsakar dakin,Luba tabi Kayan da kallo duk tsofafin kayan Asabe ne duk babu na arziki ma a ciki. "Sai anjima kenan sai kifito ki dan shashare mana gidan kafin mai gidan ya dawo ya naga Wai kina b'ab'ata Rai ne" ko ban miki k'ok'ari ba? Murmushin yake Luba tayi tana "kinyi k'ok'ari ngd" "Aa toh na d'auka zakice ban k'ok'arta Miki ba sai ki dan fito anjima kiyi abinda zakiyi kafin ya dawo ko" Luba gyada Mata kanta tayi dan bazata iya magana ba da ido ta bita har ta fice daga d'akin "Dan Allah ki bani rancen kudin nan Luba idan baki taimaka min ba wa zai taimaka min haba Aminiyata" "Asabe ba hanaki zanyi ba banida kudi ne Amma ki bari Alhaji ya dawo Zan tambaye shi nasan bai isa ya hanani ba kinsan idan inasan abu ya hanani yanzu nan zance zan tona masa asiri" Dariya Suka kwashe dashi sai da Asabe ta take cikinta ta hada da take away a lokacin batayi aure ba da kuwa Salis ya dawo haka ta saka shi a gaba sai da ya bata kudin,ta Kira Asabe akan tazo ta karba wanan kad'an daga cikin Abubuwan da tayi wa Asabe bazata iya fadar ma morar da Asabe ta mata ba Wai yau ita ta kawo gidanta da Sunan Yar aiki ta cije lebbenta a lokacin da ta tuno baya tana "Asabe kafin ki wulakani ni zan wulakanta ki" Tana susa ta dan gyara d'akin ta Shiga bandaki tayi wanka a cikin kayan da ta kawo mata ta dauko daya ta saka tafi Asabe kib'a dole kayanta suyi mata kadan amma haka tasa a jikinta. Ta shafa maganin ta a jikinta ko kasanta zai rage mata kaikaiyi Wato har kumbura jikin ta yayi sabida tusa inama tana da halin da zata shafawa asabe wanan masifar da ta shafa mata. Yunwa take ji amma ba yanda zatayi dan tasan ta nemi Asabe ma ta bata abinci sai ta wulakanta ta. Karfe biyu ta fito daga d'akin tayi cikin gidan sai take Jin wani banbarakwai a baya a motarta take zuwa Asabe tazo ta tareta wai yanzu ita zata je ta mata wanke wanke har da shara. A Palo ta tarar da ita ta mimike kafa akan kujera tana Shan fruit basu cewa juna komai ba tayi kitchen dan ta fara wanke wanken tana shiga kitchen tajiyo muryar Asabe tana "Kar fa ki taba komai wanke wanke kawai zakiyi ki fito sai anjima zan zo na dorawa mijina girki da kaina" Luba bata ce komai ba ta fara wanke wanken tana tausar zuciyarta dan tasan tana dab da samun cikar burinta zata shanye duk wulakanci da Asabe zata mata. A takaice tana ji tana gani ta zama yar aikin Asabe sabida kawai ta samu wajen da zata saka hakarkarinta,abincin ma bana arziki take bata ba kamar ta roka,ko kad'an ba mai yarda wai sun tab'a wani kawance dan Asabe har wani aikenta takeyi sabida kawai ta wulakanta ta wanan kenan. Salis A cikin sati guda idan ka ganshi dauka zaka yi ya shekara Yana jinya sabida tashin hankali a yanzu lambar uje ma baya tafiya gani yake a kowane lokaci Yan sanda na iya duro masa. A yau ya shirya fita asibitinsa bawai dan yasan zai iya tsinana komai ba sai dan so yake ya dan Kara samun nutsuwa kafin yasan abin yi. Iyayen Aneesa sun matsa masa har sai da ya saki Aneesa saki daya,rabuwarsa da Aneesa ya kara hargitsa shi. Koda ya isa office haka ya ringa sakawa Yana kuncewa a karshe ya d'auko wayarsa ya fara k'ok'arin Nemo lambar hajiya fauza turo k'ofar da akayi da shigowar Hajiya fauza da wasu a cikin fararen kaya yasa gabansa wani irin faduwa amma yanda yaga Hajiya fauza fuskarta ba wani tashin hankali yasa shima ya aro jarumtaka ya dake Yana amsa sallamar da suka masa sukayi musabiha da mutanen da kana ganinsu kasan hukuma ne seat ya nuna musu akan su zauna suka girgiza masa Kai "dayan ya fito da I D card dinsa Yana "Alhaji idan bazaka damu ba muna so "zamu tafi da Kai office akwai Yan tambayoyin da zamu maka" "Dafatan ba wani abune ya faru ba"? "Sai dai munje daga office din zaka ji" "Alhaji Salis mik'ewa yayi Yana "Muje" Sallati kawai yake a zuciyarsa Yana Addu'a Allah ya rufa masa asiri tunda yaga Hajiya fauza yasan asirin sa ya gama tonuwa amma zai dake duk tambayar da zasu masa sai ya musanta musu. Koda suka isa wani office suka Kai shi ba karamin k'ok'ari yayi wajen Aron jarumtaka ba, iya fuskar Wanda Suka Kai shi wajensa ya isa ya Kada Masa yayan hanji dan fuskarsa sam ba annuri takardar dake gabansa ya matsar gefe yana "Alhaji Salisu gidan marayun nan daka bud'e shin mallakin ka ne ko na wani"? "Mallakina ne ba na wani ba" "Da kyau ko zaka iya fada mana manufarka ta bud'e wanan gidan marayun"? "Dama ana bud'e gidan marayu da wani manufa ne ai ana bud'e gidan marayu ne sabida a taimaka wa Yara marasa galihu da wayanda suka rasa iyayensu ko" "Alhaji muna zargin ba dan wanan manufar ka bud'e Wanan gidan marayun ba ka bud'e ne sabida wata biyan bukatar ka ko zaka iya fada mana Inda aka Kai Yan matan da samarin dake gidan marayun Alhaji ka fito kawai ka fada mana gaskiya karka wahalar damu" "Ba inda nake Kai su Ina dai d'aukar nauyin karatunsu tamkar yanda kowa yasan Ina d'aukar nauyin komai daya shafi Wanda ke gidan marayun nan ko a yanzu haka karatu suke yi a waje" "Baka shirya fada Mana gaskiya ba Alhaji domin akwai yaran ka da muka kama itama mai kula da gidan marayun ta dage ba inda kuke Kai yaran yanzu Ina wanan yarinyar take"? Mutumin ya tura masa hoton wata Yar budurwa da bata fi shekara Sha biyar ba gabansa Yana "wane kasa ka turata karatu kuma a yanzu ya za'ayi mu sameta"? "Banida masaniya dan iyakacina d'aukar nauyinsu bazai yu na Kuma ringa bibiyarsu ba Hajiya fauza ita tasan komai a kansu zata iya sanin kasar da take da Kuma yanda za'a sameta" "Muktar" Mutumin ya kwalla Kira da sauri ya shigo ya Sara masa yace "jeka shigo min da mai kula da gidan marayun nan". ASHRAF A cikin kwarewa da aikinsa ya fara bincikensa kuma Allah cikin ikonsa Yana ta samun duk abinda yake so Yanzu saura kad'an ya kamalla bincikensa. A yau gidan Yaya mustapha ya nufa wajen karfe uku na yamma a lokacin da ya isa gidan Yaya mustapha baya nan Aisha da Aunty mamy ya tarar a falo sai muhasim dake Kan kekenta da alama duk ba kowa a gidan. Har kasa ya duka ya gaida Aisha da Aunty mamy kafin ya samu waje ya zauna Yana "hajiya umma na fara bincike ne akan case din muhasim yanzu akwai tambayoyin da zan yiwa muhasim idan bazaku damu ba inaso Zan Kai ta d'aki" "Kana da hankali kuwa muhasim da bata iya magana zaka yiwa tambayoyi" Murmushin Ashraf yayi Yana "Nasan bata magana ai hajiya umma ki barni kawai nayi aikina" "Kayi haukanka dai" "Jata ka kaita d'akin Ashraf karka biye mata batasan ku din Allah ya muku baiwa bane idan har kasan da yanda zakayi din ka kaita d'akin" Ashraf mik'ewa yayi Yana dariya ya hau Jan keken muhasim yayi d'akin su da ita wuyanta na nan a karkace tana ta wurga idanu A gabanta ya zauna ya bud'e jakarsa ya fito da wani farin takarda da biro a hannunsa Cikin murmushi ya kalli Muhasim da shi take kallo wuyanta na karkacen hakan yasa yaje ta wajen da zata iya ganin komai Ya fara magana yana "Aunty muhasim nasan duk abinda zan fada kina jina amma bazaki iya bani amsa ba,inaso na gano wanda ya karkata miki wuya ne duk tambayar da na miki idan hakane ki lumshe idonki idan ba haka bane karki lumshe idonki kinji"? Gani yayi ta lumshe idonta ya saki murmushi dan yasan taji mai yace Hoton Salis ya fara daukowa ya haska mata Yana "Shi ya miki fyade ko"? Lumshe idonta tayi hawaye na zubo Mata Ta sake bud'e idonta yace "Kuma shi ya karkata miki wuyanki sabida Kar asirinsa ya tonu ko"? Sai yaga ta tsura masa ido bata lumshe
Chapter 53 · 0% Book details