Sashe 71
Nida Kishiyoyina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
damu ba amma jininsa ce Luba sai ya tsinci kansa cikin damuwa,irin wanan ranar ya ringa hangowa Luba fada da nasiha ba irin wanda baya mata har sai da ya gaji ya kawo ido ya zuba Mata,fadan da yake mata akan Asabe tun lokacin da tayi Aure ya gano ba matuniyar arziki bace sai da Luba ta masa rashin kunya ta nuna ba haka ba,yau ga irinta nan duk da itama da nata bakin halin Asabe ta kai ta ta barota Koda su Habiba Suka tafi kotun bai bisu ba. Aisha da Aunty mamy a suna daga gaba dan Aisha Allah Allah ta ringa yi gari ya waye dan babban burinta taga an yanke wa Luba hukunci Mai tsauri inta Kama ma ayi mata hukuncin kissa ta hanyar rataya,bazata iya fasalta illar da Luba tayiwa rayuwarta ba. Daga lokacin da aka shigo dasu kallo daya tayiwa Luba da suka hada ido ta d'auke kanta tana jinjina lamarin ubangiji Wai hukuncin dan Adam ne ya firgita luba haka hukuncin dan Adam ne ya maidata haka inaga ranar da duk zamu tsaya gaban Allah wani irin tsoron Allah ne ya Kara shigarta da ido ta raka Luba har ta shige witness box ko kad'an bata ji alamar tausayinta ba dan Luba tayi abubuwa da yawa da ya Kamata ayi mata hukuncin. Luba tana daga tsaye da idonta da sukayi luhum luhum ta ringa bin mutanen dake cike a kotun sultan ta hango da ilham suna daga gidan gaba sun zuro Mata ido, d'auke kanta tayi da sauri tana Jin hawaye na kara gudu a fuskarta ta riga da ta makara ba dama ta maida hannun agogo baya ballantana ta gyara kuskurenta,duk abinda ta aikata nasan zuciya bata tab'a tuno da makomar yayanta ba,bata tab'a tunanin halin da zata jefasu a ciki ba,ita dai bukatar da ta saka a gaba shine kawai burinta, a yau sai ta tsinci kanta da kunyar yaran da ta Haifa a cikinta sabida San abin duniya ta rabu da mahaifinsu,ta wulakanta shi,ta watsar dasu taje tayi auren cin Amana duk a san abin duniya,sai a ayanzu ta yarda yan Adam suna da gajen hakuri,da ace yau tayi hakuri ta zauna da Hamza da kila tayi arzikin cikin kwanciyar hankali,yau gajen hakurinta san zuciyarta ya kaita ya baro,ta tashi a tutar Babu, ba miji ba yaranta ba dukiyar. A hankali ta Kara maida kallonta cikin mutane ta hango mahaifiyar ta da ta rufe bakinta da hannu da gani kuka take tamkar yanda Habiba dake gefenta ke kuka, batasan lokacin da kukan da take rikewa ya kwace mata ba,inama tana da sauran lokacin da zata gyara kuskurenta,inama tana da lokacin da zata farantawa Iyayenta,inama duk rayuwar da tayi a baya ace mafarki ne,inama duk cutar da tayiwa Aisha ace ba dagaske bane mafarkine,lokacin inama inama ya riga da ya wuce,ta cutar da mutane da yawa da ya Kamata ta nemi yafiyar su. Yanda take risgar kuka haka Asabe itama take risgar kukan,Asabe duk tafi Luba ma shiga tashin hankali. A lokacin da Alkali ya fara karonta Abubuwan da suka aikata Asabe dafe kirjinta kawai tayi da taji Yana barazanar fadowa,Luba kuwa runtse idonta kawai tayi tana jiran hukuncin da alkali zai yanke musu,Jin alkali yace "kotu ta yankewa Lubabatu Bashir shekaru Ashirin a gidan yari batare da ko tara ko beli ba, Asabe lawan Kuma kotu ta yanke mata hukuncin daurin rai da rai Asabe sakin wani irin wawan ihu tayi tare da zubewa a kasa. Luba kuwa ta rik'e witness box tana ihun alkali ya mata sausauci shikenan a gidan yari zata Kare rayuwarta nan da shekara Ashirin masu zuwa ai tasan tama mutu,ihu kawai take bata ma Kara sanin mai alkali ke cewa ba har yansandan suka zagayo wajen da take suka saka mata ankwa,Asabe Kuma aka kinkimeta dan sumewa tayi,cikinta Kuma na ta zubar jini, Ihu Luba ta ringa yi tana mik'a hannu tana "Aisha ki yafe min mama Kinga za'a tafi dani ki yafe min ki rok'a min baba dan Allah Aunty Habiba shikenan rayuwata ta kare Salis ka yafemin, dan Allah karka kora su Abdul ba dan halina ba ka rikesu tamkar kai ka haifesu,bansan inda zasuje ba idan ka koresu tunda mahaifin su ya rasu Ka taimaka min Shine abinda tayi ta fadi har aka shige dasu mota. Salis kuwa sai yaji ma hukuncin da aka yiwa Luba bai masa ba,yaso ace ita aka yiwa daurin Rai da Rai din,ko bata rokeshi ba Shima baiyi niyyar rabuwa da yaran ba dan Aisha ma ko a jikinta a haka suka fara fitowa daga kotun,kowa na fadar albarkacin bakinsa. Salis kuwa da Yaya mustapha suka tsaya a jikin motarsa Yaya mustapha ya hau shigo masa da maganar Aisha akan ya mata magana akan ta koma d'akinta. Salis murmushi kawai yayi yana "karka matsa mata Yaya idan bataso ta dawo ka kyalleta ni yanzu komai ma ya ficemin a rai wlh" "Aa sai dai idan Kuma ka daina ra'ayinta ne amma ai dolenta ta dawo" Salis murmushi kawai yayi bai ce komai ba dan yaga ma kamar Aisha kunyarsa takeji shi dai a yanzu ya samu kwanciyar hankali abinda ya rage masa samun lafiyar muhasim da zasu tashi jibi a cikin masu kaita har da Ashraf. Yasamu yayi cuku cuku an fitar da John da Hajiya Shafa yanzu Kuma yanda zai gyara lahirarsa kawai yake nema. Kwana biyu a tsakani aka fita da muhasim waje Salis yaso binsu Kuma ya fasa dan ayyuka sun dan masa yawa. Hindatu kuwa ganin ba kowa a gidan yasa ta zage wajen San taga ta karkato da hankalin Salis kanta,dan ta lura ta karfin tuwo Aneesa ke san dawowa rayuwar Salis kila ta danna zawarci taji ba dadi,idan Salis yayi bacci haka take d'aukar wayarsa tayi ta duba messages din da take turo masa take kuwa zata goge a karshe ma sai tayi blocking din ta,a yanzu idan akwai wacce take so ta dawo gidan bai wuce Aisha ba tana Kuma fatan idan ta dawo yazama iya su biyun kawai Salis zai zauna dasu,a wajen Afrah take Jin labarin Aisha sun fita waje da muhasim da duk wani abu ma da yafaru dan daga Ashraf har Salis din ba Wanda ya bata labarin duk abinda ke faruwa tayi matukar mamakin Abubuwan da akace Luba ta aikata Wanda har ya kaita da a kulleta duk da basuyi zaman Dadi da ita ba sai taji tana tausayinta. Wata uku a tsakani su Aisha suka dawo gida nijeriya,ko a mafarki basu tab'a tunanin muhasim zata koma yanda take har ta warke ba sai gashi da karfin Addu'a da kwararrun likitoci da aka samu muhasim ta samu sauki wuyanta ya koma yanda yake haka ma bakinta,kuka kam a lokacin ta Sha har idonta na yaji,sai Fadi take bazata tab'a yafewa Luba da Asabe abinda Suka mata ba dan sun cutar da ita sun watsa mata rayuwa dan duk bayanin da Luba da Asabe sukayi ta gano Salis ba a hayyacinsa yayi mata fyade ba. Yaya mustapha kuwa har da sadakansa sabida farinciki samun lafiyar muhasim. Gidan yari. Wani irin wahaltacen rayuwa Luba da Asabe ke yi a gidan yari da ko makiyin su baza su tab'a fatan suyi irin rayuwar da sukeyi a gidan yarin ba,Luba tayi nadama yafi cikin kwando,kwananta biyu a gidan yarin Yan uwanta suka je ganinta da yaranta haka ta ringa kuka tana neman yafiyar su,Asabe kuwa ta dan samu ma tabin hankali dan haka kawai zata fasa ihu ta hau fusge fusge tana fadar Abubuwan da tayi da bakinta. Luba kuwa a yanzu wani irin ruwa ma take fitarwa a jikinta Mai shegen doyi gabanta fal yake da kuraje, a yanzu ma ware mata waje aka yi ita kadai tamkar yanda aka ware wa Asabe waje,da ace zasu iya maida hannun agogo baya da duk basu aikata abinda Suka aikata ba dana sani kuwa keya ce sai dai fatan Allah ya bamu ikon fin karfin zuciyar mu ya tsare Mana imaninmu. Aisha kuwa a lokacin da Suka dawo Yaya mustapha sakota yayi a gaba akan ta koma d'akinta. Aisha kuwa kunya da nauyin yanda zata koma gidan salis bayan duk cika bakin da tayi yasa ta cewa Yaya mustapha ita dai ya barta bazata koma ba, ganin Yaya mustapha ya nuna b'acin ransa gasu Ashraf da suka sakota a gaba da magiya yasa ta amince da zata koma. A ranar Asabar Aunty mamy suka rakata ta koma gidan salis Kamar wata amarya ko Salis din ma baisan a ranar zata dawo ba,dan duk kin sanar masa suka yi. Salis har ga Allah a lokacin da ya dawo yaji dadin dawowarta dan gani yake itace fitilar dake haska gidan. Kulawar da ya kwashi shekaru bai samu ba a ranar Aisha ta bashi dan ba karya itama tayi kewarsa. A yanzu Salis yasan ya samu nutsuwar da yake dashi kafin Luba ta shigo rayuwarsa,a yanzu yasan ya samu kwanciyar hankali,Auren muhasim da Afrah Yana cikin Abubuwan da suka matukar faranta masa rai,dan Muhasim ko shekara biyu batayi ba ta samu mijin Aure. Har a yanzu Yar b'uya sukeyi da ita idan sun had'u dan kunyar juna suke ji Luba kuwa yafiyar Allah kawai take nema dan a yanzu babban burinta Allah ya yafe mata Abubuwan da ta aikata,da taimakon su sultan dake zuwa dubata akai akai ta aikasu wajen Aisha da Salis akan su yafe mata ciki kuwa har da muhasim,dak'yar dak'yar ta samu da naci da komai suka ce sun yafe mata, mahaifinta ma kafin ya rasu yazo gidan yarin dubata ta nemi yafiyarsa yace ya yafe mata,Asabe kuwa abin nata yayi tsamari da sai da aka dangana da kaita asibitin mahaukata. *ANAN NA KAWO KARSHEN NOVEL DIN NIDA KISHIYOYINA KUSKUREN DA NAYI A RUBUTA NOVEL DINAN INA ROKON ALLAH YA YAFE MIN SAI MUN HAD'U A SABON NOVEL DINA INA MUKU FATAN ALHERI MASU BIBIYAR NOVELS DINA*.... Times New Roman Times New Roman Calibri Calibri !%),.:;>?]} $([{ SummaryInformation DocumentSummaryInformation WpsCustomData TECNO LD7 WPS Office d2fd08778a6749c384b9b17b2befc975