Sashe 69
Nida Kishiyoyina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
akan wani dakali suka ringa watsa mata ruwa suna mata fifita Koda ta farfado kuka kawai take tana Luba ta cuceta Allah ya Isa tsakaninta da ita. Ashraf kuwa sai rarrashin ta suke Alhaji Salis daya hango yasa ya mik'e ya nufi wajensa da isarsa ya zauna a gefensa Yana "Abba ba kuka zakayi ba ka godewa Allah da gaskiya ta fito akasan duk abinda ya faru ba yin kanka bane sharrin Luba ne Abba dama akwai alluran da ake yiwa mutum wuyansa ya karkace haka da baki" Gyada masa kansa yayi Yana "Akwai amma baa fiye samunsa anan ba sai kasar waje nayi matukar mamaki da yanda har suka samu alluran Suka yi mata tunanin mu a lokacin bai tab'a bamu akan allura aka mata ba" "Kasan to Dr Saeed din"? "Aaa bansan shi ba may be ta bakin Luba Asaben ce ta hadata da wani likitan amma babu wani Dr Saeed da muke dashi a asibitin a wanan lokacin" "Abba zaa samu maganin toh da zai warkar da ita tunda angane mai aka Mata"? Za'a samu idan aka fita da ita waje Luba ta cuceni ASHRAF mahaifiyarka ma ta cuceni dan duk ita ta bawa luba k'ofa taci galaba a kaina" "Kayi hakuri Abba Allah ya riga da ya rubuta hakan zai faru baku isa ku k'aucewa kaddararku ba ka godewa Allah da asirinta ya tonu" Salis bai Kara cewa komai ba a daidai lokacin da Yaya mustapha ya nufo wajen da suke zaune. Ashraf shi Kuma ya mik'e yayi cikin kotun. Minti talatin a tsakani aka koma cikin kotun gabadaya Luba idonta yayi luhum luhum sabida kuka,Asabe kuwa gumi kawai takeyi dan batasani ba ko itama kotun zasu iya zargarta su daureta. Sai da Alkali yayi gargadi akan yin hayaniya da magana batare da an bada dama ba kafin yace Ashraf ya cigaba daga Inda ya tsaya. Ashraf ya karasa gaban Asabe Yana "kikace Dr Saeed shine ya bawa Luba alluran da aka yi wa muhasim bakinta ya karkace da aka bata alluran ta kawo miki kin gani"? Asabe sai tayi sauri ta girgiza kanta tana "Aa bata kawomin ba sai da tayiwa muhasim din alluran tazo gidanmu take fadamin" "Ta Baki labarin yanda akayi ta mata alluran a Kuma Ina tayi mata alluran dan Muhasim a bayan makarantar su aka tsinceta a kwance" "Eee a lokacin cemin tayi a ranar da aka bata alluran washegari taje makarantar islamiyarsu muhasim tace mata ta samo mata maganin da cikin zai zub'e dan haka gobe tazo ta sameta da sassafe ta shafa mata maganin a cikinta tana shafa mata cikin zai zub'e, ta kwatanta Mata gidan da zata zo ta sameta,shine washegarin ranar muhasim tazo gidanmu da sassafe Au taje gidansu Luba da sassafe ta sameta shine ta mata alluran ta tari abin hawa taje ta jefata a Bayan makarantar" Murmushi Ashraf ya saki yana "Kinaso kice bakya wajen akayi alluran"? "Eee gaskiya labari tabani" "Amma yanzu Kuma kince tazo gidanku da sassafe ita muhasim din kenan a tare kuka mata alluran" "Aaa gaskiya ba gidanmu tazo ba gidansu luban taje" "Toh menene dayan sirrin Luba da kike san fadawa kotu" "Yaran da Luba ta haifawa Salis" Ihuuuu Luba ta saka Asabe kuwa ta cigaba da magana tana "Bintu ce kawai Yar Alhaji Salis sauran biyun yaran Dr Saeed ne dan shima barazana ya ringa mata akan idan bata bashi hadin kai zai tona mata asiri" "Kin kasheni Asabe kin cuceni ke Kika bani shawara fa Asabe ke kikayiwa muhasim allura fa bani ba wlh karya take min Yanda ta ringa ihu da kururuwa yasa alkali buga gudumarsa Luba kuwa ta Yanke jiki ta Fadi. Shigowar wani kotun da Yan sanda ke biye dashi a baya yasa Asabe ja da baya cikin ihu tana "Ghali"............ Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba ko kit dinsu inamai shaidamuku anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne, knuckles,wrinkles,stretch mark dama dukkan wani prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using sabulun mg's batare da kunbukaci wani Mai b Mai bukata should Chat 08062991549 07046881166 07067210195 Call 08064532391 Team glow *WANAN LITTAFIN NA KUDINE BIYA 500 TA WANAN ACCT 0272061655 WEMA BANK NAFISA NUHU KO KATIN MTN KO AIRTEL TA WANAN LAYIN 08033719070 DOMIN KI MALLAKI NAKI KI MUTANEN NIGER KUMA KU TUNTUBI WANAN LAYIN* *+227 96 82 89 84 DUK WACCE TA MIN SHARING NA BAR TA DA* *RABBI ZAI FIDDA MIN HAKKI NA DA IZININ ALLAH DOMIN BA YAFEWA NAYI BA* *NI DA KISHIYOYINA* *NA SADNAF* *PAGE 38* Asabe jikinta ne ya hau karkawa,Wanda ta Kira da ghali ya tsaya a gefen witness box a daidai lokacin da Yan sanda suka watsawa Luba ruwa ta farfado. Tana cigaba da ihun kuka ghalin da tayi tozali dashi a tsaye yayi zuru zuru yasa ta saki ihu tana "Alhamdulillah ya Allah ga Ghali nan Asabe idan kina tunanin ni zaki tona asiri naki ya rufu toh gashi nan Allah ya turo shi kema ya tona miki asiri. Asabe tuni ta jike da gumi tana sallati a ranta tana ta mamakin ya akayi aka kamo Ghali uban me yazo nema a kotun ai indai Ghali ya tona mata asiri ta Kade har ganyenta ta saci kallon Yusuf dake tsaye idonsa jajjur,tamkar yanda shima Salis ya kasa zama har hular kansa ya cire dan fadar yaran Luba guda biyu ba nashi bane ba Abdul da khalifa ya matukar daga masa hankali yanzu duk wahalar da Luba ta ringa bashi akan yaran ba yaransa bane na wani ne, jikinsa rawa kawai yake Luba ta wuce tunaninsa dama duk tsawon lokacin nan tana zuwa wajen wani,taya ma zai yarda Bintu yarsa ce ba Yar wani ba,kallon ita da Asabe kawai yake, sanin Luba bai tab'a zame masa alheri ba sai sharri Ashraf kuwa tsayuwarsa ya gyara ya maida hankalinsa kan Asabe Yana "kinsan ghalin ne naga kin Kira sunansa"? Da sauri Asabe ta hau girgiza kanta tana "Bansan shi ba kama yayi min da wani" Ashraf ya saki murmushi Yana "kinaso kice iya Bintu ce Yar Alhaji Salis sauran bashine mahaifinsu ba"? "Eee hakane" "Akwai Kuma wani sirrinta da kike ganin ya kamata kotu ta sani Bayan wanan"? "Bai wuce juya masa tunani da tayi sai yanda tayi dashi ba,iya sirrinta dana sani kenan" Gyada kai Ashraf yayi ya juya wajen Luba Yana "Hajiya Luba kinji abinda kawarki aminiyarki tace ke Kika yiwa muhasim allura da taimakon Saurayinki Saeed zaki yarda ki amsa laifinki batare da kin wahalar da Sharia ba ko kuma kina da ja"? "Ina da ja asirina ya riga da ya tonu zan Fadi iya gaskiyata duk maganar da tayi karya take yi, duk wani abu da na aikata ita ta Sakani na aikata,a lokacin da na gano muhasim na d'auke da cikin Alhaji Salis ban taba tunanin tab'a lafiyarta ba Asabe itace ta bani shawarar haka,Dr Saeed da take magana Kuma abokin saurayinta ne,a lokacin ita ta hadani dashi akan na hakura da Alhaji Salis na auri shi Alhaji Saeed din tunda a lokacin bashida mata matarsa ta rasu,ni Kuma sai nace mata bai yi min ba dan bashida irin kudin da nake so ya zama mijina na da shi,sai ta bani shawarar na ringa wankarsa Yana da sakin kudi,yaso Aurena a lokacin naki yarda a lokacin da maganar muhasim ta b'ullo muka yi ta shawara da Asabe yanda zan samu cikar burina akan Alhaji Salis duk shawarar da muka yanke har na sace muhasim din bai yi ba sai da ta kawo shawarar ko ayi mata allurar da bazata tab'a iya magana ba ballantana tace Salis ne ya mata ciki,a lokacin na dauka iya alluran d'auke magana ne shiyasa jiki na rawa nace na yarda Muka je office din Dr Saeed din a tare,ita ta fada masa abinda muke so ya mana take ya nuna mana da hatsari alluran dan Yana iya zuwa da karar kwana,take naji hankalina ya tashi dan idan har muhasim ta mutu bazan tab'a samun cikar burina ba,sai da yace zai nemo Wanda bashida k'arfi sosai dan ba'a samun sa anan sosai kafin na yarda akan za'a mata alluran duk da a tsorace nake Asabe haka ta ringa zugani,kwana biyu a tsakani Dr Saeed ya aiko ghali akan ya kawo mana alluran baya gari yayi tafiya. Ghali shine saurayin Asabe. A lokacin ma Ghali muka so ya mata alluran yace bazai samu zuwa a ranar ba hakane yasa Koda na yaudari muhasim.akan tazo zan taimaka mata Asabe ce tace min zata iya mata alluran. Washegari da sassafe muhasim taje gidansu Asabe da kwatancen da na mata,dama ta riga ta hadani da wani mai abin hawa na biyashi akan ya jiramu a bayan gida,a lokacin da muhasim tazo sai naji Kuma hankalina ya tashi dan Ina tsoron ta mutu ba Kuma wai dan Zan damu da mutuwarta ba sai dan burina da bazai cika ba. "Wlh wlh da Asabe ta bani alluran ban iya mata ba rufe mata baki nayi da hannu daya na danne ta Asabe tazo ta danna Mata alluran a wuyanta sai da ta karar da ruwan ta zare daga wuyanta,bani na mata alluran ba nidai na rike muhasim anyi mata alluran,tare muka kinkimi muhasim muka kai ta mota,na hau muka je muka jefata a bayan makaranta,Asabe Kuma itace ta kashe kishiyarta Rabi ta hanyar saka mata guba ghali shine ya hada alluran guban,yanda na ringa muamalla da Saeed da aurena haka take muamalla da ghali wanan shine iya gaskiyar abinda ya faru" "Wlh karya take min bani na mata allura ba ni bansan wani ghali ba" Asabe tace hankalinta a tashe Yusuf mijinta kuwa sallati kawai ya ringa kwadawa da k'arfi yanda Ya ringa k'ok'arin yin wajen Asabe yasa Yan sanda sukayi waje dashi. Ashraf ya kalli Luba Yana "Yanzu Ina shi Dr Saeed din yake"? "Bansan Inda yake ba dan gaskiya bana Jin Yana shigowa Nigeria yanzu dan indai ya shigo sai ya kirani mun had'u"